Natasha Da Akpabio: Sanata Natasha Ta Gabatar Wa Majalisar Dattawa Ƙorafinta
Published: 5th, March 2025 GMT
Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance.
Sanata Natasha Ta Gabatar Da ƘorafintaA ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar.
Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.”
Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta.
Martanin AkpabioSanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya yi watsi da zarge-zargen da ta ke masa.
“Na miƙa wannan ƙorafi ga kwamitin ladabtarwa don yin nazari. Amma ina so na fayyace cewa ba ni da wata alaƙa da zargin cin zarafi da aka yi min.”
Ya ci gaba da cewa bai taɓa cin zarafin wata mace ba, yana mai bayyana cewa mahaifiyarsa ta koya masa mutunta mata.
Ya kuma ƙara da cewa yana da ‘ya’ya mata huɗu, don haka ba zai taɓa aikata abin da ake zarginsa da shi ba.
Ƴan Majalisa Ba Su Goyi Bayan Natasha BaDuk da cewa Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafinta, kusan dukkanin ƴan majalisar da suka yi tsokaci ba su goyi bayan ta ba.
Hatta Sanatoci mata ƴan uwanta ba su mara mata baya.
Wasu sanatocin sun ce irin wannan ƙorafi bai dace a gabatar da shi a majalisa ba, yayin da wasu suka buƙaci a yi ganawar sirri kan batun.
Sai dai Akpabio ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin akwai wakilai daga Birtaniya da suka halarci zaman majalisar domin nazarin yadda al’amura ke gudana.
Tuni lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin majalisa da wajenta,
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Cin Zarafi Majalisar Dattawa Zargi gabatar da ƙorafi a gabatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Karamar Hukumar Bubura Ta Kai Tallafin Kayayyakin Abinci Cibiyar Gyaran Hali
Daga Usman Mohammed Zaria
Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar.
Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya.
A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali.
A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa taimakon ya zo ne a lokacin da ake matuƙar buƙata.
A yayin hudubarsa ga fursunonin, Babban Limamin Babura, Imam Salisu Aliyu, ya shawarce su da su nemi gafarar Allah, su kuma kara kusanci gare Shi, tare da rungumar canji mai kyau.
Kayan tallafin da aka bayar sun haɗa da buhunan masara, gero, shinkafa, garin rogo, man gyada, sinadaran dandano, gidan sauro da maganin kwari.
Manyan baƙin da suka raka shugaban ƙaramar hukumar a lokacin ziyarar sun haɗa da Hakimin Babura, Sarkin Bai Ringim, Alhaji Muhammad Nata’ala Mustapha, jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin, CSP Abdu Jinjiri, da jami’in Hukumar Tsaro ta Civil Defence, CSC Sunusi Usman Chamo, da sauransu.