2025-11-03@22:01:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4557
«Old Trafford»:
Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open. ’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian...
Kakakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, He Yadong ya sanar da cewa, za a gudanar da taron CIIE karo na 8 a birnin Shanghai daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Nuwamba. Kuma firayim ministan kasar Sin Li Qiang zai halarci bikin bude taron da sauran ayyukan tare da gabatar da...
Daruruwan matafiya ne suke zaman dirshan a filin saukar jiragen sama na kasar Tanzania saboda rikicin da ya barke sanadiyyar rikicin zaben shugaban kasa, da Samia Suluhu Hassan ta lashe da kaso 97%,kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. An soke dukkanin tafiye-tafiyen jiragen sama da hakan ya sa matafiya na kasashen waje da dama...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce; sabanin da yake a tsakanin Jamhuriyar musulunci da Amurka na tushe ne, ba wani abu ne na sama-sama ba. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi da dubban dalibai da iyalan shahidai a jajiberin ranar “Fada Da Masu Girman Kai...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai...
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mullki na biyu a matsayin shugabar Tanzaniya, duk da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen da aka gudanar a makon jiya. A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar cikin matakan tsaro a Dodoma, babban birnin ƙasar, an rantsar da shugabar a wani wurin da ba a bai...
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT
A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36. Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya. Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa. NAJERIYA A YAU: Ko...
Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza Ismail al-Thawabteh y ace Rundunar sojin Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. al-Thawabteh, darektan ofishin, ya shaida wa kamfanin dinalancin labarai na Anadolu cewa laifukan sun hada da hare-haren da Isra’ila ta kai...
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta sanar da cewa mutane 1,205 sun rasa matsugunansu a Sudan a garuruwan da suka hada da Bara da Umm Ruwaba a Jihar Kordofan ta Arewa, yayin da wasu 360 suka rasa matsugunansu daga Al-Abbasiya da Delami a Kudancin Kordofan saboda tabarbarewar rashin tsaro. A cikin...
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara. Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano,...
Wani magidanci, Malam Jibrin Rabi’u, ya bayyana yadda matarsa, Khadijat Ado, ta ɓace a gidansu da ke unguwar Life Camp a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata, sannan kuma aka gano ta a Sakkwato washegari. Ya shaida wa wakilinmu da yammacin Lahadi, cewa ya dawo gida a ranar Alhamis, sai ya tarar da matarsa...
Kakakin hukumar kula da kanana yaran ta majalisar dinkin duniya tess ingram ta bayyana cewa yanayin da yara ke ciki a yankin gaza yayi muni sosai, inda sama da yara miliyan daya dake gaza suke bukatar taimakon gaggawa na ruwan sha da kuma abinci Ingram ta fadi a wata hira da aka yi da ita...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas tayi watsi da zargin da Amurka ta yi mata a baya bayan nan na cewa mayakanta sun wawushe kayayyakin agaji da wata mota take dauke da shi a yankin Gaza, ta bayyana zargin a matsayin karyace kawai mara tushe balle madafa, tace Amurka na wannan zargin ne...
A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta...
Kakakin gwamnatin kasar iran fateme muhajirani ta bayyana cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta tabbar da karbar sakon da ya kunshi batun fara tattaunawar diplomasiya tsakaninsu da Amurka, sai dai za’a bayyana yadda za ta kasance da kuma abubuwa da ta kunsa a nan gaba. Wannana mataki ya nuna cewa ana iya ci gaba...
Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin. A ranar 26 ga Oktoba, dakarun...
Daga Usman Mohammed Zaria Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar. Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya...
Allah Ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood, Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Dadin Kowa rasuwa. Wannan na cikin wani saƙo da fitacciyar marubuciya, Fauziyya D. Sulaiman ta wallafa a shafinta na Facebook a daren ranar Lahadi.
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe. Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar. Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai...
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025 Wasanni Barcelona Na Shirin Ɗauko Victor Osimhen Na Galatasaray October 30, 2025
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI). Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da...
Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba....
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama...
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya...
Rahotanni da muka samu sun nuna cew wasu yan ta’adda sun kashe wasu dakarun sa kai guda biyu a kudu masu gabashin iran a yankin sisitan Baluchistan. Jami’In huda da jama’a na dakarun kare juyi yayi karin harke game da harin da aka kai, yace an kashe mutane ne yayin da suke kokarin ketare da...
Taron kaddamar da rabar da taraktocin noman, ya gudana ne a Shalkwatar Ma’aikatar Kula da Aikin noma da kuma yin Noman Rani da ke garin Kalaba. Kazalika, taron ya samu halartar ‘yan Majalisa da Sarakunan Gargajiya da kungiyoyin manoma mata da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da ke jihar da abokan...
A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3, Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin...
Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar wuri a matsayin ci gab da nuna kin amincewa da sakamamon zabe. A can garin Marwa dake a matsayin babban birnin Arewacain kasar,dukkanin harkokin yau da kullum sun tsaya kacokau....
Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher. Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka. Ministan harkokin wajen kasar...
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan. A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da...
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su...
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza...
Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya. Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son...
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA ...
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama...
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5 yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba, A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake...
Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II. Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da...
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a. Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne...
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League. Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4. Kotu ta...
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa. A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya...
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa. Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis,...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta raba zunzurutun kuɗi naira miliyan 63.4 ga iyalan jami’anta 84 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Rundunar ta raba kudin ne a ƙarƙashin tsarin inshorar rayuwa da kuma tsarin kula da lafiyar iyali na Sufeto Janar na ’yan sanda. An gudanar da rabon kuɗin ne a ranar...