Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Cika Kwanaki 713 Suna Kisan Kiyashi A Zirin Gaza
Published: 18th, September 2025 GMT
Gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan Gaza a rana ta 713 a daidai lokacin da kasashen duniya ke shiru
Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza a rana ta 713, inda suke ci gaba da yin amfani da ruwan bama-bamai ta sama da na bindigogi, inda suka kashe mutane da ke fama da yunwa da rashin muhallan, tare da goyon bayan siyasa da soji na Amurka, gami da shirun kasa da kasa, da gazawar da ba a taba gani ba daga kasashen duniya.
Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama ta sama tare da aiwatar da kisan kiyashi, lamarin da ya ta’azzara wahalhalun da mutane sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu ga kuma bullar masifar tsananin yunwa. Hare-haren wuce gona da iri kan birnin Gaza ya kara tsananta da nufin raba su da mazaunansu da kuma rusa yankin baki daya.
Majiyoyin lafiya a asibitocin Gaza sun tabbatar da mutuwar wasu Falasdinawa da dama da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka harba tun daga wayewar garin ranar alhamis, musamman a birnin Gaza, inda rikicin yunwa da barna ke kara ta’azzara yayin da sojojin mamayar Isra’ilaa ke neman korar mazaunanta gaba daya.
Asibitin Al-Awda da ke birnin Nuseirat ya bayar da rahoton cewa, a daren jiya ya karbi shahidai hudu tare da jikkata wasu 10, sakamakon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida da ke Block 7 na sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke tsakiyar zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa September 18, 2025 Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai September 18, 2025 Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar Kasuwanci Da HKI September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji.
“Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza.
Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.”
Sanarwar ta karyata ikirarin CENTCOM cewa “kusan kasashe 40 da kungiyoyin kasa da kasa suna aiki a Gaza,” yana mai jaddada cewa ainihin adadin kungiyoyin da ke ba da agajin jin kai bai wuce 22 ba, “yawancinsu suna fama da cikas da kuntatawa saboda matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanya.”
Haka kuma ta soki shiru da CENTCOM ta yi game da laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi a kullum tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
“Shirun da rundunar sojin Amurka ta yi a gaban wadannan laifukan na yau da kullum, yayin da take aiki don yada labaran da ba su da tushe game da rundunar ‘yan sandan Falasdinu, ya nuna cikakken son kai ga mamayar Isra’ila da kuma rashin sahihancinta a matsayin wacce ya kamata ta kasance mai shiga tsakani,” in ji sanarwar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci