2025-12-14@04:14:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 321
«ya yi sanadiyyar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an lalata dukiyar N11bn yayin zanga-zangar yunwa a Kano — Rahoto Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno Hakan ya sa Gwamnatin Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta ɗauki wani matakin da take ganin zai kawo lafawar lamarin. Sai dai kuma matakin da gwamnatin ta ɗauka bai yi wa jam’iyyar APC daɗi ba, inda ta nuna rashin gamsuwa tare da zargin ba a...
Mujallar “Qiushi” Ta Gabatar Da Muhimmin Sharhin Xi Jinping Game Da Inganta Tsarin Daukar Kwararan Matakai Wajen Kula Da Harkokin Jam’iyya
Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”. A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar. Saboda haka, dole ne dukkan mambobin jam’iyyar a ko da yaushe su sa lura da nuna karfin zuci, da daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar na dukkan fannoni, ta yadda za a iya raya jam’iyyar yadda ake bukata. Ban da haka, ya kamata...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari. Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan Siyasa Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru. Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk...
Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta fara kaɗawa a tsakanin jam’iyyun siyasa a Arewa maso Yammacin ƙasar na da alaƙa na son zuciyar ’yan siyasar yankin. Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a taron ƙusoshin jam’iyyar PDP da ya gudana yau Asabar a Jihar Kaduna. Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu Tambuwal ya zargi ’yan siyasar da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da son zuciya waɗanda ya ce ba sa kishin al’umma. Tsohon gwamnan ya ce akwai dalilai da ’yan siyasa ke sauya sheƙa daga wannan jam’iyyar zuwa...
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa. N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum Ya bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta. Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice. Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice....
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin. An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin. Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya. Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama,...
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take. Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya...
Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar. Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar Burtania a jam’iyyar Larbor Afzal Khan yace, wannan shawarar ta Natanyahu tabbaci ne na laifin fitta mutane daga kasarsu da karfi, don kawai ya na son a kwace zirin gaza daga Falasdinawa. Falasdinawa basa bukatan karin kasa suna son yenci ne a kasarsu. Inji dan majalisar dokoki Kim Johnson na jam’iyyar Lebour.. Kafin haka dai sarki Saman bin Abbdul azizi na kasar Saudiya yace ba...
A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari. Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba. Na baya-bayan nan shi ne samar da wata sabon jam’iyyar siyasa mai suna ‘The Alternatibe’, domin tabbatar da madafun iko a babban zabe na 2027. Wani tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa, Segun Sowunmi, wanda ke tallata wannan sabuwar jam’iyyar, ya ce an kafa jam’iyyar ne saboda ‘yan Nijeriya sun...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa. Domin sauke shirin, latsa nan
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin. Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati. Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon...