A soma duba watan Sha’aban ranar Laraba — Sarkin Musulmi
Published: 28th, January 2025 GMT
Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Sha’aban na kalandar musulunci daga daren Laraba.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a fadar, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Kwamitin ganin wata na Nijeriya a Fadar Sarkin Musulmi ya ce ranar Laraba ce za ta zama 29 ga watan Rajab, 1446, daidai da 29 ga watan Janairun 2025.
Sanarwa da Fadar Sarkin Musulmin ta fitar, ta ce idan aka ga watan a kai rahoto zuwa ga hakimi ko kuma mai unguwa mafi kusa wanda shi kuma zai sanar da fadar.
Watan Sha’aban dai yana da muhimmanci a kalandar Musulunci, saboda daga shi ne za a shiga watan azumin Ramadan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fadar Sarkin Musulmi Jinjirin Wata Sarkin Musulmi Watan Sha aban Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
APC Zamfara Ta Taya Sabon Sarkin Katsinar Gusau Murna
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma nadin sarautar Allah, wanda ya zo ne jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi sarki, Alhaji Ibrahim Bello.
Sanarwar ta nuna cewa Alhaji Abdulkadir kyawawan halaye na gaskiya, kwazonsa, sadaukarwa, biyayya ga mahaifinsa da ya rasu, da kuma mutunta al’umma ta kowane hali, sun nuna shi ne wanda ya cancanta.
A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na farko a tarihin masarautar da wani dan da ya haifa kai tsaye ya gaji mahaifinsa, wanda jam’iyyar ta ce hakan yana nuna yardar Allah da kuma ci gaba da gadon adalci na marigayi sarki.
Jam’iyyar APC ta bukaci sabon sarkin da ya kiyaye dabi’u da abubuwan gado na mahaifinsa da kakanni, musamman na fitaccen malamin addinin musulunci kuma shugaba, Sambo Dan-Ashafa.
Jam’iyyar ta yi addu’ar Allah ya yi masa jagora, ya kare shi, da kuma hikimar Sarki don ya jagoranci al’umma zuwa ga zaman lafiya da wadata.
Har ila yau, ta ba da tabbacin ci gaba da goyon bayanta da shirye-shiryenta na neman shawara, jagoranci, da albarka daga sabon sarki.
Daga karshe sanarwar da sakon fatan alheri ga mai martaba sarki da daukacin masarautar Gusau.
REL/AMINU DALHATU