2025-07-31@16:12:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 108
«dimokuradiyya a Nijeriya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain. A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya. A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka ƙara. Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya kuma yi kira ga dukkan maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta yin hakan. Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin bayan ranar 10 ga Fabrairu ba, don haka ya bukaci maniyyata su yi amfani da wannan damar su kammala rijistarsu kafin ko zuwa Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025. Rel/Adamu...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...