2025-09-18@08:34:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 109
«gyaran zuciya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya. Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu. NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa Daraktan cibiyar Salama Centre da ke Asibitin Gambo Sawaba ƙofar Gayan Zariya, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa Wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne hukumar ‘yan sanda da ke Kasuwar Mata a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025. Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin. Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...