Aƙalla mutane 20 ne suka mutu bayan wani hari da jiragen sama na sojojin Najeriya (NAF) ya kai domin fatattakar ’yan bindiga a a Jihar Zamfara.

Jiragen sojin sun kashe wasu ’yan sa-kai bisa kuskure, a yayin da ’yan sa-kan suke ƙoƙarin fatattakar ’yan bindiga da suka kai hari a yankin Mani a Ƙaramar Hukumar Maru.

Jiragen sojin sun kai hare-haren ne domin fatattakar ’yan bindiga da suka kai wa manoma hari a kan babura da rana tsaka.

Mazauna yankin sun ce bayan ’yan bindiga sun sace manoma sama da 50 ne jirgin sojin ya amsa kiran gaggawa, amma aka samu kuskure ya kashe wasu ’yan sa-kai da ke ƙoƙarin fatattakar maharan.

Bom ɗin Boko Haram ya kashe fasinjoji 9 a tashar mota a Borno NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa

Wani mazaunin yankin ya shaida wa kafar BBC cewa, “Mun sanar da jami’an tsaro bayan harin, amma kawai sai muka ga jirgin ya zo ya kashe ’yan sa-kai na mu.”

Wani mazaunin garin ya ce, a yayin da jama’a ke ƙoƙarin taimaka wa wadanda aka kai wa hari, sai ga wani jirgin saman soji ya iso.

Ya ce, “’Yan bindigar sun tafi da mutane 50, amma yayin da muke ƙoƙarin kai ɗauki, sai muka ga jirgin soji, kuma ya fara harbin mu. Kowa ya gudu neman mafaka,” inda ya ƙara da cewa sun yi kamar matattu ne don su tsira.

Wani mazaunin kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara yawa, inda ya buƙaci a yankin amma su yi taka-tsantsan yayin gudanar da ayyukan.

Har yanzu sojojin Najeriya ba su ce komai ba game da lamarin.

Idan ba a manta ba, ire-iren wannan harin huskure ya faru a baya a yankin Jihar Zamfara. A watan Janairun 2025, wani harin jirgin saman sojin Najeriya ya kashe mutane 16 bisa kuskure, ciki har da ’yan sa-kai da manoma, a ƙauyen Tungar Kara a Jihar Zamfara, bayan an zaci su ’yan bindiga ne.

Hakazalika, a watan Disambar 2024, wani harin jirgin sama a Jihar Sakkwato ya kashe fararen hula 10 a sakamakon abin da Gwamnan jihar ya bayyana a matsayin harin kuskure kan fararen hula.

A watan Disamban shekarar 2023 wani jirgin soja ya kai irin harin inda ya kashe sama da fararen hula kimanin 100 a wurin taron Mauludi a yankin Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ke ƙoƙarin yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu

“Sun jikkata mutane biyu tare da sace maza, mata da yara da dama.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  • Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Na Isra’ila Da Makami Mai Linzami Nau’in Flasdinu
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ƙauyen Katsina, Sun Jikkata Mutane 2, Sun Sace Wasu
  • Ɗan Shekaru 15 Ya Kashe Wani Matashi Kan Rikicin Gona A Jigawa
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Gwamnatin Zamfara Ta Kira Babban Taron Tsaro Tare Da Bayyana Sabbin Dabaru Na Yakar ‘Yan Bindiga.
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kwara Ta Taimaka Wajen Hana Lalacewar Wani Bene A Ilorin
  • APC Ta Zabi Kamilu Sa’idu A Matsayin Dan Takarar Kaura Namoda Ta Kudu A Zamfara
  • Jami’in Shari’ar Kasa Da Kasa Ya Bayyana Cewa: Harin Da Aka kai Kan Iran Babban Laifi Ne