2025-06-13@17:46:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3938

«makamashin nukliya ta»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan ba da jimawa ba al’ummar Nijeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar. Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa da ke yankin Lekki a Jihar Lagos. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya Mijina bai saci kuɗin Nijeriya ba — Maryam Abacha Ya ce sauyin da al’umma za su gani a yanzu, ba wai na rage farashin man ba ne kaɗai, wanda zai sauya baki ɗaya yadda ake gudanar da harkokin mai ne a ƙasar. “A yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarcemu, kuma ya ba mu ƙarin makamashi, ina mai...
    Iran ta bayyana cewa: Tace sinadarin Uranium wani bangare ne na bunkasa masana’antar nukiliya kuma ba zata amince kan tattaunawa ko yin sulhu kansa ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Sarrafa sinadarin Uranium wani bangare ne na masana’antar nukiliya, kuma batu ne da ba za a tattaunawa kansa ko yin sulhu kansa ba, kasancewarsa masana’antar cikin gida ne kuma an shefe tsawon shekaru da dama ana sarrafa shi a cikin kasa, sakamakon kokarin da masana kimiyya suka yi. babu wata kasa da ke da ikon bayyana ra’ayi kan wannan hakkin. A cikin taron manema labarai na mako-mako, Baqa’i ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, yana mai jaddada...
    Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...
    Babban darektan hukumar IAEA ya zama tamkar wata yar tsana ce a hannun kasashen Yamma don dakile shirin nukiliyar Iran An fara taron kwata-kwata na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 35 mambobi hukumar Bisa la’akari da rahoton da babban daraktan ya fitar game da sa ido da tabbatar da shirin nukiliyar Iran karkashin yarjejeniyar kare kai da kuma tsarin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa ta (JCPOA) na daya daga cikin batutuwan da za a tattauna. Babban darektan hukumar ta IAEA Rafa’el Grossi ya sanar a wani rahoto da ya fitar a makon da ya gabata cewa; Yawan sinadarin uranium da Iran ke da shi ya ninka har...
    Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza Kwamandojin sojojin mamayar Isra’ila sun yi garkuwa da jirgin ruwan farare hula Madeleine, wanda ke yunkurin karya killace yankin Zirin Gaza da aka yi a kokarinsu na shigar da kayan agaji ga al’ummar yankin da suka rage. Sojojin mamaya sun garkuwa da masu fafutuka tare da kai su tashar ruwan Ashdod. Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin sun yi tir da laifin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata. Kungiyar Hamas ta bayyana shi a matsayin ta’addancin kasa da kasa. A wani sabon laifin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa da na jin kai, sojojin...
    Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.” Sanarwar ta...
    Da safiyar yau Talata ne dai sojojin HKI su ka kai wani hari a garin “Aytas-sha’ab’ dake kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane biyu. Kafafen watsa labarun Lebanon sun ambaci cewa, mutanen biyu da su ka yi shahada sun hada da wani makiyayi da dansa da suke kiwon dabbobinsu a burtalin dake kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya.  A jiya Litinin ma dai wani jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniyar, ya kai hari a garin Nabadhiyyah. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko harin na jiya ya yi sanadiyyar shahadar wasu ko jikkata. Sai dai kuma gobara ta tashi a cikin motar da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa harin na jiya. Daga...
    A wa’adinsa na farko a 2017, Trump ya kafa irin wannan haramci da ya shafi ƙasashe bakwai ns Musulmai, wanda ya jawo gagarumar suka daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam. Masana harkokin tsaro da na diflomasiyya na ganin cewa wannan sabon mataki na iya ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen da abin ya shafa, musamman a lokacin da ake buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya wajen fuskantar manyan ƙalubale na tsaro da tattalin arziƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.” Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar. Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar. Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba. “Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba. “Dole ne a daina wannan.” Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A bara ne dai dam ɗin Alo ta cika da ruwa har wani ɓangare ya buɗe, lamarin da ya haddasa mummunar ambaliya a Maiduguri, inda aka rasa rayuka da dukiyoyi da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya zanta ta wayar tarho da firay ministan HKI Benyamin Natanyahu kan kasar Iran da kuma yakin Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa majiyar ofishin Natanyahu ta bayyana cewa tattaunawar tana zuwa ne a dai-dai lokacinda rikici da yaki yake ci gaba a gaza, da kuma tattaunawa kan shirin Nuclear kasar Iran ke ci gaba. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Amurka na jirin jawabin da kasar Iran zata mayar masa dangane da shawarar da ya gabatar na warware matsalar tashe makamancin Yuranium a Iran. Har’ila yau ya na jiran jawabin da kungiyar Hamas za ta bayar kan yarjeniyar  dakatar da yaki a Gaza. Shugaban dai yana cikin matsin...
    Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje. Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana...
    Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi samun isasshen abinci mai lafiya da kuma wadatacce a cikin kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan kiwon lafiya Muhammad Reza Zafarkandi yana fadar haka a jiya litinin a taron raya ranar abinci da duniya wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar gidajen radio da talabijin a nan birnin Tehran. Ministan ya kara da cewa, samun abinci mai gina jiki da kuma bada sinadaran da jiki yake bukata yana daga cikin abubuwan da suke bada lafiya ga jiki. Har’ila yau wannan yana kwantar da hankalin mutanen ko wace kasa wacce...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa.   Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka saboda jami’in ya ki ya mika wayarsa. Ko me mahukunta suke yi don hana aikata wannan laifi? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya gana da babbar ministar kudin Birtaniya Rachel Reeves jiya Lahadi a birnin Landan, inda suka zurfafa musaya game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da hadin gwiwa a fannin hada-hadar kudade, da sauran batutuwan dake janyo hankulan kasashensu. He, wanda kuma shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki da harkokin cinikayya tsakanin Sin da Birtaniya, ya ce kamata ya yi kasashen biyu su yi aiki tare, wajen aiwatar da muhimman kudurori da shugabannin kasashen suka cimma, su kuma ingiza nasarar dandalin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Birtaniya, da zurfafa musaya da hadin gwiwa a dukkanin sassan tattalin arziki da cinikayyarsu, da ingiza cimma moriya tare, da wanzar...
    Uwargidan tsohon shugaban Nijeriya, Maryam Abacha ta musanta zarge-zargen da ake yi wa mijinta na wawure maƙudan kuɗaɗen ƙasar a lokacin da yake kan karagar mulki. A wata hira da aka yi da ita a kafar talabijin ta TVC a yayin cika shekara 27 da rasuwar Abacha, Maryam ta nanata cewa bai sace kuɗaɗen Nijeriya, tana mai cewa, da gangan aka sauya manufarsa ta adana dukiyar ƙasar a ƙetare. Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe  Maryam Abacha ta ƙalubalanci waɗanda ke zargin mijinta da wawure dukiyar talakawa da su gabatar da gamsasshiyar hujja kan zarge-zargensu, tana mai ɗiga ayar tambaya kan wane ne shaida kan kuɗaɗen da...
    Wata mata, Shidoo Tortiv da ta tsere daga matsugunninta sanadiyyar matsalar tsaro ta haifi ’yan huɗu a gidan ’yan uwa da take zaman gudun hijira a Jihar Benuwe. Shidoo Tortiv wadda ta fito daga ƙauyen Ucha na Ƙaramar Hukumar Gwer ta Yamma sun tsere tare da mijinta, Wilfred Tortiv sakamakon matsalar tsaro da ta yi kamari, inda suka nemi mafaka a gidan ’yan uwansu. Bom ya kashe masu yawon murnar sallah a Sakkwato Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza Mista Wilfred Tortiv Mijin matar ya shaida wa wakilinmu a ranar Litinin cewa ta haifi jariran ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Asabar a gida bayan nakuda ta kama ta kuma ungozomai suka karbi haihuwar...
    Kimanin mutum bakwai sun riga mu gidan gaskiya bayan tarwatsewar wani abun fashewa da ake zargi mayaƙan Lakurawa sun dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Aminiya ta ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su da ke kan babura na hanyarsu ta dawowa daga yawon bikin sallah a ƙauyen Gwabro. Isra’ila ta ƙwace jirgin ruwa a hanyar kai agaji Gaza Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe Bayanai sun ce an dasa abun fashewar ne a ƙarƙashin wata itaciya da ke zaman wurin hutawar dakarun sojoji a lokacin da suka fito sintiri a yankin. Majiyiyo sun ce mutum shida sun mutu nan take yayin da ɗaya daga cikin wasu mata biyu yara da suka jikkata ta...
    Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda da dama a cikin wasu jerin hare-hare na sama da na ƙasa da suka kai sansanonin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke Nzalgana, a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce hare-haren da sojojin suka ƙaddamar da sanyin safiyar Litinin 9 ga watan Yuni sun yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan Boko Haram a ƙauyukan Ngorgore da Malumti, Ameer Malam Jidda. Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba Zaɓen 2027 ba — ACF NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Duk da cewa sanarwar...
    Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce ta kashe ’yan ta’adda da dama a cikin wasu jerin hare-hare na sama da na ƙasa da suka kai sansanonin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da ke Nzalgana, a ƙaramar hukumar Gujba ta Jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Nijeriya. Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce hare-haren da sojojin suka ƙaddamar da sanyin safiyar Litinin 9 ga watan Yuni sun yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan Boko Haram a ƙauyukan Ngorgore da Malumti, Ameer Malam Jidda. Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba Zaɓen 2027 ba — ACF NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Duk da cewa sanarwar...
    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027. ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tiinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin da ƙungiyar cewa hakan ya yi wuri. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Ɓarawon waya ya kashe babban jami’in soja da wuƙa a Kaduna Wannan kira dai na kunshe cikin wata sanarwar yi wa musulmi barka da Sallah Babba da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar. Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da...
    Jiragen ruwan wadanda aka bai  wa sunan: “Jajurcewa” za su tashi ne daga Tunisiya jim kadan bayan da sojojin HKI su ka hana wani jirgin ruwan dake dauke da masu fafutuka daga kasashen turai,isa gabar ruwan Gaza. Jirgin ruwan na ” Jajurcewa’ zai bi ta ruwan Libiya, sannan Masar daga can kuma ya nufi gabar ruwan Gaza. Jiragen ruwan dai suna dauke da masu fafutuka 7,000 daga kasashen Tunisiya, Moroko, Aljariya, Murtaniya, da Libiya. Kwamitin kasa da kasa domin karya killace Gaza, wanda ya shirya wannan tafiyar, ya kuma yi wani kiran ga ‘yan fafutuka a duniya da su shirya wasu tafiye-tafiyen ta ruwa zuwa Gaza, domin kawo karshen killace yankin da aka yi tun 2007.
    Ya ce dukkan wadanda aka sacen, da suka hada da mata 9 da maza 2, an kubutar da su ba tare da wani rauni ba. PPROn ya bayyana cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don ganowa tare da cafke ‘yan bindigar da suka tsere, inda rundunar ‘yansandan ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka a jihar. ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a Katsina     Rundunar ‘yansandan jihar Katsina tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane 11 daga hannun masu garkuwa da mutane a daren Lahadi 8 ga watan Yuni 2025.   Wannan nasarar an sameta ne da misalin karfe 10:30...
    Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu. Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan. Haka nan kuma wuraren da ake killace su, sun yi kadan. Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara. A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar sauya musu gandun daji da wuraren da aka killace...
    A daidai lokacin da kungiyar kasashen  tsakiyar Afirka ta tattalin arziki        ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta. Bayanin da gwamnatin kasar ta Rwanda ta fitar ya kunshi cewa; Kasar Rwanda tana nuna takaicinta akan yadda kasar DRC take amfani da kungiyar tattalin arziki ta  tsakiyar Afirka a matsayin wani makamin a hannunta.” Bayanin gwamnatin ta Rwanda ya kara da cewa: Yadda DRC take amfani da wannan kungiyar ya sake fitowa fili a yayin taron kungiyar karo na 26 a Malabo, ta yadda aka kau da kai akan hakkin Rwanda na shugabancin karba-karba,kamar yadda yake a cikin doka ta shida ta kundin kungiyar. Hakan kuma ya faru ne sanadiyyar shiftar DRC ga kungiyar.” A...
     Majiyar sojan Rasha ta sanar da cewa; Tun daga watan Febrairu na 2024, zuwa yanzu ta tarwatsa tankokin yaki samfurin ” Abrams” kirar Amurka da ta bai wa kasar Ukiraniya har guda 26. Ya zuwa yanzu adadin wadannan tankokin da su ka rage a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5, ba domin adadinsu 31 ne. Kamfanin dillancin labarun ” Sputnik” ne ya bayyana cewa; adadin  tankokin yakin  na Amurka da su ka saura a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5 ba. Tun a watan Janairu na 2023 ne dai tsohon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya sanar da bai wa Ukiraniya  tankokin yaki samfurin Abrams a karkashin taimakon kayan yakin da take bai wa kasar....
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fara sana’a na cikin manyan jerin kalubalen da ’ƴan Najeriya suke fuskanta sakamakon wasu dalilai wadanda suka hada da rashin ilimi, ko Rashin wanda zai ba su shawara ko kuma, uwa uba, rashin jari.   Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga Ta Kasa – NBS – ta fitar sun nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya suna sha’awar fara sana’a, amma sun kasa saboda rashin jari. Haka kuma, wani bincike da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matasa masu so su fara kasuwanci suna fuskantar babbar tangarda wajen samun jari daga bankuna ko hukumomin gwamnati. Shin ko akwai wata hanya da matasa...
    Jami’an tsaro a kasar Amurka sun cilla tear gas da albarusan roba kan masu zanga-zangar kin amincewa da shirin shugaba Trump na korar wasu Amurkawa wadanda ya kira bakin haure. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa, rikicin wanda aka fara tun kwanaki uku da suka gabata ya tashi ne bayan da jami’an shege da fice na Amurka suka kama wasu yan Latino da nufin korarsu daga kasar. Sun kama mutane da dama a birnin Los Angeles a cikin rana kowa na gani. Gwamnan jihar Calfonia Gavin Newson ya rubuta a shafinsa na X kan cewa basu da wata matsa sai bayan da shugaba Trump ya aiko da ‘Sojojin Tarayya ko “National guard”, kuma wannan keta hurumin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghae ya bayyana cewa gwamnatin kasar amurka tana amfani da karfi inda bai dace ba a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghae yana fadar haka a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa gwamnatin Amurka tana amfani da kujerar VETO a kwamitin tsaro na MDD don hana tsagaita wuta da kuma dakatar da kissan kiyashi a gaza, sannan ta yi amgani da takunkuman tattalin arziki kan alkalai da Jami;an kotun ICC wadanda suke aikinsu na tabbatar da adalci a duniya. Kakakin ma’aikatar ya kara da cewa lokaci yayi wanda kasashen duniya zasu tashi don kawo karshen wadannan mummunan halayen gwamnatin Amurka wadanda suke girgiza asasin dokokin kasa da...
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
    Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ta sanar a jiya Asabar cewa bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta yi masa, memba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai ziyarci Birtaniya tun daga yau Lahadi har zuwa Juma’a 13 ga watan nan na Yuni.   Ana sa ran yayin ziyarar tasa a Birtaniya, He Lifeng zai halarci taron farko na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Myanmar Min Aung Hlaing, sun mikawa juna sakon murnar cika shekaru 75, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 75 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar, bangarorin biyu sun bi ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, da kuma tunanin Bandung, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma kasance abun koyi a fannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da Myanmar, don gaggauta raya hadin gwiwa mai...
    Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji. Lamarin ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College (AFCSC). Matawalle ya yi wa Gwamna Lawal da wasu tayin shiga APC  Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Shaidu sun bayyana cewa yayin da jami’in ke cikin gyara tayar, sai wani mutum ya zo ya buƙaci ya ba shi wayarsa. Jami’in soja ya ƙi bayar da wayar, inda ɓarawon ya ciro...
    Kafofin yada labarai daga Isra’ila na tabbatar da kutsen da akayi wa kasar akan wasu takardun bayyanan sirrin shirinta na nukiliya. Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Iran ta ce ta samu tarin takardun sirri da suka shafi ayyukan nukiliyar Isra’ila. Ministan leken asirin kasar Iran Esmail Khatib ya ce tarin takardun sirri na Isra’ila da kasar ta samu na da alaka da makaman nukiliyar gwamnatin kuma za su kara karfi ga tsarin garkuwa daga hare-haren sama na Iran. “Takardun da muka samu na da alaka da bayanai game da cibiyoyin nukiliyar su,” kamar yadda Khatib ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na IRIB. Kafafen yada labaran Isra’ila sun tabbatar da hakan, tare da bayyana shi a matsayin “babban...
    Kamfanin sojojin haya na Rasha, Wagner, ya sanar da janyewarsa daga kasar Mali, abin da ya kawo kƙarshen fiye da shekaru uku na ayyukansa a wannan kasa ta Yammacin Afirka. “Mun taimaka wa ‘yan kishin kasa wajen gina wata rundunar sojoji mai karfi da tsari, wacce za ta iya kare kasarsu. Dukkan manyan biranen yankin sun koma karkashin ikon mahukuntan da ke da ikon tafiyar da harkoki a kasar,” in ji Wagner. Kasar Mali, da ke yankin Sahel, ta sha fama da hare-haren ‘yan tawaye tun daga shekarar 2012, kuma sojojin dake mulki a kasar sun nemi taimakon Rasha bayan sun katse dangantaka da Faransa da sauran abokan hulda. A farkon wannan shekarar, kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, da...
    Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana shirin kasarsa na samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasaahen Pakistan da Indiya. Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a ranar Asabar. Shugaban na Iran ya ce manufar Iran ta mayar da hankali ne kan inganta samar da zaman lafiya a duniya musamman a cikin kasashen musulmi. Ya kara da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana maraba da duk wani mataki da kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Pakistan da Indiya, kuma za ta iya taka rawar shiga tsakani ga wannan manufar.” A nasa bangaren firaministan kasar Pakistan ya mika sakon gaisuwar babba salla da sakon fatan alheri ga al’ummar Iran da...
    Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadi game da tabarbarewar matsalar jin kai a zirin Gaza da Isra’ila ke ci gaba da yi wa kawanya. Kakakin hukumar James Elder ya yi gargadin cewa, yara da dama da ke kwance a asibiti masu fama da matsananciyar yunwa ba za su iya rayuwa a mako mai zuwa ba idan har Isra’ila ta ci gaba da kafar ungulu da ayyukan jin kai a yankin. A wata hira da yayi da gidan talabijin na Sky News, James Elder ya bayyana mummunan halin da ake ciki a Gaza da kuma sadaukarwar da iyaye mata suke yi don ciyar da ‘ya’yansu. Wannan lokaci shi ne mafi wahala da mata da yara...
    Wani rahoto na gungun kwararru da aka fitar a Lahadin nan, ya nuna yadda kasar Sin ke ta kokarin samar da kyakkyawan yanayin zaman lafiya, da kawance, da hadin gwiwa a yankunan tekun kudancin kasar. Rahoton na kwararrun cibiyar Xinhua, mai alaka da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, na da lakabin “Mayar da tekun kudancin Sin wuri mai cike da zaman lafiya, kawance da hadin gwiwa: matakan da Sin ke dauka”, ya ce har kullum Sin na nacewa matakan wanzar da zaman lafiya, da daidaito a yankunan tekun kudancin kasar, kuma nasarar hakan na da alaka da matakan hadin gwiwa da ake aiwatarwa tsakanin Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN. Rahoton ya kara da cewa, ta hanyar...
    Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Matawalle ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, a garinsu Maradun, yayin da dubban magoya bayansa suka kai ziyarar gaisuwar Sallah. Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000 Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da masu kishin ƙasa. Ya ce maimakon a ci gaba da takun-saka tsakanin gwamnati da ’yan adawa, zai fi kyau Gwamna Dauda ya fito fili ya rungumi jam’iyyar da ke da madafun iko domin ci gaban jihar da ƙasar gaba ɗaya....
    Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bai wa alhazan jihar su 3,200 kyautar Riyal 1,000 na Saudiyya (kimanin Naira 450,000) a matsayin barka da sallah. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da ya kai wa alhazan ziyara a Minna. Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa Ya taya su murna bisa kammala aikin Hajji lafiya, inda ya ce wannan kyauta ce domin tallafa musu kafin su dawo gida Najeriya. Gwamna Aliyu, ya yaba da yadda alhazan suka kiyaye doka da oda a ƙasa mai tsarki, inda ya ce sun wakilci Jihar Sakkwato cikin ƙwarewa da girmamawa. Ya kuma gode musu bisa ladabi da haƙuri da...
    Aƙalla mutum tara ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Kyaramma da ke Ƙaramar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Asabar, inda motoci biyu ƙirar Golf 3 suka yi taho-mu-gama, kuma mutane da dama sun jikkata. Edgar Lungu: Za a yi zaman makokin kwana 7 a Zambiya  Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah Ɗaya daga cikin motocin, mai lambar Kaduna MKA 687 AY, ana ɗauke da ita ne daga Abuja zuwa garin Gujungu, kuma direban motar mai suna Adamu Sunusi, mai shekaru 35 daga Ƙaramar Hukumar Hadeja. Rahoton ’yan sanda...
    A masana’antar Nollywood dake Kudancin Nijeriya, manyan masu kudinsu, sarakuna, hukumomi da gwamnatoci na iyakar kokarinsu wajen ganin masana’antar ta cigaba, ta hanyoyi daban daban da suka hada da kayan aiki, wajen daukar fim, fadada ilimi, tallace tallace da sauran tallafi da masana’antar ke bukata, a wasu lokutan ma akan daukesu har kasashen Turai wajen koyon aiki da kuma tallata hajarsu ga manyan dillalan fim a Duniya wanda ta wannan hanyar sai su samu manyan kudade. T Y ya cigaba da cewa idan ana maganar masana’antar Kannywood ba haka abin yake ba, domin kuwa a nan yankin sai mai shirya fim ya nemi gida ko kamfanin da zai shirya fim din sa ya rasa, hakan zai sa ya je ya...
    Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun 2007. A cikin wannan jirgin ruwan da akwai ‘yan gwgawarmaya masu rajin kare hakkin bil’adama su 12 da su ka fito daga kasashe daban-daban, yana kuma dauke da kayan agaji na abinci da magani.  Jirgin ruwan ya samo sunansa ne daga wata Bafalasdiniya mai suna; Madeleine Kulaib, wacce ita ce macen farko ta Falasdinu da ta kware a sana’ar kama kifi bayan da mahaifinta ya yi shahada a yayin  yakin da HKI ta shelanta akan Gaza a 2023. Jirgin ruwan na “Madline” ya taso ne daga kasar Italiya, wata daya bayan da jirgin sama maras...
    Idan ana shan ruwan ganyen mangwaro, yana taimakawa wajen rage gudawa da kumburin ciki. 4. Yana Taimakawa ciwon sanyi da tari Yana da sinadaran da ke taimakawa wajen warkar da tari da mura, wanda ke iya zama matsala ga wasu mata masu ciki. 5. Yana inganta lafiyar zuciya Yana rage hawan jini, wanda ke iya zama hadari ga masu ciki, musamman masu ciwon hawan jini (preeclampsia).   Yadda ake amfani da ganyen mangwaro: A tafasa ganyen a ruwa na tsawon minti 10-15, a bar shi ya huce, sannan a sha a hankali. Za a iya hada shi da zuma ko lemon tsami don kara dandano.   Lura: Kar a sha fiye da kima, musamman idan ba a saba ba, domin...
    Jami’in gabatar da kara, Anil Kumar, ya tabbatar da hukuncin kotun, kamar yadda jaridar The Times of India ta ruwaito a ranar Litinin. Rahoton ya bayyana cewa, “A ranar 30 ga Mayu, 2020, ta shigar da karar, tana mai cewa ta samu sako a ranar 12 ga Mayu, 2020, daga wata lambar kasa da kasa da ke ikirarin ta fito daga Landan.” A cewar rahoton, “Mai aikawa ya gabatar da kansa a matsayin ‘Deepak Lee’ kuma ya ba da ID na imel.” “Ba da jimawa ba, wanda ake zargin ya kira ta ya ce ya same ta ne ta wani shafin aurenta, inda suka fara hira ta WhatsApp, sai ya shaida mata cewa ya aika da shaidarta.” Rahoton ya ci...
    Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
    PPRO ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana auren mahaifiyar wanda aka cutar (da sakaya sunanta). “An bayyana cewa ya yi lalata da yarinyar a lokacin da mahaifiyarta ke barci, yana shiga dakinta kuma yana aikata abubuwan da ba su dace ba a lokuta da dama. “Wakil ya ce, “Yarinyar na shan wahala amma duk da haka ta kame bakinta sai da lamarin ya ta’azzara sannan ta fada wa makwabta, wanda hakan ya kai ga daukar matakin kama wanda ake zargi da aikata laifin,” Ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi an ruwaito wanda ake zargin ya amsa laifinsa. “An kwashe wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da...
    Ƙasar Zambiya ta ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai don girmama tsohon shugaban ƙasar, Edgar Lungu, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni, 2025, a ƙasar Afirka ta Kudu. Ya rasu yana da shekaru 68. Gobara ta tashi a otal ɗin da ke ɗauke da Alhazan Najeriya 480 a Makkah 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce Lungu ya shugabanci Zambiya daga watan Janairun shekarar 2015 har zuwa watan Agustan 2021, lokacin da ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci yanzu, Hakainde Hichilema. Gwamnati ta sanar da cewa daga ranar 8 zuwa 14 ga wata Yuni, duk tutocin ƙasar za su kasance a ƙasa, sannan kuma an dakatar da duk wasu...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...
    Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta amince da samun tauyaya a yawan adadin sojojin mamayar Isra’ila sakamakon halakar wasu daga cikinsu Rundunar sojojin Isra’ila ta yarda cewa: Suna fama da matsanancin karancin sojoji masu yawa, a halin yanzu akwai yawan 10,000, da aka rasa kuma ana neman fiye da rabinsu a fagen gudanar da yaki, a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a zirin Gaza. Rundunar sojin ta ce suna fuskantar karancin sojoji fiye da 10,000, ciki har da kusan 6,000 na rukunonin yaki,” wannan rashin sojojin rashi ne maim ai tsanani da ake bukatar samunsu cikin gaggawa, don haka rundunar soji take gudanar da duk matkn da suka dace don toshe wannan gurbin, in ji kakakin rundunar sojin mamayar...
    Ran 4 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan sanarwar hana baiwa daliban ketare dake neman gurbin karatu a jami’ar Harvard bizar shiga kasar da dakatar da shigar daliban ketare dake karatu a jami’ar da ‘yan ketare masu shirin mu’ammalar ilmi a cikin kasar. Sanawar ta ce, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bisa la’akari da batun tsaron kasar. Gwamnatin Amurkta ta matsa lamba kan jami’o’in kasar ciki hadda Harvard ta hanyar katse ayyukansu dake da nasaba da kasashen ketare da hana baiwa dalibai Sinawa bizar shiga kasar ba gaira ba dalili, matakin da ya bullo da ainihin burinta na amfani da sunan wadannan jami’o’i don cimma nasarar matakanta na siyasa. Ba...
    Gobara ta tashi a otal ɗin Imaratus Sanan da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya, inda sama da alhazan Najeriya 48 suka sauka yayin aikin Hajjin shekarar 2025. Otal ɗin yana unguwar Sharamansur a birnin Makkah. Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa dukkanin alhazan sun tsira kuma babu wanda ya ji rauni. A cewar NAHCON, hukumomin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin sun gaggauta kashe wutar kafin ta bazu. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ziyarci otal ɗin tare da wasu jami’an hukumar domin duba halin da ake ciki. Ya bayar da umarnin a kwashe alhazan zuwa wani sabon otal cikin gaggawa,...
    A ‘yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da masu masana’antu da ‘yan kasuwa na kasa da kasa, inda ya karfafa musu gwiwar kara gudanar da harkokinsu da zuba jari a kasar Sin. Roland Busch, shugaban kwamitin darektoci na kamfanin Siemens yana daya daga cikin baki mahalarta ganawar. A yayin da yake zantawa da wakiliyar CMG, ya bayyana cewa, shugaba Xi da kansa ya halarci ganawar, wanda ya isar da sakon cewa, kasar Sin za ta kara bude kasuwarta, da maraba da kamfanonin kasashen waje da su gudanar da kasuwanci da zuba jari a kasar, lamarin da ya burge kowa da kowa kwarai da gaske.   Roland Busch ya jaddada cewa, kamfaninsa bai taba yin...
    ’Yan Sanda sun kama wani mutum mai suna Mohammed Sani mai shekara 31 da duniya, bisa zargin dukan matarsa Hauwa mai ɗauke da juna biyu, wanda ya zama ajalinta. Lamarin ya faru ne a gidansu da ke unguwar Banin Hashim da ke Minna, a Jihar Neja. Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 13 a wajen rabon tallafi a Gaza 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce Hauwa mai shekara 24 a duniya wadda ke ɗauke da cikin wata tara, an same ta a mace a ɗakinsu kwance cikin jini. Rundunar ’yan sandan ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar 3 ga watan Yuni, 2025. Jami’an ‘yan sanda daga sashen A Division a Minna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      CGTN ta wallafa nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. Kuma mutane 5610 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani Lauya Okere Kingdom Nnamdi, wanda ya gabatar da takardu don samun rajistar Jam’iyyar Mutanen Kasa (PPP) a ranar 28 ga Maris, 2025, ya ce bayan wata daya sai INEC ta bayyana cewa ba ta bude adireshin fara yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa. Jami’an INEC da suka yi magana kan lamarin, sun musanta zarge-zargen. Sun bayyana cewa duk da cewa an karbi bukatar yin rajista har guda 104, ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan kuma tsarin zai fara gudana nan ba da dadewa ba ta hanyar sadarwaar zamani don inganta gaskiya da ingancin aiki. “Hukumar ta amsa wa masu nema. Ba daidai ba ne a zargi INEC da jinkirin amsa bukatun yin sabbin rajistar. Za a bude Shafin...
    Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev. Sojojin na Rasha sun yi amfani da kamamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake da su ka haddasa tashin gobara. Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kharikiev ya bayyana cewa; A kalla mutane 10 su ka jikkata a bisa kididdigar farko.  Ita kuwa rundunar sojan saman kasar ta Ukiraniya ta sanar da cewa; an yi amfani da makamai masu linzami samfurin “Cruise” wajen kai harin. Su ma sojojin na Rasha sun sanar da cewa, sun kai wa Ukiraniya hare-hare akan sansanonin soja da kuma muhimman cibiyoyin kasar ta hanyar...
    A rana ta biyu tabukuwan  babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza. A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu. An sami shahidai 5  da kuma wasu mutane  biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza. A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu. A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama. A kusa da cibiyar kiwon...
    Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bayyana cewa; Matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumin  shiga Amurka akan wasu ‘yan kasa da kuma wasu kasashen musulmi yana nuni da yadda Amurkan take adawa da musulmi. Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce; Daukin matakin hana wasu mutane yin tafiya saboda  kasar da su ka fito, ko addininsu yana nuni ne da yadda Amekin take jin fifiko da kuma nuna wariya. A karshe ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira ga MDD da sauran cibiyoyin kasa da kasa na shari’a da su dauki mataki karara kuma a fili akan abinda Amurka ta yi, da ya sabawa duk wani ma’auni na ‘yan adamtaka. A ranar...
    Za su fara wasansu na farko da kungiyar Wydad Casablanca ta Morocco a Philadelphia ranar 18 ga watan Yuni, za a bude kasuwar musayar ‘yan wasa har zuwa ranar 10 ga watan Yuni domin karbar kungiyoyin da ke son sayen ‘yan wasa a gasar cin kofin duniya kafin a sake budewa a ranar 16 ga watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A shekarar da ta gabata, kamfanin Dangote ya biya haraji N450 biliyan – wanda ya fi dukkan bankunan Nijeriya suka hada jarin harajin da suka biya. Wannan shiri na gina hanyoyi yana cikin shirye-shiryen gwamnati na ba da rangwamen haraji domin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wasu lokuta, matsalolin suna fitowa kai tsaye sakamakon rashin fahimta daga mataki na kasa, wadada a wasu lokutan ba su da wata alaka da sakatariyar jam’iyyun da ke mataki na sama. Ko a cikin jam’iyyar APC da ke mulki, akwai jayayya a cikin rassan jihohinta da ba su warware ba kuma suna barazanar ga damar jam’iyyar a jihohin da abin ya shafa. Wasu masana harkokin siyasa sun bayyana cewa rarrabuwar kawunan ta samu ne sakamakon nuna iko tsakanin wasu mutane a wasu jihohi. Akwai batun wanda ke da iko da tsarin jam’iyyar shi ne shugaban jam’iyyar a jihar. Yayin da wasu ke cewa wannan shi ne tushen da ya haifar da rarrabuwar kawuna da ke faruwa a cikin tsarin...
    Wasu sahihin rahotannin daga cikin gwamnatin sun shaida cewa Gwamna Eno ba zai iya sauya sheka zuwa APC ba tare da amincewar Emmanuel ba, domin yin hakan na iya jawo masa asarar goyon bayan mambobin majalisun kasa da na jihar, ciki har da sauran muhimman masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. An kuma tattaro cewa wani bangare na shirin fadar shugaban kasa shi ne, dukkan jihohin Kudu Maso Gabas su kasance na APC. Gwamnonin kamar Hope Uzodimma su ne kan gaban wajen yin matsinlamba ga Gwamnan Peter Mbah na Jihar Inugu, Aled Oti na Jihar Abiya da Chukwuma Soludo na Jihar Anambra don su sauya sheka zuwa APC. Duk da haka, rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Inugu bai bayar da...
    Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.   Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...
    Shugaban kasar Amurka ya ci gaba da fadin kalamai na zagi ga tsohon mai taimaka masa a harkokin gwamnati bayan sun babe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana cewa hamshaken  attajirin ya haukace. Labarin ya nakalto Fadar white house na karyata zancen cewa mutanen biyu zasu dinke barakan da ta faru a tsakaninsu wanda yasa shugaban ya kore shi. Wani mai Magana da yawun fadar white House yana cewa shugaban bai da wani shin a Magana da Musk a yau. Ya ce Trump ba ya kaunar sake ganinsa, duk da cewa Musk ya bayyana anniyarsa ta gyaran barakar da ta barke a tsakaninsa da maigidansa shugaba Trump. A safiyar jiya Jumma’a Trump ya fadawa radiyon...
    Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza. Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu. Kafin haka dai a jiya Jumma’a dakarun na Hamas tare da hadin guiwa da na Saraya Qudus sun aiwatar da wani shiri ko tarko kan sojojin yahudawan wanda ya sami nasara halaka sojojin yahudawa da dam. Majiyar yahudawan sun tabbatar da aukuwar hare-haren na Khan Yunus dake kudancin Gaza, wanda kuma ya halaka yahufawa da dama., Abu ubaida ya kammala da cewa aikin soje da suka yi a Khan Yunus...
    Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da mutuwar wasu da dama daga cikin sojojin su a wani tarkon da dakarun Hamas suka yi masau a garin Khan Yunus na Gaza, wasu sun ji nrauni, sannan har yanzun akwai wadanda ba’a fito dasu daga karkashin burbushin gine-gine ba. Kamfanin dillancin labatan IP na kasar Iran. Majiyar yahudawan ta kara da cewa karfin da kungiyar Hamas ta tokwarorinsu suke da shin a halaka sojojin HKI kamar haka ya Sanya shakku a kan yiyuwar samun nasara a kansu. Kamfanin dillancin labaran Hadashot Bazman na yahudawan ya tabbatar da cewa an kashe yahudawa 5 sannan wasu 12 sun ji Rauni a yayinda har yanzun ba’a san halin da wasu daga cikin sojojin suke ciki...
    A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, a duk irin kalubalen da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar za su kasance a ko yaushe masu jan hankali wajen zuba jarin waje. An ba da rahoton cewa, a yanayin tangardar da tattalin arzikin kasa da kasa ke fuskanta, huldar kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin da sauran kasashen duniya na nan daram ko gezau. A cikin watanni biyar na farkon wannan shekara, kasar Sin ta bude hanyoyin sufurin jiragen sama na dakon kaya na kasa da kasa guda 101, kuma an kara yawan zirga-zirgar jiragen sama na...
    Akalla mutane hudu ne, ciki har da wani matashi dan shekara 13, an ce an harbe su tare da fille kawunansu a ranar Alhamis a yankin Gangaran Kwata da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na tsakar daren ya haifar da tashin hankali a yankin na Mangu. Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Abdullahi Maicibi, shugaban addini a yankin Kwata, ya tabbatarwa da wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa babban masallacin Mangu da ke garin Mangu domin yin sallar jana’iza. Shagari Madaki, another resident, said...
    “Gidauniyarmu ta farko da aka kafa a shekarar 1952, ta tallafa wa masu fasaha daban-daban na Afirka, ta hanyar ba su damar shiga kasuwannin duniya. Gidauniyar Egbuagu, wadda aka kaddamar a yau; za ta mayar da hankali ne wajen kula da ayyukan shari’a, domin taimaka wa ‘yan Nijeriyan da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba,” in ji shi. “Babban bangaren da za mu bai wa fifiko shi ne, na matasan fursunoni, masu basirar kirkire-kirkire. Muna so mu taimaka musu su yi amfani da kwarewarsu, domin samun damar rike kawunansu ko da kuwa a gidajen yarin ne. Kazalika, bincikenmu zai mayar da hankali kan shekaru da kuma yanayin daurin da aka yi musu.” Dangane da batun hadin gwiwa kuwa,...
    Idan za a tuna dai kamfanonin samar da wutar lantarki a kwanakin baya sun gargadi gwamnatin tarayya kan ci gaba da rike musu basuka wanda yanzu ke neman kai wa naira tiriliyan 4. A kwanakin baya ne kwamitin majalisar datawa mai kula da wutar lantarki ya nuna damuwarsa kan matsalar karancin wutar lantarki da ta dabaibaye bangaren wutar lantarki, inda ya koka da yadda karancin kudin wutar lantarki a masana’antar, ya nuna cewa gwamnati na rike da kudaden kamfanonin da ke samar da wutar lantarki kusan naira biliyan 200 a duk wata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya. Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce...
    A zangon farkon 2025, jihohi bakwai din dukkaninsu na neman naira biliyan 46.80 daga asusun gwamnatin tarayya domin cike gibin kudin shiga da biyan basukan da suke yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) da ke samun goyon bayan sojojin sama Air Component sun kashe wasu manyan kwamandojin Kungiyar ISWAP guda uku. Rundunar ta kashe kwamandojin ne a harin ta’addanci da ba a yi nasara ba a kan Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam a Jihar Borno. Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Wata majiya mai tushe daga jami’an rundunar ta OPHK ta tabbatar a ranar Alhamis din nan cewa, kwamandojin da aka bayyana sunayensu: Amir Abu Ali Weldone da Amir Ibunu da Amir Abu Waldume, na daga cikin wadanda aka kashe a harin da aka kwashe sa’o’i hudu ana yi a sansanin ‘yan...
    Kwamishinan Harkoki na Musamman a Jihar Akwa Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa biyo bayan sauya sheƙar Gwamna Umo Eno daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Sallah: Gwamna Inuwa ya yi kiran sadaukarwa da haɗin kai Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Gwamna Eno ya faɗa wa kwamishinoninsa cewa duk wanda ba ya son bin sa zuwa APC ya ajiye aikinsa. Ememobong, ya ce yana girmama ra’ayin gwamnan, amma ba zai iya binsa APC ba. “Ba zan iya yin wannan tafiya ba,” in ji Ememobong. “Na yarda da siyasar aƙida. Na gode wa gwamna bisa ƙauna da...
    Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar sace-sacen jama’a sun biya matsakaitan kudin fansa na naira miliyan 2.67, wanda ya kai naira tiriliyan 2.23. An fitar da rahoton ne kwana guda bayan rahoton hukumar kare kakkin Dan’adam na Nijeriya na shekarar 2024, ya nuna cewa akalla mutane 526 ne aka kashe a wasu munanan hare-hare tare da yin garkuwa da wasu 949 a wasu sassan kasar. Duk da masana sun sha nusar...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna. A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya da haɗin kan Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya. Ya jaddada muhimmancin nuna soyayya, tausayi da zama mai ƙyau da maƙwabta a rayuwar yau da kullum. “Yayin da muke murnar Babbar Sallah, mu yi tunani kan abin da take nufi biyayya, sadaukarwa da ƙwarin gwiwa,” in ji Gwamna Yahaya, yana mai ƙarfafawa al’umma da su ci gaba da...
    Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. Ya bayyana hakan ne a hukumance a ranar Juma’a a gidan gwamnatin jihar da ke Uyo, babban birnin jihar. Tinubu ba zai canza Kashim a matsayin mataimakinsa ba a 2027 – APC Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda Wannan mataki ya biyo bayan wasu kwanaki da ya shafe yana nuna sha’awarsa na sauya sheƙa. A wani taron jama’a da aka gudanar a Ikot Abasi, ya ce: “Lokaci ya yi da za mu motsa” domin a haɗa kai da Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta. Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan...
    Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai. Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO. “Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar.   “Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah.   “Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da muke da ita ga al’umma da bil’adama, ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani a kan kimar sadaukarwa da biyayya ga Allah Maɗaukakin Sarki.   “Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma laifuka da suka shafi al’ummarmu.   “Haƙƙinmu ne na gamayya mu yi aiki don tabbatar da tsaron al’ummarmu,...
    Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da kuma sauran kasashen duniya suka gudanar da sallar Layyah, wanda yake daga cikin manya-manya bukukuwa a cikin addinin musulunci. Tashar talabijin na Press tv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan sallar wanda maniyya da kuma sauran musulni suke yi ya hada da yanka dabba gwagwadon hali, da kuma raba namansa a tsakanin mabukata musulmi. Don tunawa da annabi Ibrahim a lokacinda ya yi kokarin yanka dansa annabi Isma’ila duk da cewa shi kadai ne yake da shi. Kuma yana sonsa, da yayi haka sai All..T ya fance shi da rago, don haka a mai makon dansa ya yanka rago, Ana son duk musulmi baligi wanda ya ke da lafiya da ikon zuwa...
    Kotun kasa da kasa ta ICC ta yi tir da gwamnatin kasar Amurka wacce ta kakabawa al-kalan kotun guda hudu saboda hannu da suke da shi wajen fidda sammacin kama fray ministan HKI Benyamin Natanyahu. Kotun ta kara da cewa tana goyon bayan alkalanta kuma zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya duk tare da abinda suke faskanta. Kotun ta bayyana cewa tana aikinta ne bisa goyon bayan kasashen duniya 125 wadanda suka fito daga dukkan kusruwowin duniya. Takunkuman dai ya shafi wadannan alkalai su 4 kuma mata. Kuma sun hana ko wanne daga cikinsu, shiga kasar Amurka kuma idan suna da kadarori ko kudade gwamnatin Amurka ta kwace su. A cikin watan Nuwamban shekara ta...
    Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa. Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare da wannan fasahar ta kula da zafin dukkan wuraren da mahajjata zuwa zuwa da kuma hana cinkoson mutane a kewayen Kaaba da sauran wurare.. Jami’I mai kula da bangaren kirkirerren fasaha wato AI na aikin Ajjin bana ya shaidawa Jaridar ArabNews kan cewa sun kirkiro abubuwa da dama don sawwaka aikin hajji ga mahajjata da kuma khidimomin da kasar saudiyya take yiwa mahajjata, Ya ce...
    Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais ya rasu yana da shekaru 89 a duniya. Mmarigayin, wanda ya kasance Alkalin Alkalan na tsawon shekaru 11 daga 1995 zuwa 2006 ya rasu ne a Abuja ranar Juma’a. Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Wata majiya daga iyalan mamacin ta tabbatar da rasuwar sannan ta ce shirye-shirye sun kankama na yi wa mamacin jana’iza. An dai haifi marigayin ne a ranar 12 ga watan Yunin 1936 a Zariyan jihar Kaduna. A zamanin da yake shugabancin Alkalan, ya kawo sauye-sauyen shari’a da dama musamman a bangaren fadada harkokin siyasa, inda hakan ya zama silar...
    “Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan. A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce an samu yawan mace-macen ne saboda rashin bin umarnin gargadin ambaliyar ruwa daga mutane a jihar. Ya bukaci jihohi su dauki matakai don hana mummunar ambaliyar ruwa da ka iya lalata rayuka da kadarori, ministan ya ce, “Ma’aikatar Tarayya ta Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli tana mika ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar Jihar Neja, musamman ga al’ummomin da lamarin ya shafa a Mokwa, wadanda suka fuskanci asara, mutuwa da canjin wuri sakamakon wannan bala’i na ambaliyar ruwa. “Ina jaddada cewa ambaliyan da aka samu ba ta kasance saboda sakin ruwa daga dam din Kainji ko Jebba ba ne, domin duka dam din suna cikin tsaro. “Mun yaba da kokarin gaggawa na gwamnatin Jihar Neja da hukumomin yankin, da...
    Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-hare a kan birnin Kiev da kuma wasu gundumomi 9 na kasar. Rundunar sojan saman kasar Ukiraniya ta ce; Kasar tasu ta fuskanci munanan hare-hare da makamai masu linzami a cikin gundumomin gabashi, yammaci da kuma babban birnin kasar Kiev. Rundunar soja da take tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kiev ta sanar da cewa; Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren da akwai tashar jirgin kasa, hakan nan kuma muhimman cibiyoyi da gidajen fararen hula. Magajin birnin Vitali Klitschko ya sanar da cewa; Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu mutane 20 su ka jikkata sanadiyyar harin na Rasha. Haka nan kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotannin daga kasar Lebanon sun ce jiragen HKI sun kai hare-hare sau 17 a cikin unguwar Dhahiya a birnin Beirut. Kafafen watsa labarun HKI sun ce; harin shi ne mafi girma da HKI ta kai a Lebanon tun bayan tsayar da yaki, kuma tuni sojojin na HKI sun kafa na’urorin kakkabo makamai a arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya saboda harin da za a iya kai ma ta daga Lebanon. Kananan jiragen yaki marasa matuki masu yawa sun rika yin shawagi kasa-kasa a saman birnin Beirut, tare da yin kira ga mazauna yankin da su fice daga gidajensu. HKI ta riya cewa, wurin da ta kai wa harin, masana’anta ce ta kera jiragen sama marasa matuki, lamarin da majiyar Lebanon ta...
    Kafafen watsa labarun kasar ta Zambia da kuma jam’iyyarsa ta “PFT” sun sanar da cewa; Tsohon shugaban kasar ya fadi ne a lokacin da yake motsa jiki a gidansa dake birnin Lusaka. Bayan da aka kai shi asibitin soja na “Maina Soko” likitoci sun tabbatar da cewa ya rasu. Gwamnatin kasar ta Zambia ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, tare kuma da shelanta ranakun alhini na kasa. Shi dai Lunga ya jagorancin kasar ta Zambia ne daga 2015 zuwa 2021 da ake yabonsa da gina muhimman cibiyoyi a kasar, sai dai kuma hakan ya bar kasar da dimbin bashi. Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin da za a yi jana’izar tsohon shugaban kasar ba.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin.   Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu. Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu. NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah...
    Abdullahi ya ce, an dauko wanda ya fadan a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.   Ya kara da cewa, an mika gawar marigayin ga Hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau ce ranar muhalli ta duniya. An yi sharhi a baya cewa, a cikin ’yan shekarun nan, kasar Sin ta jagoranci ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a duniya, da samun gagaruman nasarori a fannin raya makamashin da ake sabuntawa da sauran fannoni, da taimaka wa sauran kasashe masu tasowa wajen aiwatar da ayyukan sauyin makamashi. Yayin da yake amsa tambayoyi a wurin taron manema labaru da ya gudana a yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance mai fafutukar neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a ko da yaushe, kana mai taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ta wannan fuskar...
    A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025.   Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin.   Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take.   LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga...
    “Al’ummar kasa da kasa da yawa sun sauya ra’ayinsu mai kyau game da Amurka zuwa mummunan ra’ayi, yayin da yawan masu nuna kauna ga kasar Sin ya karu.” Wani bincike da kamfanin bincike na Morning Consult na Amurka ya fitar kwanan nan ya nuna cewa, har zuwa karshen watan Mayu, yawan al’ummar duniya dake nuna kauna ga Amurka ya ragu zuwa -1.5, yayin da adadin ya karu zuwa 8.8 ga kasar Sin. Ko da yake sakamakon ya fito ne daga hukumar bincike guda daya kawai, amma yana da ma’ana sosai wajen yin kashedi, idan aka yi la’akari da cewa binciken ya shafi kasashe da yankuna fiye da arba’in, inda akasarinsu su ne muhimman abokan huldar Amurka a fannin tattalin arziki...
    A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno. Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai. Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a Saudiyya Rahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam. An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na...