2025-05-03@06:14:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2816
«Sakamako Mai Kyau»:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kan Zaman Tattaunawan Amurka Da Iran
Ministan harkokin wajen Iran ya sanar da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ci gaba da ake samu a shawarwari makamashin nukiliyar Iran tsakanin Amurka da Iran amma ana buƙatar gaskiya da hangen nesa daga ɗayan ɓangaren A yammacin jiya Juma’a ne ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho...
Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar Majiyoyin cikin gida na kasar Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Siriya bayan da suka yi shawagi a kan garuruwan Hama,...

Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka...
Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa...
Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar. Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwana biyu, inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta yi. Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, da tsohon Gwamna jihar Bello Masari na cikin manyan mutanen da suka tarɓe shi tun daga filin jirgin Umaru Musa. Tinubu zai yi shekara takwas...
Ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta shaida wa masu sukar Shugaba Bola Tinubu cewa zai yi wa’adi biyu ne a kan karagar mulki. Kungiyar ta kuma ce rashin adalci ne a hana Tinubu ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027, ganin cewa jigo a Arewa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a baya ya yi cikakken...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa...
Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam kazim Sadiki ya bayyana cewa kasar tana da kwararru wadanda suke da kwarewa a sanin fasahar nukliya da kuma hanyoyin dublomasiyya a tattaunawar da Iran take da Amurka dangane da shirin Nukliyar kasar. Tashar talabijin ta Al-alam a nan Tehran ta nakalto limamin yana...
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya sun kama wani jami’in sojan kasar Burtania mai suna Manjor Micah Polo tare da zarginsa da shigo da makamai kasar sannan da kokarin fasa korinsu zuwa wajen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, an lama manjo polo ne da makamai wadanda suka hada da MK-47...
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo. Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna. Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan...
“Siyasar da na sani ba ita ce abin da ke faruwa a yau ba. Siyasar da na sani ita ce gwagwarmayar muradun jama’a don tabbatar da cewa suna da kyakkyawar rayuwa a duk fannoni kamar ilimi, ruwa, kiwon lafiya, da sauransu. “Na kasance a siyasa tsawon shekaru 48 da suka gabata,” in ji shi. Ya...
Kalli ya da Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajao Saka Adewale, ya yi hole ababen hawa da sauran kayan laifi da rundunarsa ta kama a gaban ’yan jarida a ranar Juma’a. Hotuna: Abubakar Sadiq Isah.
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ƙwato motocin sata guda 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi. Kwamishinan ’Yan sanda CP Ajoa Saka Adewale, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar...

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana. A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau...

Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
Ministan harkokin jin kai da rage radadin talauci na UNOCHA, Farfesa Nentawe Goshwe, ya sanar da yunkurin hukumar na ficewa daga Nijeriya. Ya shaida hakan ne a yayin taron kara wa juna sani kan tsarin da za a dauka a Nijeriya, wanda aka gudanar a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, ofishin mai ba shugaban...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu. Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin...
Hukumar ta FIRS ta yi gargadin cewa duk bankunan da ke shiga cikin tsarin tattarawa, kudaden da ake aikawa da su, da kuma tsarin sasantawa dole ne su bi wannan umarnin ba tare da bata lokaci ba, su daina amfani da asusun da ba su izini, sannan su tabbatar da cewa ana sarrafa hada-hadar kudaden...
Wata ƙungiyar matasa mai suna “North-East Coalition Against Terrorism” ta yi maraba da Major General Abdulsalam Abubakar, sabon kwamandan yakin Operation HADIN KAI (OPHK), inda ta bayyana cewa tana fatan zaman lafiya ya dawo yankin. A cikin wata sanarwa da Ismail Mustapha da Sakatare Danlami Bukar suka rattaba hannu, ƙungiyar ta ce Sojojin Nijeriya a...
Haka zalika, mutuwar mutane 33 da jikkata 54 sun faru ne sakamakon munanan ayyuka na ganganci da rashin yanayi mai kyau, yayin da yin aiki ba bisa ka’ida ba ya kai ga mutuwar 23 da jikkata shida. Masu barnatawa da lalata kayan wuta sun janyo mutuwar mutane 18 da jikkata wasu 7, sai kuma hatsarin...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar...
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, Babban Sufuritendan dansanda, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cewa, cikin gaggawa aka yi tura jami’an ‘yansanda wanda hakan ya kai ga kamo Amusu. Wakil ya ce an kai yarinyar zuwa babban asibitin Bayara domin likita ya dubata kuma wanda ake zargin ya...
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC reshen jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar Kano kan kudirin ta na daidaita bashin da ake bin ‘yan fansho da ya haura naira biliyan 16. Da yake jawabi yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano,...

Zamfara Ta Biya Sama Da Naira Biliyan 13 A Matsayin Bashin Garatuti Da Aka Gada – Mataimakin Gwamna.
Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala biyan sama da naira biliyan 13 na garatuti, wanda ke nuna wani gagarumin mataki na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya bayyana hakan a yayin bikin ranar ma’aikata na shekarar 2025 da aka gudanar a Gusau, babban...
Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Comr. Muhammad Haruna Ibrahim ya bukaci gwamnatin jihar Taraba da ta gaggauta biyan ‘yan kungiyar SSANU, jami’ar Jalingo ta jihar Taraba alawus-alawus da suke bi bashi. Comr. Haruna ya yi wannan bukata ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron majalisar zartarwa na shiyyar karo na...
“Murkushe ‘yan adawa tare da musguna musu, musamman jam’iyyar PDP, wata alama ce karara da ke nuna cewa; zangon karshen mulki na karatowa; domin kuwa tarihi ya sha nuna hakan”, in ji Lamido a tattaunawarsa da BBC Hausa. “Ya kamata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kasance mai adalci, domin shi ne shugaban dukkanin...

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta...
Al’ummar Arewa mazauna yankin Obalande da ke Jihar Legas sun yunƙura domin tunkarar matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya, musamman yadda suka ce ’yan ƙasa ke musu cin kashi. Sun ce sun gaji da irin tsangwama da ƙasƙanci da ’yan ƙasa a yankin ke nuna wa ’yan Arewa, musamman Hausawa mazauna. Sun bayar...
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da...

Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yaba wa takwarorinsa na gwamnonin Jihohin Borno, Bauchi, Adamawa, Gombe da Taraba a bisa ga samun damar da suka yi na halartar taron ƙungiyarsu ta Arewa maso Gabas (NEGF) karo na 11 a garin Damaturu. Ya yi wannan yabo ne a ranar Alhamis a ɗakin taro na gidan gwamnati...
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi...
Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu,...
Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana kiran a samar da hanyar kawar da makaman nukiliya wacce a karkashinta ba za a iya raba tsaro na kashin kai da tsaro na bai daya ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Babban darektan sashen kula da makamai na ma’aikatar harkokin...
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho. A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da...
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta nuna matukar kaduwa game da halin da ake ciki a Gaza. Abin da ke faruwa a Gaza “ba abinda za’a lamunta da shi ne ba,” in ji Mike Ryan, mataimakin darekta-janar na Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin wani taron manema labarai. Mista Ryan, ya nuna fushinsa matuka game da...
Jiragen yakin Amurka sun sake kai hare-hare da dama kan lardunan Saada da Hudaidah na kasar Yemen yau Alhamis. Wata majiyar tsaro a Yemen ta kara da cewa, an kai wasu hare-hare uku a yankin Kataf da ke lardin Saada, yayin da wani kuma ya afkawa gundumar al-Houk da ke lardin Hudaidah a gabar tekun...
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda tabarbarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, inda ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.” “Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin...
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu fashewar wani abu a wurin ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri wanda ya faru sakamakon tsananin zafi da aka samu a yankin. A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin daraktan...
Ƴan ta’addan Boko Haram sun kashe masunta 18, a wani harin da suka kai a yankin Mobbar, wanda ke arewacin Jihar Borno, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar. Harin ya faru ne a kogin Fadana-Garuwa a yankin Duji, lokacin da mayakan suka kai hari cikin ruwan, inda suka zargi masu kamun kifin da haɗin kai da...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma...
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 51.5 wanda ba a taba ganin irinsa ba, domin muhimman ababen more rayuwa da ayyukan yi wa al’umma hidima a fadin jihar, a wani bangare na tsare-tsare na gwamnatin na bunkasa zamantakewa da tattalin arziki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai...
Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa...