Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3
Published: 31st, August 2025 GMT
Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar.
Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar.
Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasuShugaban hukumar, Dokta Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a cibiyar hukumar da ke kan titin Aba Fatakwal, da yammacin ranar Lahadi.
Ƙarin bayani na tafe…
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ƙananan Hukumomi Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.
Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.
Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.
“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.
Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.
Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.
“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.