2025-11-01@13:22:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8632

«ambaci cewa»:

    Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.” A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi,...
    A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi. “Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka. “Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
    Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba. Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka. Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare. Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.   BBC
    Daga Usman Muhammad Zaria   Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
    Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai.   Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa. Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita. Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada...
    Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne. Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar. Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar...
    Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan. A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da iyalinta cikin ruɗani da damuwa. Ta ce, “Na shiga firgici bayan na ga wannan labarin. Ba ni da wata alaka da Mai Wushirya. Wannan sharri ne tsagwaron karya.” Rahoton da aka yada a jaridar AMC Hausa ya yi iƙirarin cewa wai Mansurah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana son ta da gaske. Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa...
    Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP,  yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa. Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin...
    Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa. Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta...
    Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani. Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa. Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.
    A wani rahoto da miami herald ya wallafa a jiya jumaa ya nuna cewa kasar Amurka na shirin kaiwa kasar Venuzuwela hare hare,  yayin da Donald trump shugaban kasar Amurka yake musantawa cewa babu wani shiri na daukar matakin soji a kasar ta latin Amurka. Yace gwamnatin trump ta yanke shawarar kai hari kan wasu wuraren soji a kasar, a kowanne lokaci. Yace duk da yakin da washington ke yi kan miyagun kwayoyoi gwamnatinsa ba ta la’akari da kai hare-haren sojin kan venuzuwela yana nuna a akwai karo da juna a kalamansa na makon da ya gabata Da manema labarai suka tambayeshi ko hare-haren da Amurka takai a yan kwanakin nan kan jiragen ruwa a yankin karebiya da aka ce...
    ’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu. Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma. Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.
    Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya. Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son kofi, shi ne ya ƙaddamar da wannan sabon nau’in abin sha mai daraja. Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai. Wani daga cikin masu mallakar gidan, Serkan Sagsoz, ya ce sun zaɓi Dubai ne saboda “birni ne da  ya...
    3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
    Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya. Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP A lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu. Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u    Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi. A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati. A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi. Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne...
    A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025
    Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke Sipaniya na ƙoƙarin ɗauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski wanda ke fama da matsalar raunuka Ɗan jaridar ƙasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa ƙwallo a raga, hakan ne ya sa ƙungiyyar ta amince da ɗaukar Osimhen. ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA A ƙarshen kakar bana ne ake tunanin up Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa ƙungiyyar neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo. Victor Osimhen dai a bazarar nan ne ya...
    Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo. Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida. ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP Mai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada. Sai dai a cikin wata sanarwa da...
      Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da...
    Daga Usman Muhammad Zaria    Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse. A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne. Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar. Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar. Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru. Shedun gani da ido sun ce...
    Gwamnatin kasar Iran  ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami  suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi  a iran da kuma kasa da kasa. Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta...
    Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta yi gargadin game da barazanar hadarin gwajin makamanin nunkiliya bayan da shugaban Amurka Trump ya bada umarnin a fara gwajin makaman nukiliya,  Tace wannan matakin barazana ne  ga tsaro da zaman lafiyar duniya. Farhan Haq mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya  ya shaidawa manema labarai a birnin New York cewa sakataren janar din majalisar Antunio Guteress ya jaddada cewa hatsarin da makamin nukiliyar yake da she a halin yanzu yana ishara game da muhimmancin rashin daukar mataki akanshi don kaucewa babbar matsalar da zai haifar Har ila yau Guterres ya gaya wa duniya irin bala’in da gwajin da makamin nukiliyar ya jawo wanda aka yi na nukiliya 2000 a shekaru 80 da suka...
    A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.   Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.   Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga...
    “Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.” Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne. “A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen...
    Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin fara amfani da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da Allah SWT ya hore ma ta da nufin haɓaka tattalin arzikinta tare da samarwa al’umma aikin yi. A yayin ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na Jihar da aka yi a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu, Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya ce kamfanin haɓaka ma’adanai ta Yobe Limited ita ce kawai hukumar da aka bai wa izini don gudanar da duk ayyukan bincike da haƙar ma’adinai a faɗin jihar. Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA Yana mai cewa, kamfanin haƙar ma’adinai na Yobe a halin yanzu shi...
    “Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa. “Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki October 31, 2025 Labarai...
    Daga Usman Muhammad Zaria   Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma. Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade. Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su. Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban. A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan majalisar wakilai, Abubakar Gummi daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Gummi yana wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara a majalisar wakilai. An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku Mai shari’a Obiora Egwuatu ne, ya yanke hukuncin, inda ya umarci kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, da ya daina amincewa da Gummi a matsayin dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum. Haka kuma ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta shirya sabon zabe cikin kwanaki 30 domin cike gurbin kujerar...
    Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya  da ya sanya rundunar  Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta. A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje,...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa. Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar  suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i. Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran...
    Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba. Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi. Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda.   An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar Alhamis a Maiduguri babban birnin jihar kamar yadda Kakakin rundunar a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa. A cewar sanarwar, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, wanda ya wakilci Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, shi ne ya gabatar da takardun cakin kudin ga iyalan waɗanda suka ci gajiyar tallafin. “Harkokin da suka shafi jami’anmu da...
    Oguntala ta bayyana cewa, ana sa ran babban ministan ma’aiktar bunkasa tattalin arziki na teku Mista Adegboyega Oyetola, zai halarci taron, wanda aka tsara za a gudanar a watan Disambar wannan shekarar a garin Ibadan. Ta bukaci hukumar ta Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, da ta yi hadaka da kungiyar domin gudanar da taron wanda ta sanar da cewa, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ne, zai kasance babban mai gabatar da jawabi, a wajen taron kungiyar. Kazalika, ta yi kira ga Hukumar ta NPA, da ta dauki nauyin manyan kasidun da za a gabatar da wajen taron tare da samar da ilimi kan batun da ya shafi fannin na bunkasa tattalin arziki na teku....
    A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar...
    Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu duniya ba ta bukatar sai an aiko annabi, ba ta bukata sai an aiko ma’aiki, a’a wanna abu da Manzon Allah ya zo da shi za mu iya kafa dalili da shi mu shirya kanmu ba sai da annabi ba. Wannan abu da Manzon Allah ya zo da shi yanzu ya kafa dalili da shi, da shi muka karantar da kanmu ba sai da Annabi...
    A zantawar Sule Lamido da BBC, ya bayyana cewa; an yi masa kora da hali a hedikwatar jam’iyyar ta PDP. Ya kara da cewa, ya je hedikwatar jam’iyyar PDP ne; domin karbar fom na takarar shugabancin PDP, sai ya samu ofishin da ya kamata ya karba a kulle, da ya tambaya sai aka ce da shi, a hannun gwamnan Adamawa kadai zai samu fom din. Lamido ya ci gaba da cewa, ba ya fata a kai ga matakin da za a hana shi shiga takarar, “domin ina tunanin rigimar cikin gida ce, sannan kuma za mu iya samun maslaha a cikin gidan. Amma idan hakan bai yiwu ba, daga nan kuma na san me zan yi,” in ji shi. Haka...
    Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
    ’Yan sanda a jihar Legas sun kama wani tsohon fursuna tare da wasu mutum biyu bisa zargin hannu a jerin laifukan fashi da yankan aljihu a jihar kwana biyar da fitowa daga kurkuku. Tsohon fursunan mai shekaru 25 da haihuwa, Segun Kolawole, an kama shi ne bayan kwana biyar da aka sako shi daga cibiyar gyaran hali ta Kirikiri, a jihar Legas. Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti Sauran wadanda aka kama tare da shi sun haɗa da Sodiq Isa mai shekaru 27 da Adekanmbi Ganiu mai shekaru 21. Rahotanni sun nuna cewa an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifukan yankan aljihun mutane da...
    Shugabannin Rundunar tsaro da Tinubu ya sallama sun hada da shugaban rundunar tsaro ta kasa Janar Christopher Musa da shugaban sojojin ruwa, Emmanuel Ikechukwu Ogalla da shugaban sojojin sama Hassan Abubakar. Wadanda suka maye gurbin su da idanu ya koma kan hobbasar kwazon da za su nuna su ne shugaban rundunar tsaro Olufemi Oluyede, shugaban sojojin kasa Waidi Shaibu, shugaban sojojin ruwa Idi Abbas da shugaban sojojin sama S.K Aneke sai kuma shugaban rundunar leken asiri, EAP Undiendeye wanda ya ci-gaba da rike kujerar sa. Yan Nijeriya sun jima suna kukan duk da kwarewa da gogewar jami’an sojojin Nijeriya da irin makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro a kowace shekara amma matsalar kullum gaba- gaba take kara...
    Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci. An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo. Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa. Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa...
    Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira. Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa. Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum A cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.   Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi. Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba. Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati? NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP...
    Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan. Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi. Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum Spalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda...
    A cewar Salahudeen, Ranar Yaƙi da Cutar Polio ta Duniya muhimmiyar dama ce ta faɗakar da jama’a kan barazanar da cutar shan-inna ke haifarwa ga rayuwar al’umma da tattalin arziki, tare da sake duba nasarori da kalubalen da ake fuskanta.   Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnatin jihar da kungiyoyin bunkasa lafiya — musamman Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) — ya taimaka matuƙa wajen cimma wannan gagarumar nasara.   “Gwamna Dauda Lawal ya ayyana dokar ta-baci a bangaren lafiya, kuma hakan ya zame ginshiqin da ya taimaka wajen samun tallafi, goyon baya da isassun ma’aikata don tabbatar da an kai rigakafi ko’ina,” inji shi.   Dekta Salahudeen ya kara da cewa WHO, UNICEF, Chigari, Sultan Foundation da Salina Foundation sun...
      A nata bangare, Amurka za ta dage aiwatar da matakai bisa bincikenta karkashin sashe na 301 na dokar cinikayya ta 1974, wanda zai shafi sashen jiragen ruwa na Sin, da hidimomin sufurinsu, da na kirar jiragen ruwan na Sin da karin shekara daya. Sakamakon hakan, ita kuma Sin za ta dage aiwatar da matakan martani ga sashen Amurka a wannan fanni da shekara daya, da zarar Amurkan ta aiwatar da na ta matakan.   Kakakin ya ce “An Kai Ruwa Rana” kafin cimma wannan sakamako, kuma Sin na fatan ganin ta ci gaba da aiki tare da tsagin Amurka, ta yadda za su hada karfi wajen tabbatar da an aiwatar da sakamakon, da ingiza karin tabbaci, da daidaito cikin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025 Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  October 30, 2025 Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025
    Shugaba Bola Tinubu ya nemi sabbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance duk wata barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu da ma wadda ka iya kunnowa nan gaba. Shugaban ya gargadi sabbin hafsoshin tsaron cewa ’yan Nijeriya sakamako kawai suke buƙata, ba uzuri ba, saboda haka dole ne su cika aikin da aka ɗora musu. Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026 Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket Tinubu ya bayyana hakan ne bayan bikin ƙara wa sabbin hafsoshin tsaron da shugabannin rundunonin soji girma da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis a Abuja. A cewarsa, “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi...
    Gwamnan Jihar Borno, Umara Zulum ya sanar da fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba a wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Jihar. Gwamnan ya jaddada cewa, wannan matakin wani ɓangare ne na babbar ajanda na bunƙasa masana’antu da kuma kawar da dogaro da jihar kan yi na kason da gwamnatin tarayya ke bayarwa duk wata. Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Zulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rangadin duba masana’antar robobi ta Borno da ke cikin yankin masana’antu na Maiduguri. “Ina farin cikin lura cewa mutanen Jihar Borno ba za su sake sayen kayan...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai. Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ya ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da...
    Wani haziƙin matashin ɗan wasan Cricket mai shekara 17 ɗan asalin ƙasar Australiya ya mutu a yau Alhamis bayan ƙwallo ta buge shi a lokacin wasa. Ƙwallon ta bugi, Ben Austin a wuyansa ne duk da cewa yana sanye da hular kariyar kai (Helmet) a lokacin da yake ƙoƙarin kare ƙwallon da aka bugo. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Nan take aka garzaya da shi asibiti cikin mawuyacin hali, daga bisani rai ya yi halinsa. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar haziƙi Ben ɗinmu, wanda ya mutu da safiyar yau Alhamis,” in ji mahaifinsa Jace Austin a cikin wata sanarwa. A cewar jaridar ABC News, matashin...
    Iran ta yi ikirarin cewa Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya “san”sarai da cewa shirin nukiliyar kasar na lumana ne, don haka ya kamata ya guji yin “kalamai marasa tushe” kan lamarin. A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa kalaman da Rafael Grossi ya yi a baya sun share fagen ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa Iran a watan Yunin da ya gabata. Ya kamata Darakta Janar na IAEA ya guji yin kalamai marasa tushe game da shirin nukiliya na Iran, in ji shi. Rafael Grossi ya bayyana a ranar Laraba cewa IAEA ta gano kwanan nan...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Ma’aikatar Yakin da ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya nan take, shawara da tauni ta tsorata masu fafutukar yaki da irin wannan manufa. A cikin wani sako da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social yau Alhamis, Trump ya bayyana cewa ya bayar da umarnin “saboda shirye-shiryen tantancewa da wasu kasashe suke yi.” Kuma a cewarsa wannan tsari zai fara nan take,” Shugaban Amurka ya bayyana Rasha da China a matsayin kasashe na biyu da na uku na duniya masu karfin makamman nukiliya, bi da bi, yana mai tabbatar da cewa idan Washington ba ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya ba, wadannan kasashe za su cimma ta nan da ” shekaru biyar.”     ...
    Isra’ila ta kai hare-hare da dama a safiyar Alhamis kan yankunan gabashin Khan Younis, a kudancin Zirin wanda ke nuna yadda isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. A cewar kafofin watsa labaran Falasdinawa, sama da hare-hare 10 a jere Isra’ila ta kai. Bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna makamai masu linzami na dira  akan wuraren zama a gabashin birnin. A lokaci guda, tankunan yaki na Isra’ila da motocin sulke sun yi ruwan bama-bamai a yankunan zama a gabashin Gaza. Sojojin Isra’ila sun kuma lalata gidaje da dama a gabashin birnin Gaza. Kasa da awa daya bayan haka, sojojin gwamnatin sun sake kai hari kan gidajen fararen hula a wannan yanki....
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa garin El-Fasher da ke Darfur a ranar Alhamis, da kuma mummunan tasirin da ya yi ga fararen hula. A cikin sanarwar da ya fitar, kwamitin ya nuna matukar damuwarsa game da karuwar tashin hankalin da ke faruwa a El-Fasher da kewaye, wanda Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta kwace iko da shi kwanan nan, kuma ya yi Allah wadai da ta’addancin da ake zargin dakarun RSF sun yi wa fararen hula, ciki har da kisan gilla da tsare mutane ba bisa ka’ida ba. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta “firgita da rahotannin kisan sama da marasa lafiya 460 da abokan aikinsu a...
    Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sabbin Shugabannin Sojoji ado da karin girma domin su dace da sabbin muƙamansu. Sabbin shugabannin rundunar sojin kasar da aka yi wa ado sun hada da Laftanar Janar, wanda yanzu ya zama Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS); da kuma Manjo Janar yanzu ya koma Laftanar Janar Emmanuel Undiendeye Undiendeye a matsayin Babban Hafsan Tsaro na farin kaya (CDI). Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  Sauran su ne Manjo Janar, wanda yanzu ya zama Laftanar Janar Waidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Soja (COAS); Air Vice Marshal, wanda yanzu ya...
      Da yake sharhi game da wannan batu a wani rubutu da ya yi a Facebook a ranar Alhamis, Sheikh Gumi ya ce, Sanda ta yi matukar nadama kuma ya tabbata ba halinta ba ne irin wannan mugun aiki face aikin shaiɗan ne ya yi sanadiyyar iftila’in, ba don son ranta ba ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025 Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025
    Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa. An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David Adamu, a sashi na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021. Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Domin tabbatar da ƙarar sa, mai gabatar da ƙara Funmi Bello, ya kira shaidu shida da waɗanda ake ƙara da su gabatar da jawabi, da fom ɗin shaida da kuma wuƙa a matsayin nunin...
    Rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta ƙone wani shagon Adidas Sports da ke cikin rukunin babban kantin nan na sayar da kayayyaki na Jabi Lake Mall, Abuja da tsakar daren Alhamis. Daily Trust ta ruwaito cewa, shagon ne kaɗai gobarar ta shafa. An kuma samu rahoton cewa, an baza jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da na Kamfanin Berger da na hukumar kashe gobara ta Abuja da kuma jami’an ’yan sanda zuwa wurin. Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 A lokacin da Wakilin Daily Trust ya kai ziyara da safe zuwa wurin, an shawo kan gobarar. Wani ma’aikaci a shagon ya ce...
    An zabi Doro ne bayan naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Kakakin fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana Doro a matsayin ƙwararren masani da ke da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni da dama ciki har da aikin asibiti, gudanar da harkokin magunguna, da jagoranci a Nijeriya da Birtaniya. An haifi Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a Kwall, ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Plateau. Yana da digiri a fannin magunguna da shari’a, MBA a dabarun kasuwanci na IT, da kuma digiri na biyu a fannin aikin lafiya mai zurfi (Advanced Clinical Practice). Da amincewar da aka yi masa a yau, ana sa ran Bernard Doro zai rantse a matsayin...
      Daga Abdullahi Shettima. Ƙungiyar taimako mai zaman kanta mai suna Rays Heaven for Special Needs Children and Adults ta gudanar da taron wayar da kai a Kaduna domin ƙarfafa fahimtar muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke shafar rukunin jama’a masu rauni. Shugaban shirye-shiryen ƙungiyar, Sadiq Abdilatif, ya bayyana cewa wannan shiri mai taken Youth Resilience Project ana aiwatar da shi ne da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) tare da Global Youth Mobilization Fund. Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kai ga makarantun sakandare, al’ummomi, da sansanonin ’yan gudun hijira kan mahimmancin lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarfafa matasa su koyi magana idan suna fuskantar damuwa ko matsaloli, da kuma koyar...
    Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta yi kira ga jihohin kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa wajen tare kujerun aikin hajji domin baiwa Maniyatan su damar sauke farali. Kwamishina a hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yamma , Sheikh Muhammad Bin Usman yayi wannan kiran a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Dutse, babban birnin Jihar. Sheikh Muhammad Bin Usman yayi bayanin cewar, ya zama wajibi ga sauran hukumomin Alhazan kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi wajen bai wa hukumomin Alhazai bashin kudade domin tare kujerun aikin Hajji ga maniyata. Yana mai nuni da cewar, a halin yanzu, jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kujerun...
    Kamfanin Amazon, wanda shi ne na biyu a yawan ma’aikata a Amurka, zai sallami ma’aikata kusan 600,000 ta hanyar maye gurbin su da mutum-mutumi nan shekaru 10 masu zuwa. Wani rahoton takardun cikin gida na kamfanin ne ta bayyana hakan, kamar yadda jaridar The New York Times ta Amurka ta wallafa. Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35 A cewar rahoton, wannan dabarar na fitowa ne daga masu lura da ma’aikata na kamfanin da alkaluman su ke nuna cewa kamfanin na iya kauce wa ɗaukar fiye da mutum 160,000 da ake bukata a Amurka nan da shekarar 2027. Kamfanin dillancin kaya na Amazon ya taɓa bayyana cewa amfani...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025 Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Amurka ta ɗaga tutar zaman lafiya yayin da muggan makamanta suke ci gaba da kai hare-hare kan al’ummun duniya Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya tabbatar da cewa: Taken zaman lafiya da Amurka ke gabatarwa a yanzu karya ne, yana mai cewa: Yayin da Amurka ke ba da shawarar zaman lafiya da tattaunawa a lokacin yakin da ya gabata, jiragen yakinta B-2 suna shirin kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran a lokaci guda. A lokacin da ya ziyarci lardin Khorasan ta Arewa da ke arewa maso gabashin Iran, Qalibaf ya yi jawabi a wani taro na tunawa da shahidan lardin a ranar Laraba da yamma, yana mai cewa:...
    Kwamandan Runduna Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan ya yi ikirarin kafa kwamitoci don binciken kisan kiyashin da aka yi a birnin El Fasher Kwamandan Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Sudan (RSF), Muhammed Hamdan Dagalo “Hemedti,” ya amince a ranar Laraba cewa: Mayakansa sun aikata “keta haddi” a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan. Ya yi ikirarin cewa: An kafa kwamitocin bincike kuma sun riga sun isa birnin domin fara ayyukansu. A cikin wani jawabi na bidiyo, Hemedti ya ce, “Ya ga keta haddi da aka yi a El Fasher, kuma daga nan ya sanar da kafa kwamitocin bincike, ba kawai kafa kwamitoci ba, har ma kwamitocin bincike sun riga sun isa birnin na El...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta ƙirƙiri ƙarin ƙananan hukumomi 29 a jihar. Wata takarda da Aminiya ta samu ta nuna cewa Mukaddashin Mataimakin Magatakarda na Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Musa Yerima, ya tura wannan ƙuduri zuwa Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki, yana neman amincewar Majalisar Tarayya domin tabbatar da dokar a cikin gyaran kundin tsarin mulki da ake yi. Tinubu ya ƙirƙiri sabon harajin da zai iya ƙara N100 a kan kowacce litar man fetur Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati A halin yanzu, Jihar Bauchi na da ƙananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya amince da su. Da...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar da sabon harajin shigo da kaya na kashi 15 cikin 100 kan dukkan man fetur da dizil din da aka shigo da shi zuwa Najeriya. An tsara wannan mataki ne domin kare matatun man cikin gida da kuma daidaita kasuwar man fetur a ƙasa, sai dai ana sa ran hakan zai iya haifar da ƙarin farashin man a gidajen mai. Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35 Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai A cikin wata wasiƙa da aka rubuta a ranar 21 ga Oktoba, 2025, kuma aka bayyana a hukumance a ranar 30 ga Oktoba, 2025, zuwa Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa...
    Masana sun bayyana cewa wannan sabon haraji zai iya sa wa farashin mai ya tashi. Gwamnati ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage yawan kashe kuɗi wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai October 30, 2025 Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025
    Ana zargin mutumin da hannu wajen sace Alhaji Adamu. Wanda ake zargin ya samu raunuka bayan jama’a sun yi masa duka kafin isowar sojoji, kuma an garzaya da shi asibiti, yayin da ake ci gaba da bincike. Brigedi Janar Kingsley Chidiebere Uwa, kwamandan Rundunar 6, ya yaba da yadda sojoji, ‘yan sa-kai da mafarauta suka haɗa kai, yana mai cewa wannan haɗin kai ya taimaka wajen samun nasarar ceto wanda aka sace. Ya kuma buƙaci jama’ar Taraba su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai da wuri domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya October...
    Wani matashi mai shekaru 20, Jibrin Saidu Lamido, ya rasa ransa bayan wani rikici a kan soyayya da ya auku  ƙauyen Gurdadi da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je zance wajen budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri. Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35 Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati Wata majiya ta ce wani mutum da ba a san ko waye ba ya zo wajensu, tare da tafiya da budurwar sannan ya ƙalubalanci Jibrin da ya biyo su idan shi “namijin gaske ne.”...
    “Muna kira ga hukumar da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da daidaito a lokacin ɗaukar ma’aikata na gwamnatin tarayya,” in ji shi. Shugaban Majalisar ya yaba wa Dala bisa kishin ƙasa da ya nuna, sannan ya umarci kwamitin majalisar da ya binciki lamarin tare da gabatar da rahoto domin ɗaukar mataki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II October 30, 2025 Manyan Labarai Atiku Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Sauya Sunayen Waɗanda Aka Yi Wa Afuwa October 30, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU October 29, 2025
    “Ba za mu ci gaba da ɓata kuɗi a kan abubuwan banza ba, kamar yawan ministoci, sayen motocin gwamnati, da ma’aikatan da ke yi wa shugabanni hidima. “Idan muna samun ƙarin kuɗi amma muna kashe su ba daidai ba, to duk ci gaban da muka samu ba zai yi tasiri ba,” in ji shi. Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce matsalolin tattalin arziƙin Nijeriya sun samo asali ne shekaru da dama. Ya shawarci shugabanni su riƙa sauraron masu faɗa musu gaskiya maimakon waɗanda ke yabonsu kawai. Ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa da an cire tallafin man fetur tun wuri da ha rage wahalar da ake ciki yanzu, amma gwamnatocin baya sun kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan. ShareTweetSendShare...
    “Ba za mu ci gaba da ɓata kuɗi a kan abubuwan banza ba, kamar yawan ministoci, sayen motocin gwamnati, da ma’aikatan da ke yi wa shugabanni hidima. “Idan muna samun ƙarin kuɗi amma muna kashe su ba daidai ba, to duk ci gaban da muka samu ba zai yi tasiri ba,” in ji shi. Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce matsalolin tattalin arziƙin Nijeriya sun samo asali ne shekaru da dama. Ya shawarci shugabanni su riƙa sauraron masu faɗa musu gaskiya maimakon waɗanda ke yabonsu kawai. Ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa da an cire tallafin man fetur tun wuri da ha rage wahalar da ake ciki yanzu, amma gwamnatocin baya sun kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan. ShareTweetSendShare...
    Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba. “Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris. “Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.” Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya...
    “Ba wasa ba ne yi wa mutane afuwa. Ya kamata ta zama alamar adalci da muradun ƙasa, ba dama ga masu aikata laifi ba,” in ji shi. Atiku ya ce wannan lamari ya nuna cewa gwamnatin ba ta da tsari, sannan ya buƙaci a wallafa cikakken jerin sunayen mutanen da aka fara yi wa afuwa domin ‘yan Nijeriya su san gaskiya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025 Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October...
    Kasar Rasha ta sanar da samun nasarar gwajin jirgi maras matuki  na nukiliya wanda yake ninkaya a cikin ruwa. Gwajin dai ya biyo bayan wasu gwaje-gwajen da Rashan ta yi ne na makamai masu linzami samfura mabanbanta masu iya daukar makaman  Nukiliya. Jirgin  maras matuki mai daukar makamin Nukiliya  yana a karkashin rundunar sojan ruwan kasar,da aka bai wa sunan; Bosidon. Bugu da kari shi kanshi jirgin yana aiki ne da nukiliya a matsayin makamanshin da yake tafiyar da shi. Shugaban kasar Rasha Vladmir ya ce; babu wata na’ura wacce za ta iya dakatar da wannan jirgin  mai ninkaya a cikin ruwa na Nukiliya. Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa; Wannan sabon makamin babu kwatankwacinsa a duniya saboda...
    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima. Shugabannin ƙungiyar sun kai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka gayyace shi zuwa bikin cika shekaru 25 da kafa ACF. An sanya dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga kan zaɓen Tanzania Gwamnati ta bai wa ASUU N2.3bn domin biyan bashin albashin malamai Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin Shugaba Tinubu da Shettima, ya bayyana cewa hakan alama ce ta haɗin kai da shugabanci na gari. “A wajenmu ’yan Arewa, Mataimakin Shugaban Ƙasa shi ne jakadanmu na farko. Yana yin biyayya ga Shugaban Ƙasa kuma...
      Dr. Alausa ya ce, za a fitar da kudaden ne ta Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), wanda hakan ke nuna kudirin Shugaba Bola Tinubu na biyan basussukan da ya gada domin karfafa kwarin gwiwar ma’aikata a manyan makarantu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro October 29, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya October 29, 2025 Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025
      Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”. A yayin da ra’ayin bangaranci da babakere ke takura tsarin hadin gwiwa na duniya, wannan sabon tsarin ya samar da wata hanya iri ta Asiya don kiyaye tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tataunawa...
    An bayyana cewa mahalartan EIMC 18 sun fito ne daga hukumomin tsaron Nijeriya da kuma ƙasashen Afrika kamar Chadi, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambiya.   A cikin laccarsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa salon Zamfara ta zama abin koyi ga sauran sassan Afrika wajen nazarin yadda ake ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci gaba.   Ya ce, “A cikin shekaru 20 da suka wuce, tsarin tsaro a Afrika ya sauya sosai. Ra’ayin cewa gwamnati ita kaɗai ke da ikon amfani da ƙarfi yanzu ya fara fuskantar kalubale daga ƙungiyoyi marasa bin tsarin gwamnati – ciki har da ‘yan sa-kai, ƙungiyoyin kare kai, ‘yan ta’adda, barayin daji da kuma cibiyoyin aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.”   Gwamnan ya bayyana...
    Gwamnatin Tarayya ta fitar da naira biliyan biyu da miliyan ɗari uku har da ɗoriya domin biyan bashin albashi da na ƙarin girma ga malamai a jami’o’in tarayya. Wannan dai wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa jin daɗin ma’aikata da kuma ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU. Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake jawabi kan tattaunawar da gwamnati ke yi da ƙungiyar ASUU da sauran ƙungiyoyin jami’o’i. Ya ce an riga an tura kuɗin ta ofishin Akanta-Janar na Ƙasa (OAGF), kuma jami’o’in da abin ya shafa za su fara...
    Kakakin ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei ya bayyana a yau cewa, yanayin ruwa da na iska a kasar ya ci gaba da ingantuwa a cikin watanni 9 na farkon bana. A cewarsa, matsakaicin nauyin burbushin abubuwan dake cikin iska na PM2.5, wanda shi ne muhimmin ma’aunin gurbatar iska, ya tsaya kan microgram 26 kan kowane cubic mita, a cikin birane ko garuruwan Sin 339, daga watan Janairu zuwa na Satumba, wannan ya nuna cewa an samu raguwar ma’aunin da kaso 5.1 kan mizanin shekara-shekara. Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, an samu ingantacciyar iska a kaso 87.6 na kwanakin, wanda ya karu da maki kaso 1.8 kan na bara. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa...
    Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai kamata a kwace kudin ba har abada, amma babu wanda ya amsa.   “Saboda haka, muna neman a ba da umarnin a kwace kudin har abada a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya, saboda bin umarnin wucin gadi kuma babu wanda ya nuna adawa da hukuncin,” in ji Akponimisingha ga kotun.   Hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sassauci wa matar nan da kotu ta yankewa hukuncin kisa bayan samunta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda.  Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasar ya janye sunan Maryam Sanda daga cikin jerin waɗanda ya yi wa afuwa a kwanakin baya. Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba Ana iya tuna cewa, a farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rayayyu. Abin da ya fi daukar hankali a lokacin da aka sanar da afuwar shi ne ganin sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka, cikin wadanda...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump October 29, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu October 28, 2025
    Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa wasu wadanda suka hada da masu manyan laifuka kamar kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu. A baya dai wasu sun yi ta suka da ce-ce-ku-ce kan sanya sunan Maryam Sanda cikin wadanda shugaba Tinubu ya yi wa afuwa. Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika Duk da maganganun mutane sunan Maryam Sanda na cikin sabon jerin sunayen wadanda aka bari, bayan cire wasu. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunan aƙalla mutum 50 daga tsohon jerin sunayen da aka fitar bayan ce-ce-ku-cen jama’a....
    Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu laifukan da suka haɗa da kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu. Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa saboda zargin kashe mijinta, ba ta cikin sabon jerin sunayen wadanda aka yafe wa laifi. Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunayen mutane kimanin 50 daga tsohon jerin bayan ce-ce-ku-ce daga jama’a. “Bayan duba martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun kwayoyi, da fataucin mutane daga jerin wadanda aka bai wa afuwa,” in ji Onanuga. Ya kara da cewa an dauki wannan...
    Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin tantance ma’aikata sama da 7,000 ta hanyar Intanet domin tabbatar da bayanansu da kuma kawar da ma’aikatan bogi. Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar (CSC), Hajiya Rabi Shu’aibu Jimeta, wacce ke jagorantar aikin, ta ce wannan shiri na nufin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikata. An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra Ta bayyana cewa za a kammala aikin cikin makonni takwas, kuma duk ma’aikatan da abin ya shafa za a ɗauki bayanansu domin sauƙaƙa samun bayanai. Hajiya Jimeta, ta ce an keɓe ma’aikatan shari’a, hukumar malamai (Teachers Service Commission), da ma’aikatan lafiya, saboda hukumominsu na da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin. An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara...
    Wata gamayyar malaman addinin Musulmai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta aika da ƙorafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin wasu malamai biyu da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Ana zargin malaman ne da yi batancin a cikin wa’azozinsu na kafafen sada zumunta. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Ƙorafin, wanda malamai goma sha shida (16) suka sanya wa hannu, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Umar Shehu Zaria da Malam Muhammad Sani Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Na’iya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki. A cewar masu ƙorafin, ayyukan waɗannan malamai biyu “na...
    Mummunan cin zarafi a birnin El Fasher na kasar Sudan ya haifar da tofin Allah tsine da Allah wadai daga al’ummomin ƙasashen duniya da na cikin gida Kisan gilla da laifukan da ake aikatawa kan fararen hula a El Fasher, Arewacin Darfur, sun jawo Allah wadai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam, yayin da gwamnati da hukumomin yankin ke musayar zarge-zarge game da musabbabin bala’in da kuma nauyin da ke kan al’ummar duniya. An ci gaba da Allah wadai da kasashen duniya da na cikin gida game da take hakkin da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta aikata kuma har yanzu take aikatawa kan fararen hula a El Fasher Arewacin Darfur. Kwamishinan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa fararen hula a Sudan Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar a yammacin jiya Talata, Baqa’i ya nuna damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. Baqa’i...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba. Ya bayyana cewa: Kawo ƙarshen waɗannan matakan ba wai kawai zai samar da sauƙi ga al’ummar Cuba ba ne, har ma zai aika da saƙo mai haske da yanke hukunci ga duniya cewa zamanin tilastawa, mulkin mallaka, da rashin adalci na tattalin arziki ya ƙare. Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka...
    Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu ta soki shirin Trump kan Gaza tana mai jaddada cewa: “Yana daga mafi munin cin mutuncin da ta taɓa gani a rayuwarta Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Haƙƙin Dan Adam a Yankin Falasɗinu, Francesca Albanese, ta bayyana shirin zaman lafiya na Shugaban Amurka Donald Trump a Gaza a matsayin “mafi munin cin mutunci da na taɓa gani a rayuwarta,” tana mai tabbatar da cewa Shirin ba shi da haƙƙi na shari’a da na ɗabi’a. Albanese ta bayyana cewa: Ba ta da imani da tsarin siyasa na yanzu da ake Shirin aiwatarwa a Gaza ba, tana mai ƙarawa da cewa, “Ba za a iya gina...
    Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno. Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi Ya ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma...
    Gwamnatin kasar Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan babban jagoran adawar kasar, Issa Tchiroma Bakary, bisa zarginsa da tayar da tarzoma bayan zaben shugaban ƙasa. Ministan cikin gida na kasar, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna. Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Ya ce hukumomin kasar sun fara tattara saƙonnin kafafen sada zumunta da bidiyo da aka bayyana a matsayin “ƙarya” da kuma masu tayar da hankali domin a gurfanar da masu wallafa su a gaban...