2025-05-23@01:05:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4872

«kasar Sweden»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma masu kamuwa da cutukan kwakwalwa yana karuwa.” Majiyar tsaron ‘yan sahayoniya ta tabbatar da cewa; sojojin nasu sun shiga wannan halin ne na kashe kai da tabin kwakwalwa, tun bayan da su ka shiga Gaza. Tun da yakin Gaza ya barke, an sami sojojin 9000 da su ka sami tabin kwakwalwa, kuma a halin yanzu suna karbar magunguna daga asibitocin mahaukata. Su kuwa sojojin da suke kashe kansu, ba a yi musu jana’izar soja don haka ba a bayyana adadinsu.
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.”  Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda ya gana da iyalan shahid Ra’isi da sauran shahidan hidima, da safiyar yau Talata, ya kara da cewa: Manufar girmama shahidai da kuma jinjinawa ayyukan da su ka yi, shi ne daukar darussa daga rayuwarsu. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ake fada dangane da shahid Ra’isi shi ne cewa ya kasance mai dukkanin siffofin jami’in da yake wakiltar hukumar da ta ginu...
    Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Rahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar. An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure. A yanzu matashiyar ta fi mayar da hankali...
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tshouwar Mawakiyar Hausa Hip-Hop, Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Rahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar. An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure. A shekarun baya, Queen...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin CSP Rabiu Gidado ta kama wani da ake zargi, Saidu Abubakar, a Jihar Filato. Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja  An kama ɗan bindiga a hanyar zuwa aikin Hajji a Sakkwato An same shi da wata mota ƙirar Toyota Corolla samfurin 2016 da aka sace wa wani mazaunin unguwar Naibawa a Kano. Yayin gudanar da bincike, Abubakar ya amsa cewa...
    A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya. Ya ce duk da cewa aiki ne mai matukar wahala, amma duk da haka kasar Sin ta cimma nasarar rage shi daidai da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, shekaru 10 gabanin wa’adin karshe na ajandar. Hakan ya shaida ingancin...
    Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.   Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.   “Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.   Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin.. ...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
    A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na dalar Amurka a fannin ciniki, da yadda ake sarrafa farashin kudin, sun tsananta yanayin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, da jefa kamfanonin kasar cikin mawuyacin hali. Ta yaya za a iya daidaita matsalolin da ake fuskanta? Mista Akanbi ya ba da shawarar daina dogaro da kasashen yamma, da tabbatar da bangarorin tattalin arzikin kasa da za a ba muhimmanci, bisa ra’ayin kasar, kamar yadda kasar...
    Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur. Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Harin ’yan bindiga ya sa Zamfarawa sun koma kwana a jeji Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana sunan mamatan a matsayin Umar Sa’idu da Rashida Yakubu. Ya ce lamarin ya faru ne da yamma, kuma ya sanar da manyan jami’an tsaro ciki...
    Mahajjata da jami’ai sun yaba da wannan gaskiya da rikon amana. Wasu sun ce hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa ga tsaron mahajjata da amincin tsarin aikin hajji. “Alhamdulillah, Hajiya ta samu kuɗinta gaba ɗaya,” in ji wani jami’in sansanin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen matan da aka kama ba, amma jami’an leƙen asirin Nijeriya sun ce matan na da muhimmanci wajen binciken hanyoyin samun kuɗaɗe da tallafin da ‘yan ta’adda ke samu. Wani masani kan yaƙi da ta’addanci ya ce wannan ci gaba ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro a Nijeriya ta fara ɗaukar salo na ƙasa da ƙasa. Ya kuma bayyana irin yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga Nijeriya...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka. A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma. Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen...
    Hare-haren wuce gona da irin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Gaza tun daga safiyar yau, sun yi sanadiyyar shahadan Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu na daban Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hulan Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu na daban tun daga wayewar garin ranar yau Talata, sakamakon luguden wuta da jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na zirin Gaza. Shafin yanar gizo na Palestine Today ya nakalto daga majiyoyin lafiya na cewa: A kalla Falasdinawa 10 ne suka yi shahada sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan makarantar Musa bin Nusair da ke dauke da...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
    Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila. Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa...
    Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban na Gaza cikin rabin sa’a da dare, in ji likitocin Falasɗinawa. Rahotanni daga hukumar agajin gaggawa da ke ƙarkashin Hamas sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a wurare da dama, ciki har da wata makaranta a gabashin birnin Gaza, da kuma wani tsohon gidan mai a sansanin ’yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda iyalai da dama ke neman mafaka. Hukumar ta ƙara da cewa tawagar ceto na fuskantar matsaloli wajen kai ɗauki ga waɗanda suka jikkata saboda ƙarancin kayan aiki da kuma tsananin harin. Wannan hari ya biyo bayan umarnin kwashe jama’a gaba ɗaya...
    Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...
    Kwanan baya, yayin taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar Sin da CELAC, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya ziyarci kasar Sin, inda kuma ya zanta da kafar CMG a shirin “Hira da shugabanni”. Yayin tattaunawar, shugaba Petro ya ce ya sha ziyartar kasar Sin cikin shekaru 20 da suka gabata. Ya kuma yi imanin cewa, ayyukan kasar Sin sun nuna wani sabon salo na ci gaban zamantakewar al’ummar bil’adama. Ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a fannin raya tattalin arziki da kawar da talauci, daruruwan miliyoyin mutane sun tsira daga kangin talauci, kuma sha’anin kawar da talauci a duniya ya samu gagarumin ci gaba. Shugaba Petro ya kara da cewa, wadannan nasarori ba a iya raba...
    Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26. Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26. Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku. An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin...
    Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al’ummomi a kananan hukumomin Edu/Patigi/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu.   Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken “Hatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu” wanda Michael Imoudu tare da hadin gwiwar mamba mai wakiltar mazabar Edu/Moro/Patigi na Jihar Kwara, Ahmad Adamu -Saba ya shirya, ya ce za a yi rabon ne kashi biyu.   Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Muhammed Salihu, ya ce manufar shirin bayar da tallafin shi ne tallafawa daliban da iyayensu ba za su iya biyan wasu kudadensu a makaranta ba.  ...
    Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da kayayyaki a wurin, da karfafa kiyayewa, da amfani da abubuwan tarihi da al’adu, da habaka ingantattun masana’antun al’adu da yawon shakatawa da sauransu. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na horar da matasa sana’o’i daban-daban a fadin kasar nan.   Sakataren Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci, Dokta Yakubu Adam Kofar Mata, ya bayyana haka, a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan mahalarta shirin “Skill to Wealth” na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Kano.     Dokta Kofar Mata ya jaddada cewa, makasudin bayar da horon shi ne don cika sabbin alkawurran da gwamnati mai ci ta dauka na karfafa matasa.     Shirin bayar da horon na da nufin wadata matasa sana’o’in da za su iya dogaro da kansu da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasar.     Ko’odinetan shirin na Jiha Dokta Mahdi Isa...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kafa tutar hadin kai mai tsayin mita 70 a hukumance, wanda ke zama alamar “hadin kan kasa, tafiya tare da buri a matsayin al’umma”.   Da yake jawabi a wani takaitaccen biki a Ilorin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce jihar ba ta daga tuta kawai ba, a’a tana nuna kwarin guiwar wata alama ce ta hadin kai, alfahari, da kuma kishin kasa.   Gwamnan ya samu wakilcin kwamishinan sadarwa na jihar Bola Olukoju, wanda wasu kwamishinoni uku suka taimaka masa: Aliyu Kora Sabi (sufuri); Nafisat Buge (Muhalli); da Nnafatima Imam (ci gaban al’umma) da sauran manyan baki.   A cewarsa, sandar tuta na kara karfafa martabar jihar a matsayin cibiyar kirkire-kirkire, al’adu, da jagoranci mai ma’ana....
    An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki.   Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi 24 na jihar.   Ya ce kananan hukumomin sun hada da Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi, Gumel, Gagarawa, Garki, Maigatari, Suletankarkar, Babura, Jahun, da Miga.   Sauran sune Kafin Hausa, Auyo, Hadejia, Kirikasamma, Guri, Birniwa, Malam Madori, Dutse, Kiyawa, Ringim da Gwaram.   Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi nuni da cewa jirgin ya kuma kunshi wasu jami’an hukumar alhazai ta jiha da na likitoci da...
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi na Sultan Abubakar da ke jihar. An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji. Ɗan bindigar da aka kama a Abuja, ya kasance jami’an tsaro na nemansa kan ayyukan garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kogi....
    Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi na Sultan Abubakar da ke jihar. An kama shi ne a safiyar ranar Litinin, washegarin da jami’an tsaro suka kama wani ɗan bindiga yana yana shirin hawa mota zuwa filin jirgin sama na Abuja domin zuwa aikin Hajji. Ɗan bindigar da aka kama a Abuja, ya kasance jami’an tsaro na nemansa kan ayyukan garkuwa da mutane a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma Jihar Kogi....
    Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya. An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji. Ado Aliero shugaban ’yan bindiga ne da ya yi ƙaurin da yin garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda, musamman a Jihar Zamfara da maƙwabtanta. Kafar yada labarai ta ABN News ta bayyana cewa matan biyu sun canza sunayensu domin kada a gane su. An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno...
    An shirya sake zama a ranar Alhamis mai zuwa don kammala tattaunawar gaba ɗaya. Cikin waɗanda suka halarci ganawar har da wakilan MOPPAN kamar su Abdul Amart, Nazifi Asnanic, da Abubakar Bashir Maishadda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka. ” Zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne batutuwa mafi muhimmanci ga dukkan kasashen yankin,” in ji shi. Ya nanata matsayar Iran kan turbar diflomasiyya da kuma muhimmancin da take baiwa manufofin kyakkyawar makobtaka ta hanyar tattaunawa. A wani bangare na jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce dandalin tattaunawa na Tehran karo na shida ya samu...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin na cewa tattaunawar ta yi amfani.” Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine a kan wata yarjejeniya “game da samar da zaman lafiya a nan gaba.” “Rasha da Ukraine za su fara tattaunawa nan take domin tsagaita bude wuta,” in ji Trump. A cewar wata majiya kusa da tattaunawar da ke gudana, shugaban fadar White House ya tuntubi Volodymyr Zelensky “na ‘yan...
    Yemen ta yi barazanar killace babbar tashar jiragen ruwan Haifa ta Isra’ila, tare da gargadin cewa jiragen ruwa da ke tafiya a can. “Dukkan kamfanonin da jiragensu ke nan ko kuma suka nufi wannan tashar, ana sanar da su cewa, ya zuwa wannan sanarwar, an saka tashar cikin jerin wuraren da muke son kaiwa hari,” in ji kakakin kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a Yemen Yehya Saree. Rundunar sojin Yeman ta ce kakaba takunkumi na a matsayin mayar da martani ga yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.   Sanarwar ta ce sojojin Yemen ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar...
    Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dawo da cikakken tallafin da take baiwa zirin Gaza. Tireloli tara na taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ne aka ba su izinin shiga zirin Gaza a ranar Litinin, wanda ake wa kallo a matsayin digo ‘’ digo a cikin teku,” in ji shugaban kula da ayyukan jin kai na MDD, Tom Fletcher. Al’ummar Zirin Gaza suna “fuskantar yunwa” kuma “dole ne su sami taimakon da suke bukata,” in ji ma’aikatun harkokin waje na kasashen Australia, Canada, Denmark, Estonia, Finland, Faransa, Jamus, Iceland, Ireland, Italiya, Japan, Latvia, Lithuania, Luxembourg, Netherlands, New Zealand, Norway, Portugal, Slovenia, Spain, Sweden, da United Kingdom. Kasashen da suka rattaba hannu kan bukatar sun ce, “Bai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata. Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ’yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikinsu ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita. Ko waɗanne matakai ya kamata al’umma su ringa dauka wajen kare kansu da kuma lafiyar jikinsu? NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya A YAU na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan da mahukuntan kasar Sin suka kaddamar da yadda harkokin tattalin arzikin kasar suka gudana a watan Afrilun bana a ranar 19 ga wata, mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Novonesis na kasar Denmark, Morten Enggaard Rasmussen ya tattauna da wakilin CMG, inda a cewarsa, alkaluma sun nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce Kamfaninsa zai ci gaba da fadada harkokinsa a sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko a kasar ta Sin. Haka kuma, kafofin yada labaru na kasa da kasa sun ce, yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya wuce zaton mutane, suna cewa tattalin arzikin kasar Sin na da juriya da tabbaci. A watanni 4 na farkon bana, saurin karuwar muhimman alkaluma masu alaka...
    Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da naɗin sabbin sakatarorin ƙananan hukumomi guda 21 a faɗin jihar.   Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala ya sanya wa hannu, wacce aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.   Ya bukaci sabbin sakatarorin da aka naɗa da su yi aiki tukuru don ganin nasarar wannan gwamnati da kuma ci gaban jihar gaba ɗaya.   Daga Abdullahi Tukur    
    Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Gusau. Hajiya Huriyya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da hukumar, domin gano ingantattun hanyoyin da za su taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar. “Muna shirin zama tare domin duba hanyoyin da za mu bi wajen magance matsalolin da kuke fuskanta, domin muna da aniyar ganin Zamfara ta nisanta daga illar...
    Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu. An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci  rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada da garkuwa da mutane da kuma satar shanu. A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sannan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa maboyarsa da ke kauyen Ruwan Baka a karamar hukumar Doma, inda aka samu bindiga kirar AK-49 mai lamba 453144 tare da alburusai. Wannan nasarar ta biyo bayan kama wata Fatima Salisu a ‘yan kwanakin baya, wadda aka tare tana jigilar makamai daga...
    Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da masu shirya fina-finai sun cimma matsaya bayan dakatar da wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Labarina da Dadin Kowa, Manyan Maga da Garwashi. An bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda daga Litinin 19 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu 2025 domin miƙa fina-finansu don tantancewa da sahalewa. Kwamishina ta nemi a hukunta wanda ake zargi da yi wa ’yar matarsa fyaɗe a Gombe Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma Wannan na zuwa ne bayan wani taro da aka gudanar tsakanin hukumar da shugabannin masana’antar Kannywood a ranar Litinin. Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ya ce za a duba fina-finan cikin gaskiya da adalci. Shugaban...
    A kwanakin baya, an dawo da babi na 2 da na 3 masu taken “Wu Xing Ling” da “Gong Shou Zhan” na Rubutun siliki na Zidanku, wato kayan tarihi mai muhimmanci na kasar Sin, ta hanyar hadin gwiwa kan kayan tarihi tsakanin Sin da Amurka. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, wannan misali ne na yadda Sin ta cimma nasarar neman dawowar kayan tarihi da suka bata tun a zamanin da, kana nasara ce da Sin ta samu wajen yin kira ga yin shawarwari da hadin gwiwa don sa kaimi ga tabbatar da dawo da kayan tarihin da suka bace....
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, yankin Taiwan na kasar Sin ba shi dalili ko iko ko kuma hujjar halartar babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA), har sai sai gwamnatin tsakiya ta kasar ta amince masa. Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka yau Litinin, lokacin da yake tsokaci kan matakin da WHA ta dauka na kin sanya bukatar Taiwan ta halartar taron a matsayin ‘yar kallo, cikin ajandarta. A cewar kakakin, an shafe wani lokaci yanzu, hukumomin jam’iyyar DPP da wasu kasashe suna kokarin mayar da hannu agogo baya, inda suke kalubalanta da kokarin hargitsa kudurin MDD mai lamba 2758, domin kalubalantar manufar Sin daya tak a duniya. Ya ce, wannan ba kalubale ne ga cikkaken ‘yancin kasar...
    Wadanda ake tuhumar dai, a cewar rahoton farko, sun yi wa mamacin dukan tsiya har sai da ya suma, inda aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Hong inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.     Dukkan wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen.   Kotun da ke karkashin Alkali Uwani Danladi, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a gidan gyaran hali don bai wa ‘yansanda damar kammala bincike tun da har yanzu akwai sauran mutum daya da ake tuhuma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    Gwamnatin HKI ta bude kofofin shigar kayakin Agaji zuwa cikin zirin Gaza bayan takurawan kasashen duniya daga ciki har da kawayen ta kan cewa ba zasu iya ci gaba da ganin Falasdinawa suna mutuwa saboda da yunwa ba. Tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto wata majiyar jami’an gwamnatin HKI na fada a yau litinin kan cewa zasu fara barin kayakin agaji su shiga zirin Gaza daga yau zuwa shawarar da zasu dauka nan gaba. Labarin ya kara da cewa a safiyar yau litinin tawagar motoci dauke da kayakin abinci da magungun sun shiga zirin gaza ta kofar Karim Abusaleh, sannan MDD zata kula da shigowar kayakin agaji zuwa zirin na Gaza, a fadin tashar radiyo ta sojojin HKI. Wasu majiyoyin...
    Shugaban kasar Lebanon Josept Aoun ya bayyana cewa gwamnatinsa tana son ta maida makamai a kasar Lebanon karkashin ikon hukuma kadai. Aoun ya ce kungiyar Hizbullah tana iya shiga harkokin siyasa na kasar Lebanon amma makamai na gwamnatin ne kadai. Jaridar ‘The National Ta Kasar Amurka’ ta n akalto shugaban yana fadar haka a kasar Masar a ganawarsa da tokwaransa na lasar Abdulfattah Assisi a yau Litinin. Aoun ya kara da cewa yana bukatar taimakon kasar Masar don gano ramukan da ake boye makamai a kasa. Sannan zai yi magana da shugaba Mahmood Abbas na Falasdinawa kan yadda za’a karbe makaman da suke hannun falasdinawa a sansanoninsu na yan gudun hijira da ke Ainul Helwa kusa da garin Saida na...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai  kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza  shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin. A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi...
    Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe. Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar Jauro Innayo a Gombe, inda ta tausaya mata tare da ba su kayan tallafi kamar su pampers, sabulai da kuma kuɗi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 26 a ƙauyukan Zamfara Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Asma’u ta sha alwashin cewa za a bi duk matakan shari’a domin ganin wanda ake zargi ya fuskanci hukunci. Ta ce...
    Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe. Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar Jauro Innayo a Gombe, inda ta tausaya mata tare da ba su kayan tallafi kamar su pampers, sabulai da kuma kuɗi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 3, sun sace 26 a ƙauyukan Zamfara Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Asma’u ta sha alwashin cewa za a bi duk matakan shari’a domin ganin wanda ake zargi ya fuskanci hukunci. Ta ce...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Rvanchi ya bayyana cewa a duk lokacinda gwamnatin Amurka ta gabatar da dakatar da tache makamacin Uranium a cikin Iran tattaunawar ba zata je ko in aba. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Steve Wit-koff jakadan shugaba Trump na musamman a yanking abas ta tsakiya, kuma wakilinsa a tattaunawar Tehran da Washingtong kan shirin makamashin Nukliyar Iran ya fadawa kafafen yana labarai kan cewa duk wata yarjeniya da za’a kulla da Iran a kan shirinta na makamashin Nukliya sai ya hada da rashin tashe makamashin Uranium a cikin kasar Iran, wanda zai nesantata daga makaman Nukliya. A nasa bangaren Takhta Ravanci ya bayyana cewa tun farko Iran ta bayyana...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da umurni kan babban shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin karo na 15, inda ya nanata wajibcin tsai da shiri bisa halin da ake ciki, matakin da ya kasance muhimmiyar dabarar jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS a fannin gudanar da harkokin kasa, kuma fifiko a siyasance na tsarin mulkin gurguzu mai salon musamman na Sin. Xi ya ce tsai da babban shiri na 15 na da babbar ma’ana ga tabbatar da manyan tsare-tsare da aka tanada a yayin babban taro karo na 20 na JKS, da gaggauta zamanantar da al’ummar Sinawa. Don haka dole ne a samar da shiri bisa halin da ake ciki, bisa tushen demokuradiyya...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar mata da korafi kan yadda jami’an tsaron kasar Burtaniya suke kama yan kasar Iran ma zauna birnin London tare da tuhumarsu da ayyukan Leken asiri wa JMI. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a cikin wannan watan Mayu da muke ciki Jami’an yansanda a kasar Burtaniya sun kama Iraniyawa mazauna birnin London har guda 7 a sumamen guda biyu da suka kaimasu a gidajensu. Labarin ya kara da cewa an gabatar da mutane uku a gaban kotu a birnin London tare da tuhumar su da aikin leken asiri ga JMI. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara...
    Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki. Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe. Hare-haren da ake kai wa Sabon Gari da maƙwabtan ƙauyuka na ƙara tsananta.” Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da...
    Kyaftin din kungiyar, Achu Gabriel, ya yabawa takwarorinsa da suka nuna kwazo, inda ya kara da cewa tawagar za ta ci gaba da mai da hankali wajen kwato kofin da ta lashe a shekarar 2018, tawagar ta Abuja za ta kara da mai masaukin baki, jihar Ogun a wasan rukuni na biyu a ranar Talata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hawa wannan babbar katangar na koyar darussa masu masu ma’ana,- daya daga cikinsu shi ne tsayin daka da ya kai ga Sinawa zuwa ga samun daukaka. Wannan gogewa ta nuna kyakkyawar dabi’ar aikin Sinawa, wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban da suka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata. Kafin wannan lokacin, jami’ar Yang Boazhin ya lura cewa, kasar Sin ta fi sauran sassan Afirka talauci. Ta ba da labarin ziyarar da ta kai Afirka a shekarar 1985 a matsayin jami’ar diflomasiyya, inda ta tabbatar da cewa Afirka na da gagarumin ci gaba a wannan lokacin. Jamhuriyar kasar Sin, mai yawan al’umma biliyan 1.4, ta kunshi gundumomi hudu da larduna 23, tare da yankuna biyar masu cin...
    Akalla mutane uku ne aka ce an kashe tare da yin garkuwa da wasu 26 a wani sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara. Daily trust ta bankado cewa, hare-haren na tun ranakun Alhamis zuwa Asabar, sun shafi al’ummomi da dama a yankin. Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya fi kamari akauyen Sabon Gari, inda aka kashe mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20. Wani mazaunin Kauran Namoda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa, adadin ya zarta haka, inda ya...
    Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko, ta ajiye muƙaminta. Ta bayyana murabus ɗinta ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Litinin a Birnin Benin, babban birnin jihar. Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 Oligbi-Edeko, wadda ke wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa Maso Gabas II, ta ce ta yi murabus ne, saboda jam’iyyarta ta PDP ta rasa rinjaye a majalisar bayan wasu ’yan jam’iyyar ciki har da Shugaban Majalisar sun koma jam’iyyar APC. An zaɓe ta a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar karo na takwas a ranar 16 ga watan Yunin 2023, kafin ta yi murabus. Bayan...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba. Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya. Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5 Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa. Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa...
    Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce duk da matsi sakamakon dalilai na ciki da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa daidaito a watan Afirilun da ya gabata. Alkaluman da NBS din ta fitar a Litinin din nan sun nuna karuwar hajojin da manyan masana’antun kasar ke samarwa da kaso 6.1 bisa dari a shekara, yayin da alkaluman samar da hidimomi suka karu da kaso 6.0 bisa dari a shekara. Sai kuma darajar jimillar hajojin sayayyar daidai, ta kayayyakin bukatun yau da kullum da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 3.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 515.6 a shekara, adadin da shi ma ya yi karuwar kaso 5.1 bisa dari. Kazalika, alkaluman sun nuna daga watan Janairu...
    Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023. Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye daga duk wata hulɗa da gwamnatin jihar, har sai an ba su kulawar da ta dace. Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Shugaban mawaƙan jihar, Lawan Gujungu Mai Babban Gandu ne, ya jagoranci taron, inda ya shaida wa manema labarai cewa tun bayan...
    Wasu mawaƙan jam’iyyar APC da ke Jihar Jigawa, sun bayyana ɓacin ransu kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar jam’iyyar a zaɓen 2023. Mawaƙan wajen su 35, sun gudanar da wani taro, inda suka bayyana damuwarsu da kuma sanar da cewa sun janye daga duk wata hulɗa da gwamnatin jihar, har sai an ba su kulawar da ta dace. Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Shugaban mawaƙan jihar, Lawan Gujungu Mai Babban Gandu ne, ya jagoranci taron, inda ya shaida wa manema labarai cewa tun bayan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran, don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen yankin yammacin Asiya. Inda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran suka gabatar da jawaban farko a taron. An sami halattan baki daga kasashe 53 daga cikinsu akwai jami’an gwamnatoci wadanda suka hada da ministoci  masana da shuwagabannin cibiyoyin bincike da bada shawarori na kasashen duniya da dama. Daga cikin bakin akwai ministan...
    Iyalan sarkin Okoloke na jihar Kogi, Oba James Dada Ogunyanda, sun yi kira ga al’umma don taimakawa wajen tara kuɗin fansa Naira miliyan ₦50 da masu garkuwa suka buƙata. An sace Sarkin ne daga fadarsa a Yagba West LGA ranar Alhamis da ta wuce. Duk da cewa sun tara miliyan ₦25 ta hanyar sayar da kayansu, iyalan sun ce wasu ‘yan siyasa da suke tsammanin za su taimaka sun har yanzu sun ji shiru. “Wasu ma sun toshe wayoyinmu,” in ji wani ɗan gidan, yana nuna damuwarsu game da yawan rashin lafiyar Sarkin da ke hannun masu garkuwa tsawon kwana 5. Zargin Kin Amincewar Kwankwaso Zuwa APC: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Mai Taimaka Ma Ta An Cafke Mai Garkuwa...
    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da tsohon Sojan sama (Air Vice Marshal) Ibrahim Umaru a matsayin sabon Kwamishinan tsaro na cikin gida a yayin taron majalisar zartarwa na 28 a fadar gwamnati. Tsohon hafsan Sojan saman, wanda ya yi ritaya, ya kasance Daraktan-Janar na sashin aiyuka na musamman a fadar gwamnatin jihar Kano kafin naɗin nasa. Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci Gwamnan Yusuf ya buƙaci sabon kwamishinan ya yi aiki da gaskiya, mutunci da himma wajen kare rayuka da dukiya a jihar, yana mai jaddada mahimmancin haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya. Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci. Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Gwamnan ya bai wa kowane maniyyaci kyautar Riyal 200 a matsayin goron Sallah. An kuma ja hankalin maniyyatan da ka da su karɓi kaya ko rigar wani, ko da ’yan jiharsu ne, don kauce wa matsala. Malaman addini da suka...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya. Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci. Yadda jami’an tsaron Vatican suka hana Seyi zuwa wajen Tinubu da Fafaroma NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Gwamnan ya bai wa kowane maniyyaci kyautar Riyal 200 a matsayin goron Sallah. An kuma ja hankalin maniyyatan da ka da su karɓi kaya ko rigar wani, ko da ’yan jiharsu ne, don kauce wa matsala. Malaman addini da suka...
    Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na cikin tawagar mahaifinsa da ta ziyarci fadar Vatican a ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo XIV. A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya gana da Fafaroma har suka gaisa. Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Amma abin da ya ja hankalin mutane shi ne lokacin da Seyi ya yi ƙoƙarin zuwa wajen mahaifinsa yayin da yake gaisawa da Fafaroma. A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani jami’in tsaro ya dakatar da Seyi cikin ladabi, yana nuna masa cewa bai kamata ya matsa kusa da wajen...
    Magoya bayan Everton sun yi ban kwana da filin Goodison Park, bayan shekara 133 suna taka leda a ciki. Ƙungiyar ta Mersyside za ta koma buga tamaula a Bramley-Moore Dock a kaka mai zuwa. To amma Everton za ta bai wa matan ƙungiyar filin Goodison Park, domin ci gaba da wasanni a ciki, amma za ta rage yawan kujerun zaman ƴan kallo.
    Hukumar da ke bayar da agajin magungunna ga Falasɗinawa ta ƙasar Birtaniya ta ce Isra’ila ta kai wani hari da ya afkawa rumbun ajiyar magungunna na Asibitin Nasser da ke yankin Khan Younis a tsakar daren da ya gabata a kudancin Gaza .   Hukumar ta ce harin ya auku ne “lokacin da ake kwashe Falasɗinawan da aka kashe da waɗanda aka jikkata zuwa asibiti, bayan wasu jerin hare-haren da Isra’ila ke kai”.   Daga cikin magungunnan da harin ya lalata sun haɗa da waɗanda hukumar ta samar wa asibitin na Nasser. “A yanzu dai muna kallo dukan magungunna da muka bayar tallafi sun ƙone ƙurmus” in ji kakakin hukumar.   Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da hotunan wuraren...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi.   Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su bi ka’idojin tsaro domin amfanin kowa.   Ya bayyana a matsayin al’ada mai raɗaɗi kuma ba za a yarda da ita ta rashin amfani da na’urorin kariya da gwamnati ta bayar akai-akai.   Yana rokon Allah ya jikan wadanda aka kashe. REL/ALI MUHAMMAD RABIU
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    Mutane 7 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu goma sha daya suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Essa dake kan titin Agaie Badeggi a karamar hukumar Katcha a jihar Neja.   Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Minna.   A cewar Abdullahi Baba Arah, motar na dauke da hatsin gwamnatin tarayya, da kuma wata mota dake dauke da wasu fasinjoji 36, wadanda dukkansu maza ne zasu jihar Kano daga jihar Legas suka yi toho mu gama a lokacin da hatsarin ya afku.   Hatsarin ya afku ne da...
    Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe.   Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da aka ga gwamnan yana magana da manema labarai kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro da kuma jin dadin wadanda matsalar tsaro ta shafa.   A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin rashin gaskiya da yaudara.   Malam Idris Yusuf Gusau ya yi zargin cewa, gwamnatin ta gaza cika wasu...
    “Mutanen Zamfara ba wawaye ba ne. Gwamnan ya kamata ya daina waɗannan maganganun ƙarya, ya daina farfaganda, ya kuma haɗa kai da masu ruwa da tsaki na gaskiya don magance matsalar tsaro,” in ji Gummi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Yana fatan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshgan ya bayyana cewa: Iran tana fatan tattaunawarta da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin. A yammacin jiya Lahadi, a gefen taron dandalin tattaunawa na Tehran na shekara ta 2025, a wata ganawa da ministan harkokin wajen masarautar Oman Badar bin Abdullah al-Busaidi, Shugaba Pezeshkian ya yaba da irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma irin rawar da gwamnatin Oman take takawa wajen daukar nauyin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Amurka da Jamhuriyar...
    Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22 sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar.   Cikin wata sanarwa da jami’in hul da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne bayar da umarcin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa’idojin hukumar waɗanda suka tanadi cewa dole ne hukumar ta tace su kafin fitar da su.   Wasu daga cikin fina-finan da dakatarwa ta shafa sun haɗa da   Dadin Kowa Labarina Gidan Sarauta Manyan Mata Dakin Amarya Kishiyata Garwashi Jamilun Jiddan Mashahuri Wasiyya Tawakkaltu Mijina Wani Zamani Mallaka Kudin Ruwa Boka Ko Malam Wayasan Gobe Rana Dubu Fatake Shahadar Nabila Tabarmar Rigar Aro An umurci...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ta jajirce kan harkokin diflomasiyya kuma tana neman yarjejeniya ta gaskiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada kudurin kasar Iran kan harkokin diflomasiyya da kuma cimma daidaito bisa tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, tare da cikakken mutunta hakkin nukiliyar kasar Iran, da kuma tabbatar da manufar dage takunkuman da aka sanya mata. Wannan dai ya zo ne a cikin jawabin da Araqchi ya gabatar a ranar Lahadin da ta gabata a wajen taron tattaunawa na birnin Tehran, wanda cibiyar nazarin harkokin siyasa da kasa da kasa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ta dauki nauyin shiryawa, tare da halartar tawagogi 200 na manyan jami’ai daga kasashe 53 da...
    Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa. Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin...
    Gwamnatin jihar Kebbi ta jajanta wa al’ummar Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu sakamakon harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar manoma 15 tare da jikkata wasu 3.   Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati tare da bayar da tallafin Naira miliyan 24 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.   Ya bayyana hakan a matsayin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a wannan lokaci mai cike da kalubale.   Sanata Abubakar, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace don magance matsalar rashin tsaro, tare da baiwa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin...
    A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka Biden ke fama ita Marubuciya kuma ‘yar jarida kasar Autraliya Caitlin Jahnstone a cikin wani makala da ta rubuta ta siffanta abin da ta kira matsayin munafuncin ƙasashen yamma wajen mu’amala da kimar ɗan adamtaka da gwada alhini kan batun ciwon tsohon shugaban Amurka Joe Biden game da cutar sankara da ke fama da ita a matsayin mafarin fallasa sabanin da ke cikin maganganun siyasa da kyawawan ɗabi’u na Amurka dangane da laifukan yaƙi musamman abin da ke faruwa a Gaza. Tana cewa: Ciwon daji na Prostate yana da ‘yancin wanzuwa. Yayin da ciwon daji...
    Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara wajen shiga sahun kasashen duniya a ranar cutar hawan jini ta duniya. Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tunawa da ranar hawan jini ta duniya, wanda aka gudanar a Kano.     A taron tunawa da ranar, ma’aikatar ta shirya wani tattaki da taron manema labarai da nufin wayar da kan jama’a game da cutar hawan jini da inganta rigakafinta, ganowa da sarrafa shi.     An fara tattakin ne a ma’aikatar lafiya ta hanyar gidan waya da karfe 8:30 na safe kuma aka kammala a cibiyar bayar da agajin gaggawa (EOC) da ke cikin asibitin...
    Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da kullum, ciki har da sojoji da ‘yan sanda,” Dbeibah, ya fadi haka ne biyo bayan al’amuran tsaro da suka faru a babban birnin kasar, Tripoli, a ranar litinin bayan kisan Abdul Ghani al-Kikli, wanda aka fi sani da “Ghaniwa,” kwamandan kungiyar da ake kira “Stability Support Apparatus”. Bayanin na Dbeibah ya zo ne a yayin wani taron tsaro da aka gudanar a makon da ya...
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri. Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya. Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar Muhimmanci – Gwamna Abba Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa An shirya gudanar da sallar jana’izarsa yau Litinin a ƙofar gidansa da ke unguwar State Low-Cost, Maiduguri. Abokan aiki da ‘yan uwa sun bayyana baƙin ciki game da rasuwar, suna yaba masa da halayensa na kirki da ƙwarewarsa a fannin jarida. Daga kanmu, magana ta...
    jami’in yaɗa labaran hukumar Abdullahi Sani Suleiman ya bayyana fina-finan da aka dakatar kamar haka: 1. Dakin Amarya   2. Mashahuri   3. Gidan Sarauta   4. Wasiyya   5. Tawakkaltu   6. Mijina   7. Wani Zamani   8. Labarina   9. Mallaka   10. Kudin Ruwa   11. Boka Ko Malam   12. Wa yasan Gobe   13. Rana Dubu   14. Manyan Mata   15. Fatake   16. Gwarwashi   17. Jamilun Jiddan   18. Shahadar Nabila   19. Dadin Kowa   20. Tabarma 21. Kishiyata 22. Rigar Aro Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a? NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba. Domin sauke shirin latsa nan
    Rundunar Sojin ƙasar nan ta tabbatar da kashe shahararren ɗan bindiga kuma na hannun daman Bello Turji, Alhaji Shaudo Alku a wani hari da aka kai da jiragen yaƙi. Rundunar Operation Fasan Yama ce ta kai harin a ranar Lahadi 18 ga wannan watan nan na Mayu a wata maɓoyar ƴan bindiga da ke kusa da makarantar firamare a garin Tunfa da ke ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto. Sojoji 20 Sun Ɓace Bayan Harin Da ISWAP Suka Kai Marte Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 2, Sun Ƙwato Shanun Sata 1,000 A Taraba A cewar rundunar sojin, ɗan bindiga Alku, ya zo Nigeriya ne sakamakon wata gayyatar taro da ƴan bindiga suka yi masa inda aka far musu a hanya...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya gargadi Amurka game da gabatar da “bukatun da ba su dace ba” a tattaunawar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da inganta sinadarin Uranium tare da ko ba tare da wata yarjejeniya da Washington ba. Abbas Araghchi na mayar da martani ne ga furucin da manzon shugaban kasar Amurka a yankin Steve Witkoff ya yi cewa, Washington ba za ta bar Iran ta samu karfin sarrafa sinadarin Uranium ba, ko da kashi 1%. Mista Araghchi, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na Iran, ya shaida wa manema labarai cewa, irin wadannan kalamai sun kauce wa tattaunawar. Har ila yau ministan harkokin wajen na...
    Manyan jami’ai daga kasashe da dama da ke halartar taron tattaunawa na Tehran sun yi kira da a tattauna domin tunkarar manyan al’amura a yankin. Manyan jami’ai daga kasashe 53 da suka hada da ministoci da masana da ne ke halartar taron na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen Oman Badr bin Hamad Al Busaidi ya ce a halin yanzu yankin yammacin Asiya na fuskantar kalubale da dama da ke bukatar tattaunawa cikin gaggawa. A yayin jawabin nasa, Ministan harkokin wajen Oman ya bayyana matukar damuwarsa kan tashe-tashen hankula da kisan kiyashin da al’ummar Falasdinu ke fuskanta, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin wani abin takaici a duniya. A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Tajikistan ya jaddada bukatar yin...
    Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe ‘yan jarida 5 na Falasdinawa a wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, lamarin da ya kai adadin ma’aikatan yada labaran da aka kashe tun farkon yakin Isra’ila a zirin Gaza zuwa 222. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da dan jarida mai daukar hoto Aziz al-Hajjar, da matarsa, da ‘ya’yansu, wadanda aka kashe a ranar Lahadi, lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a gidansu da ke unguwar Saftawi a arewacin Gaza. A gefe guda kuma, an kashe dan jarida Ahmad al-Zinati tare da matarsa, Nour al-Madhoun, da ‘ya’yansu, Mohammad da Khaled, a lokacin da aka kai wa tantin su hari a Khan Younis a...
    Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Birtaniya a birnin Tehran, biyo bayan tsare wasu ‘yan kasarta da dama ba bisa ka’ida ba a kasar. Shugaban bangaren kula da sashen yammacin turai a ma’aikatar harkokin wajen kasar ya yi kakkausar suka da nuna adawa da matakin na gwamnatin Birtaniyya, da kuma zarge-zargen da ba su dace ba da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Jami’in ya ce tsare ‘yan kasar Iran ya sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma hakkokin bil’adama da aka amince da su, saboda an tuhume su ba tare da wata hujja ba. Ya kara da cewa ‘yan kasar Iran da ake tsare da su, an kuma hana su harkokin ofishin jakadanci da...
    Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekara 20 ta Afrika ta Kudu ta lashe kofin gasar CAN a karon farko bayan da ta doke takwararta ta Morocco (1-0) a wasan karshe da aka buga a birnin Alkahira jiya Lahadi. Kafin hakan Najeriya ta samu matsayi na uku a gasar bayan da ta doke Masar mai masaukin baki a bugun fenariti (1-1; 4-1 a bugun fenariti). Kasashen guda hudu da suka fafata a wasan kusa da na karshe wato (Afirka ta Kudu, Morocco, Najeriya, Masar) sun samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 20 a kasar Chile da za’a gudanar daga ranar 27 ga Satumba zuwa 19 ga Oktoba, 2025.
    Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da haska shirin Labarina, Dadin Kowa da wasu ƙarin fina-finan Hausa guda 20 a kafafen Internet ko gidajen talabijin. Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne a ƙoƙarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara dora masana’antar Kannywood a kan saiti. A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar da daren Lahadi, fina-finan da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Labarina, Dadin Kowa, Manyan Mata, Garwashi, Jamilun Jidda da kuma Gidan Sarauta. Sanarwar ta ce umarnin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, bayan wani zamanta da kuma tattaunawar da ta gudanar. An kama ƙasurgumin ɗan...
    A wancan lokacin,Mrs. Bintu M.Sadik, cewa tayi  Sir S.M. Banaman shi ne Shugaban Kwalejin na farko duk kuma Malaman Turawa, daga baya ne aka dauke Hausawa ‘yan asalin wurin saboda su koyar da Hausa da kuma al’amarin daya shafi addinin musulunci.Ta ce mshahuran ‘yan Arewa sun halarci Kwalejin daga cikinsu akwai Firayim Minista na farko Abubakar Tafawa Balewa,Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan  Arewa, da kuma Sir Kashim Ibrahim,  da dai sauran wasu duk sun halarci Kwalejin ta Katsina An samu labarin kasar Katsina ta taba kasancewa wata babbar cibiyar Kasuwanci ta Sahara. Wannan  shi tun  lokacin da aka hade Arewa da Kudancin Nijeriya Katsina tana daya daga cikin wuraren da  hanyar jirgin kasa ta bi ko kuma Layin Dogo ...
    Aƙalla ’yan kasuwa 15 ne aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu garuruwa da ke Ƙaramar Hukumar Agatu a Jihar Binuwai. ’Yan kasuwar na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Oweto da yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai musu hari a kusa da garuruwan Ogwumogbo da Okpo’okpolo. An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa Tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce mutane da dama sun jikkata. Ya ce mutum biyar aka kashe a kusa da wani ƙaramin rafin da ake kira Abekoko. Shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu...
    Wata takardar bayani da aka wallafa a yau Lahadi 18 ga watan Mayun shekarar 2024, ta nuna cewa, jimillar kudin da aka samu a masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam na kasar Sin ta kai yuan biliyan 575.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 79.9, a shekarar 2024, adadin da ya karu da kaso 7.39 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Takardar game da bunkasar masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam ta kasar Sin, ta yi nuni da cewa, a karshen shekarar 2024, yawan adadin manhajojin fasahar sadarwar tauraron dan Adam a kasar Sin ya zarce 129,000, kuma an sanya wa kusan wayoyin salula miliyan 288 a kasar tsarin da suke iya amfani da sadarwar daga tsarin amfani da tauraron dan...
    Ana zargin wasu makiyaya sun kashe mutane 15 a yankunan Ogwumogbo da Okpo’okpolo na ƙaramar hukumar Agatu dake jihar Benuwe. Majiyoyinmu sun bayyana cewa waɗanda aka kashe sun kasance ‘yan kasuwa ne da ke dawowa daga kasuwar Oweto a Agatu lokacin da maharan suka fito daga daji suka harbe su, inda suka kashe 15 nan take. An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta Tsohon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Agatu, John Ikwulono, ya tabbatar da harin da aka kai wa ‘yan kasuwar a ranar Asabar da yamma, inda ya bayyana cewa maharan sun kwace kuɗaɗe da kayayyakin waɗanda aka kashe kafin su gudu cikin daji. “Har yanzu wasu...
    Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025. Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin tashin zuwa ƙasa mai tsarki. An tafka asara bayan gobara ta ƙone Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Ya ce an biya wa kowane maniyyaci Riyal 600. Mahajjatan da za su fara tafiya sun fito ne daga ƙananan hukumomin kudancin jihar, kuma za su tashi a jirgin kamfanin Max Air. Gwamna Radda ya...
    Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...