Jami’an Diblomasiyya Daga Kungiyar G20 Da Dama Sun Isa Afrika Ta Kudu
Published: 21st, February 2025 GMT
Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ yace ana saran kasashen turai zasu kara jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da kasar Rasha. Duk tare da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son kawo karshen yakin ba tare da su ba.
Kasashen Burtaniya , Faransa, Jamus da kuma tarayyar Turai EU gaba daya suna goyon bayan Ukraine a yakinta da Rasha.
Har’ila yau sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio bai bayyana a taron ba. Sai dai ana zaton jakadan kasar Amurka a kasar Afirka ta kudu Dana Brown ne zata wakilci kasar a taron.
Amurka ta ki halattar taron G20 A Afrika ta Kudu ne saboda matsayinta dangane da yaki a Gaza da kuma wasu dokokin mallaka a kasarsa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha.
Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya.
Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta.
Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna.
Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar Rasha Olog Silgy ya tabbatar da cewa,kasarsa a shirye take ta bunkasa aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran a fagen musayar dalibai da kuma nazarce-nazarce da bincike na ilimin likitanci.
Kasashen biyu sun kafa kwamitin hadin gwiwa na yin fada da cutuka masu yaduwa da zai taka rawa mai girma wajen magance cutuka.