Majalisar Jihar Kaduna Ta Bude Bincike Kan Ginin Kasuwa da Aka Yi Watsi da Shi
Published: 9th, April 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin samar da kungiyar masu amfani da ruwan sha da makamantan su na 2025 ya zama doka.
Kudirin wanda zai bunkasa samar da ruwan sha da amfani a fadin jihar, ya samu karbuwa da amincewa cikin gaggawa saboda muhimmancin ruwa ga rayuwar al’umma.
Shugaban majalisar dokoki ta jihar, Yusuf Dahiru Liman ya sanar da amincewa da kudiring a lokacin zaman majalisar a Kaduna.
Kudirin da bangaren zartarwa na jihar ya aike da shi majalisar, an mika shi ga kwamitin ayyukan al’umma da samar da ababen more rdayuwa domin yin nazari akai, inda daga bisani ‘yan kwamitin suka tuntubi masu ruwa da tsaki a bangaren domin jin ba’asin su, sannan ya gabatar da bayanan da ya tattara da kuma shawarwari a zauren majalisar.
Shugaban kwamitin ayyukan al’umma da ababen more rayuwa, Alhaji Nasir Idris ya yi bayanin alfanun kudirin wajen bunkasa albarkatun ruwa a jihar da ma kasa baki daya.
Alhaji Nasir Idris ya lura cewa an amince da kudirin ne cikin hanzari duba da muhimmancin ruwa, wanda ya kasance wajen inganta lafiyar al’umma da zamantakewar su a jihar.
A wani labarin kuma, majalisar dokoki ta jihar Kaduna ta karba tare da amince da rahoton korafin da aka gabatar mata akan wani dan kwangila da aka baiwa aikin gina kasuwar Tudun Saibu ta Zamani a karamar hokumar Soba ta Jihar.
Da yake gabatar da rahoton binciken, Shugaban kwamitin bunkasa kasuwanni kuma dan majalisar mai wakiltar mazabar Jama’a, Mr. Ali Kalat aikin hadin gwiwa ne tsakanin majalisar karamar hukumar soba da wani kamfani Bebeji Integrated Services Limited wanda dan kwangilar ya gaza cika alkawarin da aka yi da shi,
A cewar rahoton, an kulla yarjejeniyar ce tun a watan Afrilun 2021 sannan a na sa ran kammalawa cikin kwanaki 90, sai dai dan kwangilar ya rushe gine-ginen tsohuwar kasuwar ce kawai ba tare da aza harsashin gina wata ba, duk da ikirarin da ya yi na cewa ya kai bulo 30,000 da siminti rabin tirela.
Kwamitin ya gano dan kwangilar ya saba yarjejeniya sannan ya bada shawarar a soke kwangilar domin a ba wani da ya cancanta domin gudanar da aikin.
Daga karshe kafatalin ‘yan majalisar sun amince da rahoton da kuma shawarwarin kwamitin.
Shamsuddeen Mannir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: kasuwa Kungiyar Ruwan Sha
এছাড়াও পড়ুন:
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD.
Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana.
Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa ta duniya da kuma karuwar yaduwar rikice-rikice, da ma rashin hukunta masu laifi. Bugu da kari, sabbin fasahohi suna ci gaba da bullowa “ba tare da bin wani tsari ba”, yayin da rashin daidaito ke kara tsananta. A wannan yanayi, babban taro karo na 80 na MDD mai tsawon mako guda da za a fara a mako mai zuwa, zai ba da duk wata dama ga tattaunawa da shiga tsakani.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp