2025-12-12@23:33:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8335

«harkokin wajen Amurka»:

    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da naira biliyan 2 da miliyan 651 domin ayyukan Hajjin 2026, biyo bayan gabatar da bukatar da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya yi. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce za a yi amfani da kudaden ne a bangarorin sufuri da jijigilaAlhazai, jin dadinsu, ayyukan lafiya da kuma shirye-shiryen gudanarwa. Sauran bangarorin...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta haramta kafa Hukumar Hisbah mai zaman kanta tana, wadda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, yake ƙoƙarin kafawa. Gwamnatin ta ce kafa hukumar ya saɓa da doka, kuma zai iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar. Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago A cikin wata takarda da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a ranar 8 ga watan Disamba, 2025, gwamnatin ta ce ta gano an fara ɗaukar mutane aiki a hukumar ba tare da neman izini ba. Gwamnatin ta ce hakan ya saɓa wa Dokar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano. Da yake zantawa da ’yan jarida,...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi. Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna sun bayyana jin dadinsu kan yadda aka gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali.   Daya daga cikinsu, Malama Ummahani Danbala, ta ce an wayar da kan jama’a sosai ta hannun mata ’yan sa-kai a unguwarsu, inda aka karfafa gwiwar iyaye mata su kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna. Malam Yunusa, wani mai sa ido a karamar hukumar, ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa. Alhaji Ahmed Umar Labbo yace hukumar za ta sayi motar daukar marasa lafia wato ambulance domin dawainiya da mahajjatan da za su gamu da rashin lafiya a lokacin hajji a kasa mai tsarki. Yana mai bayyana cewar za a yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen kaiwa da komowa yayin aikin hajji. Sai kama masauki ga ma’aikatan hukumar da ma’aikatan...
    Mai horar da Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya ce zai sanya Mohammed Salah cikin jerin ’yan wasan da za su bugawa Liverpool wasa da Brighton a ranar Asabar. Slot wanda ya samu saɓani da Salah kan ajiye shi a benci a wasanni uku a jere, ya ce yana da yaƙinin cewa, Salah zai ci gaba da bugawa ƙungiyar wasa. 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya Ya kuma ƙara da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan domin ya ci gaba da taka leda a Anfield. Salah mai shekara 33, baya cikin jerin ‘yan wasan da suka doke Inter Milan a Italiya...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya jaddada game da mihummanci sanya hannun jari da kuma hadin guiwa a iyakoki, a matsayin abubuwan da ya fi mayar da hanakli akai a lokacin ganawarsa da shugaban kasar iraki Abdul latif rashid a gefen taron kasa da kasa na zaman lafiya a kasar Turkmenistan Tehran da Bagadaza sun dauki hadin guiwa a matsayin babban ginshikin zaman lafiya a yankin da kuma kariya daga tsangwama daga kasashen ketare  musamman Amurka da Isra’ila wadanda ke neman raba kan kasashen musulmi da kuma kawo cikas ga hadin guiwar tattalin arziki da siysa. Ana shi bangaren shugaban kasar Iraqi ya fadi cewa iran itace makwabciya mafi muhimmanci don muna da alakar tsaro mai...
    Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025. Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa. Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai Ya sami kyautar ne saboda rawar da ya taka a Galatasaray a kakar wasa ta bara, inda ya zura ƙwallaye 37 kuma ya taimaka wajen zura ƙwallo sau bakwai a wasanni 41, wanda hakan ya sa Galatasaray ta lashe gasar Turkiya. Osimhen ya karya tarihin Galatasaray na zama ɗan wasan da ya...
    Matatar man Dangote ta sake rage farashin man fetur ɗin da take sayar da man, inda ta rage farashin man fetur ɗin daga Naira 828 zuwa Naira 699 kan kowace lita. Bayanan farashin da aka wallafa a shafin  kasuwancin farashin man fetur a Petroleumprice.ng a ranar Juma’a sun nuna cewa matatar ta aiwatar da wani bita na baya-bayan nan, inda ta rage farashin man da N129 a kowace lita – ragin kashi 15.58 cikin 100. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina Wani jami’in matatar man da ya zanta da manema labarai bisa sharaɗin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin tsokaci a bainar jama’a, shi ma...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin Shirin na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu. Sannan daga karshe idan akwai lokaci mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///…Madallah, masu sauraro labarimmu na farko a wannan Shirin shi ne, dangane da furucin jakadan Amurka na musamman a kasar Tom Barrack wanda ya bayyana ‘shirin Amurka na 5’ dangane da siyasar Amurka a kan kasar Iran ya wargaje bayan rashin nasarar da ta fuskanta a yankin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin...
    A ci gaba da al’adar fiye da shekaru 30, Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka da dama a tsakanin 5-11 ga watan Janairun 2025 don sake tabbatar da dangantakar diflomasiyya da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Wannan ziyarar ta sake tabbatar da manufar ci gaba da cin moriyar juna a tsakanin bangarorin biyu.   Baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka na hudu a Changsha An gudanar da wannan taron baje kolin na hudu daga 12 zuwa 15 ga watan Yunin bana a Changsha, babban birnin lardin Hunan. Baje kolin ya tattaro kusan kamfanonin Sin da Afirka 4,700, kuma an baje kolin kayayyakin Afirka sama da 800 daga kasashe da dama....
    Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai. Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam. Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina Maharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki. Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta. Hakan ya yi sanadin mutuwar uku...
    Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu. A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar. ‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa An yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja. Kotun ta yi watsi...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma. NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari...
    Wani mazaunin Kano, Namadi Bawa, ya bayyana yadda ya shiga cikin daji a Jihar Zamfara domin kai kudin fansa ga ’yan bindiga da suka sace ɗan uwansa, inda ya tarar da su cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, kafin daga bisani ya samu ya kubutar da shi. A tattaunawar mutumin da Aminiya, y ace an sace ɗan uwan nasa ne a Gusau babban birnin jihar Zamfara, a kan hanyarsa ta dawowa daga Sakkwato.A cewar Namadi, ɗan uwansa ya ci karo da shingen da ya yi kama da na jami’an tsaro a hanya, sai dai daga baya aka gano ’yan bindiga ne suka yi masa kwantan bauna tare da wasu fasinjoji. “Sun kira ni suka tambaya ko na san ɗan uwana,...
    Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026” Masana a Taron Abuja na Tattaunawa kan Tattalin Arziki Kasa da ake wa lakabi da Abuja Economic Dialogue 2025 da Kamfanin Ignite Capital ke shiryawa duk shekara da haxin gwiwar Kamfanin Innovision Global Consulting sun yi hasashen cewa, za a samu saukar kayan masarufi da Karuwar samar da ayyukan yi a faxin kasa a shekara mai zuwa ta 2026. Masana tattalin arzikin da suka yi fashin baki kan yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya a cikin watanni tara da suka gabata, a taro sun haxa da Dakta Paul Arinze, Shugaban Kamfanin Bincike da Nazari kan harkokin tattalin arziki mai suna Pedestal Africa da Dakta...
    PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar. Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya. Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh Eno na Akwa Ibom da Sheriff Oborebwori na Delta da Douye Diri na Bayelsa da Peter Mbah na Jihar inugu. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya dade yana son barin PDP kuma yanzu yana jiran lokaci mai ya yi ne ya shiga APC. Akwai fargaba cewa gwamnonin Caleb Muftwang na Jihar Filato da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ma na iya canza sheka. Gwamnonin PDP kadai...
      A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000.   Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar Oko (Hausa), Midwifery Market da Ogbogonogo Market, sai dai a kasuwannin mako-mako na kauyuka. Bincike a babban birnin jihar ya nuna cewa farashin muhimman kayan abinci ya dan daidaita, amma ‘yan kasuwa da masu sayayya sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake da shi don sayayya. Kwandon tumatir da ake sayarwa Naira 5,000 a wasu watanni da suka gabata, yanzu ya sakko Naira 4,000....
    Da yake zantawa sa wakilinmu jim kadan bayan Kamala atisayen, mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Daji na kasa (NFSS) mai kula da Ayyuka, Manjo Muhammad Abubakar Abdullahi mai nurabus, ya ce hukumar na kara samun kaimi wajen amfani da sabbin dabaru da tsare-tsare don kare dazukan kasar. DCG Mohammed, ya bayyana suna gudanar da irin wannan atisayen musamman duk karshen shekara na Arewa maso yamma bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da ingantaccen tsaro a dazukan Nijeriya. Ya bayyana cewa NFSS za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin lalata maboyar ’yan bindiga da sauran miyagu da ke cikin dazukan kasar. DCG Mohammed ya bayyana cewa bayan kammala atisayen, za a tura dakaru daban-daban zuwa muhimman...
    A nan za mu iya cewa, wannan zunzurutun kudaden da za su tara har Naira biliyan 19 a wata daya, ya zama wajibi alummar yankin su sauya, na dakile matsalar domin kuwa, ‘yan Nijeriya, sun gaji batun ana tara dimbin kudade, domin magance wata matsala a kasar, amma daga, a karkatar da su, zuwa wata sabga, ta da ban. Kazalika, batun ba wai kawai na tara wadannan zunzurutun kudaden ba ne, amma babbar ahaure’yan ambayar a nan ita ce, shin wa zai tafiyar da wadanda kudaden ? kuma shin, takamai-mai, wacce daga cikin matsalar ta tsaron, za a tunkarar? ta yaya za a kashe kudaden tare da fayyace yadda aka kashe su? Matukar gwamonin, ba su bayar da wata gamsasshiyar...
    Wani abun lura ma a nan shi ne yadda a matsayinta na kasa mai tasowa ta farko a tarihin duniya da ta cimma nasarar samun wadata cikin lumana, Sin ta samar da wata taswira mai inganci, wadda sauran kasashe masu tasowa za su iya bi domin raya kansu cikin lumana, kuma karkashin hakan ne take ta fitar da shawarwari na ingiza ci gaban duniya bi da bi, irinsu shawarar raya jagorancin duniya da kasar ta gabatar a baya bayan nan. Shawarar da masharhanta da yawa ke ganin na da ma’anar gaske, wajen ingiza adalci, da daidaito a tsarin cudanyar mabanbantan sassan duniya. A gani na tun da har kasar Sin ta kai ga gina tsari mai gamsarwa na raya kai...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya zargi ‘yan siyasan Nijeriya da zagon kasa ga ci gaban kasar ta hanyar daukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a. Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas, Sanusi II ya ce manyan ‘yan siyasa a fadin Nijeriya, suna ci gaba da yin zagon kasa ga ci gaban kasa saboda suna fifita kansu, iyalansu da abokan huldarsu fiye da kasar da ‘yan kasarta. Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara Ya yi...
    Masana’antun kirar motoci na kasar Sin, sun samar tare da sayar da motocin da suka haura miliyan 31 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, wanda hakan ke shaida irin ci gaban da suka samu ta fuskar fitar da hajoji. A cewar wasu alkaluma daga kungiyar kamfanonin kirar motoci na kasar Sin, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamban bana, adadin kirar motoci a Sin ya karu da kaso 11.9 bisa dari kan mizanin shekara, zuwa sama da motoci miliyan 31.23, yayin da alkaluman sayar da su ya karu zuwa kusan miliyan 31.13, wanda ya shaida karuwar kaso 11.4 bisa dari kan mizanin shekara. Kazalika, alkaluman na watanni 11, sun shaida yadda yawan kirar motoci masu aiki da sabbin makamashi a kasar...
    Ya ce, wanda ake kara ya nema kuma an bashi kudin fansa har Naira miliyan 15 daga iyalan wanda aka kashe kafin su kashe shi.   “Sun bugi wanda aka kashe a kai da ƙirji da sanda sannan daga baya suka binne gawar a gidan Adamu da ke Dawakin Kudu,” in ji mai gabatar da kara ga kotun.   Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Aisha Mahmoud ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjoji game da karar da suka shigar a kan Adamu ba tare da wata shakka ba.   “Ina yanke wa Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya buga wa wanda aka kashe sanda a kansa da ƙirjinsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa....
    Hukumar kwallon kafa ta Nigeria (NFF) ta taya Osimhen murnar samun wannan babbar nasarar a kwallon kafa ta hanyar sanya hoton Osimhen a babban shafinsu na Facebook da yake da mabiya fiye da miliyan daya, Osimhen na daga cikin yan wasan da kocin tawagar ta Super Eagles Eric Chelle ya gayyata domin buga gasar kofin kasashen Afirka da za a buga a Morocco a shekara mai zuwa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Salah Ba Ya Cikin ‘Yan Wasan Liverpool Da Za Su Kara Da Inter Milan December 8, 2025 Wasanni Shirye-shiryen Fara Kofin Afirka: Abin Da Ya Kamata Ku Sani December 7, 2025 Wasanni Liverpool Ba Ta Yi Min Adalci Ba – Muhammad Salah December 7, 2025
    Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin Sin kadai ba, har da nuna yanayin sauyawar abubuwan dake haifar da ci gaba a duniya. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ta kafar intanet, ya nuna yadda masu bayar da amsa daga fadin duniya suka yi imanin cewa, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba ta kowace fuska ba tare da tangarda ba, lamarin da ya samar da tabbaci ga tattalin arzikin duniya....
    Mahukuntan kasar Sin sun gudanar da taron koli, na tattauna aikin raya tattalin arzikin kasar, don tsara abubuwan da za a aiwatar a shekarar 2026 dake tafe. An gudanar da taron ne a jiya Laraba da yau Alhamis, inda shugabannin kasar suka tantance abubuwa mafiya muhimmanci, wadanda za a aiwatar, dangane da raya tattalin arzikin kasar a shekara mai kamawa. Cikin muhimmin jawabi da ya gabatar yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya waiwayi aikin raya tattalin arziki da Sin ta aiwatar a shekarar nan ta 2025, tare da fayyace halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da ma aikin da aka tsara gudanarwa a shekara mai zuwa. Yayin taron, an yi amannar cewa shekarar 2025 ta fita daban,...
    Ministan Harkokin Waje na Jamhuriyar Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce kimanin sojoji 200 daga Najeriya da Ivory Coast yanzu haka na cikin kasar shi a matsayin wani ɓangare na aikin tsaro don tallafa wa gwamnati. Ƙaramar ƙasa ta Yammacin Afirka ta girgiza da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar Lahadi, wanda ya sa Najeriya, Faransa da Ivory Coast suka tashi tsaye wajen goyon bayan gwamnatin farar hula. Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota “A halin yanzu akwai kusan sojoji 200 da suka zo don ba da taimako ga rundunar tsaron Benin a cikin aikin sharewa da tsaftacewa,” in ji Olushegun Adjadi Bakari ga ’yan...
    Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo. Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar. Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar Alhamis, inda aka garzaya da shi zuwa Cibiyar Lafiya ta Ƙasa (FMC) da ke Yenagoa. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. An haifi Ewhrudjakpo ranar ranar biyar ga watan Satumban 1965, a ƙauyen Ofoni da ke Ƙaramar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa. Ya rasu yana da shekaru 60. Kodayake ba a san ainihin dalilin faɗuwarsa ba, majiyoyi sun ce ya faɗi ne ba zato ba...
    Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso. Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya yi, ta kuma dauki nauyin da ya dace akan batun Falasdinu. A can Amurka kuwa, manzon musamman na Amurka akan harkokin yammacin Asiya, Barrack ya  fada wa jaridar  “Jerrusalem Post” cewa: Kasar Turkiya tana da sojoji masu karfi, kuma tana hulda da Hamas, a dalilin hakan shigarta cikin rundunar da za a aike Gaza, zai yi amfani.” A ranar 18 ga watan Nuwamba ne dai...
    Ministan taron  Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ben Gafir ya sha alwashin rushe kabarin Sheikh Izzuddin al-Kassam dake kusa da birnin Haifa. Ben Gafir ya wallafa hotonsa na tsokana a shafinsa n asada zumunta a kusa da makwancin shahararren malamin addinin mususuluncin tare da motar buldoza a kusa da shi, tana rusa wata hema da aka gina daura da kabarin, wacce mutane suke yin salla a cikinta da kuma yin addu’oi. Sheikh Izzuddin al-Kassam  da reshen soja na Hamas ke dauke da sunansa, malamin addini ne wanda ya yaki Birtaniya da ‘yan sahayoniya a lokacin da suke share fagen gina haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya yi shahada ne dan lokaci kadan gabanin shelanta kafuwar wannan haramtacciyar kasa a 1948. Makwancinsa ya a garin...
    Shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro wanda yake mayar da martani akan kwace jirgin ruwa na dakon man fetur da Amurka ta yi a kusa da Venezuela ya ce; Abinda faru wani sabon salon fashi da makami ne akan doron  ruwa da Amurkan ta bude. A ranar Larabar da ta gabata ne dai sojojin Amurkan su ka kutsa cikin wani jirgin ruwa na dakon man fetur a tekun carriebia, su ka kwace iko da shi. Wannan matakin da Amurkan ta dauka dai ya sa kasuwar man fetur ta duniya ta yi tangal-tangal,sannan kuma ya kara zaman man na da doya dake tsakanin Amurkan da Venezuela. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela ta fitar ta yi tir da...
    Kamfanin samar da siminti na BUA ya bayar da tallafin karatu Naira miliyan 40 ga ɗalibai 200 da ke manyan makarantu a jihohin tsohuwar Jihar Sakkwato. An bayar da tallafin domin ganin sun cimma burinsu a fannin ilmi. An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota Ɗaliban da suka ci gajiyar sun haɗa da matasa 50 daga Sakkwato, 50 daga Kebbi da 50 daga Zamfara, sai 50 a Wamakko inda cibiyar kamfanin simintin yake. Kowane ɗalibi zai karɓi Naira dubu 200, an samu ninkin ɗaliban kuɗin ma an samu ƙari da kashi 100 bisa ga shekarun baya. Shugaba kuma Daraktan kamfanin, Injiniya Yusuf Binji ya ce sun ninka yawan ɗalibai...
    Aƙalla ɗalibai takwas na Jami’ar Jos ne aka ruwaito sun mutu, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka, a wani mummunan hatsarin da ya rutsa da wata tirela da wata motar bas. Hatsarin ya faru ne a hanyar Zariya, cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar daren ranar Alhamis lokacin da ɗaliban ke dawowa daga wani biki. Jami’in kula da wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Peter Yakubu Longsan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa motar bas...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar kula da masu bukata ta musamman a jihar Jigawa za ta gudanar da aikin gyaran gidajen gajiyayyu na shiyyar Birnin Kudu da Gumel a sabuwar shekara. Shugaban hukumar, Malam Sale Zakar Kafin Hausa, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa. Ya ce gidan gajiyayyu na shiyyar Birniwa yana cikin kyakkyawan yanayi da kulawa sosai ta fuskar abinci da sutura da kayan wanka da na wanki da sauran bukatun rayuwa, dan haka gwamnati ta kuduri niyyar gyara sauran gidajen gajiyayyun domin kyautata yanayinsu. Malam Sale Zakar ya ce an Kara yawan mata masu juna biyu da masu shayarwa da ke amfana da Shirin kula...
    Zuwa karfe 5:41 na daren ranar 7 ga watan Disamba, fim din Amurka “Zootopia 2” wanda aka fara nuna wa kwanaki 12 da suka wuce (tun daga ranar 26 ga Nuwamba), ya samu kudaden shiga a cikin kasar Sin da yawansa ya wuce yuan biliyan 30 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 424.8, adadin da ya zarce kudaden shiga da ya samu a kasashen Arewacin Amurka, har ya sa kasar Sin ta zama kasa mafi taka rawa wajen samar da kudin shiga ga wannan fim a duniya. Hakan kuma ya nuna yadda Sin ke da babbar kasuwar fina-finai. Ibrahim Akopari Ahmed, jami’in kula da harkokin cinikayya a Najeriya, a zantawarsa da dan jarida a baya, ya taba bayyana cewa, “Najeriya na daya...
    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta lalata kayayyaki marasa inganci da suka kai sama da Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa. Kayayyakin da aka ƙwato daga jihohin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da Nasarawa, Benuwe da Kogi da Filato, an lalata su ne a wurin zuba shara a Angwan Rere da ke Lafiya. Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, wanda Daraktan shiyyar Arewa ta Tsakiya, Mista Kenneth Azikiwe ya wakilta, ya bayyana cewa an ƙwace kayayyakin ne a lokacin gudanar da aikin sa ido. Ta kuma jaddada cewa hukumar na da burin hana waɗannan...
    Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila da kakkausar murya kan gazawarta wajen cika alkawarin da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Abduljabbar Saeed, memba na ofishin siyasa na Hamas, ya yi bayani na musamman kan tattaunawar da ake ci gaba da yi da masu shiga tsakani game da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a wata hira da Qods News a ranar Laraba. Ya bayyana cewa dukkan bangarorin da abin ya shafa sun yarda cewa gwamnatin Isra’ila ba ta cika mafi yawan wajibai nata ba a matakin farko. Saeed ya koka da cewa, a lokacin matakin farko na tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da kashe fararen hular Falasdinawa, ciki har da yara da mata,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa. Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana’o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta. NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Farfesa Amina Salihi Bayero, a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar Northwest. Naɗin nata zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamban 2025, har zuwa tsawon shekaru biyar. EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar, ta ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan  tantancewa da kwamitin gudanarwar jami’ar ya yi mata. A matsayinsa na jagoran jami’ar, Gwamna Abba, ya yaba wa shugaban kwamitin da mambobinsa kan jajircewarsu wajen bin ƙa’idojin tantancewar. Haka kuma ya nemi...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara. Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa. A cewar ta, za su mayar da hankali wajen inganta shirye shiryen bunkasa rayuwar mata da al’amuran da su ka jibinci kananan yara domin bada kariya ga masu rauni a cikin al’umma. Hajiya Hadiza Abdulwahab ta ce ma’aikatar ta samu nasarori wajen aiwatar da tanade tanaden kasafin kudin 2025, yayin da za su ci gaba da daukar matakan da su...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun yi musayar wuta da yan ta’adda a kudu masu gabacin kasar, sannan wasu daga cikinsu su sun yi shahada sannan sun halaka yan ta’adda da dama. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya dakarun na IRGC guda uku nesuka yi shahada a wannan fafatawar, a jiya Laraba a garinLar da ke kusa da birnin Zahidan babban birnin Lardin. Garin Lar dai yana kan iyakar kasar Iran da Pakisatan, kuma  ba wannan ne karon farko wadanda dakarun suke fafatawa da yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan kasashen waje ba. Kuma suke da sansanoninsu a cikin lardin sitan Baluchistan na kasar Pakistan ba. Har yanzun dakarun rundunar Qudus wanda suke aiki...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa dole ne musulman kasar Yemen maza da mata sun bi tafarkin addinin musulunci na kaiwa ga daukaka idan suna son daukaka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran nakalto Al-Huthi yana fadar haka a jiya Laraba da yamma a lokacinda yake magana kan zagayowar ranar haihuwar Fatimah Azzahra diyar manzon Allah (s). Malamin ya kara da cewa, Fatimah (a) abin koikoyo ne ga dukkan musulmi maza da mata a sanin Allah da halaye masu kyau don samun kusance ga Allah madaukakin sarki. Al-Huthi ya kara da cewa a halin yanzu musulmi a ko ina suke a duniya suna fuskantar matsaloli, musamman musulman kasar Falasdinu wadanda HKI ta...
    Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama tare da tsare Tsohon Ministan Ƙwadago kuma Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chris Ngige. Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe ne, ya tabbatar da hakan da safiyar ranar Alhamis. bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewar an sace Ngige. An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC Chukwuelobe, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi aka yi ba.” Har zuwa yanzu EFCC ba ta bayyana dalilin da ya sa ta tsare Ngige ba. Ana sa ran hukumar za ta fitar da sanarwa game da kama...
    Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi. A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje. Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC Ana zargin mutanen da rarraba ƙwayoyi a birane da dama a Indiya, inda suke amfani da kamfanonin bayar da kaya don ɓoye ƙwayoyin da suke safara. An gano mutanen suna da alaƙa da wani ɗan Najeriya mai suna “Nick,” wanda ake nema ruwa a jallo, kuma...
    Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi. A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje. Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC Ana zargin mutanen da rarraba ƙwayoyi a birane da dama a Indiya, inda suke amfani da kamfanonin bayar da kaya don ɓoye ƙwayoyin da suke safara. An gano mutanen suna da alaƙa da wani ɗan Najeriya mai suna “Nick,” wanda ake nema ruwa a jallo, kuma...
    Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ƙaryata zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa jami’yyar PRP. Jita-jitar ta samo asali ne bayan Sakataren jam’iyyar PRP na Bauchi, Hon. Wada Abdullahi, ya ce ba za su karɓi gwamnan zuwa jami’yyarsu ba. Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky Ya ce gwamnan bai cika ƙa’idojin da PRP ke buƙata ba a shugabancinsa a Bauchi. Amma mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya ce gwamnan bai taɓa tunanin barin PDP ba. Ya ce babu wata tattaunawa ko mataki da aka ɗauka na komawa PRP. Gidado, ya ce gwamnan na aiki ne wajen...
    Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta nuna damuwa kan rudanin siyasa a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito. Shugaban Hukumar ECOWAS Omar Touray ya shaida wa taron ministoci a Abuja babban birnin Najeriya cewa, “Abubuwan da suka faru a ‘yan makonnin da suka gabata sun nuna bukatar yin tunani sosai kan makomar dimokuradiyyar yankin da kuma bukatar saka hannun jari cikin gaggawa a harkokin kasuwanci da tsaro.” Sanarwar ta zo ne bayan wani yunkurin juyin mulki a kasar Benin a karshen makon da ya gabata, wanda ya biyo bayan nasarar juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau. Touray ya ce akwai manyan hadura da dama da suka hada da rashin bin ka’idojin mika mulki...
    Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya. Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ‘yan kasar bakwai da suka hada da ‘yan majalisar wakilai hudu, an tsare su ba tare da wani dalili ba, kuma an sake su ne bayan shafe sa’o’i masu yawa ana tatatunawa ta shiga tsakani na diflomasiyya, yayin da aka kori wasu uku. Tawagar majalisar ta kasance tana halartar wani taron kasa da kasa kan harkokin tsaro...
    Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu. Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun ruwa yadda ya kamata. Yayin da yake bayyana jimaminsa bisa wannan lamari, Dr. Muhammad Uba ya basu tabbacin cewa In Shaa Allahu matsalar ta zo karshe. A cewarsa, majalisar ta kudirin aniyar yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da ake fuskanta tare da tabbatar da samun isasshen tsaftataccen ruwan sha ga al’umma. Ya yi alkawarin tura dukkan kayan aiki da ake bukata domin...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu da ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar Taron manema labaran wani ɓangare ne na shirye-shiryen hukumar na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya. Barista Salisu Abdul ya ƙara da cewa, cin hanci babban abin da ke janyo koma-baya ne ga Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a...
    Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015. Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya. Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025 Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa Lamarin fara a matsayin ƙaramin rikici daga baya ya rikiɗe zuwa babban al’amari, lamarin da ya sanya sojoji buɗe wa mabiyan wuta. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da kwamitin bincike na jihar, sun bayyana cewa an kashe tare binne ɗaruruwan mambobin IMN a asirce bayan faruwar...
    Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma nusar da Alumma kyakkyawar makoma. Kyawawan halayen musulunci wasu ginshi kai ne da suke daidaita maza da mata, saboda Al’qur’ani yayi alkawarin kyakkyawar rayuwa ga wadanda suka yi kyawawan ayyuka, da gaskiya ba tare da la’akari da jinsin su suba, haka zalika ya jaddada wannan ka’ida inda aka tsara mata ba a matsayin na biyu ba, amma a matsayin muhimmin abokan hulda wajen gina ci...
    Daga Aliyu Lawal  Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja. Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai ɗari da aka...
    Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta. Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania. Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba. A...
    Hukumar EFCC ta tsare tsohon Antoni-Janar na Tarayya, Abubakar Malami, saboda binciken da ya shafi dawo da wani ɓangare na kuɗaɗen Abacha. Hukumar ta kira Malami a makon da ya gabata, inda ta yi masa tambayoyi kan wani bincike da ta ke inda ta sake shi daga bisani, amma yanzu ta tsare shi. Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro Malami ya ce bai aikata komai ba, kuma ba shi da alaƙa da abin da ake zargi. A cikin wata sanarwa, ya ce: “Ba a taɓa zargina, gayyata ko bincikena game da tallafa wa ta’addanci ba. Duk wani yunƙuri na danganta ni da irin wannan...
    Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar musayar bayanan leƙen asiri, horas da sojoji, haɗin gwiwa a harkar samar da kayan yaki da kuma gudanar da ayyukan tsaro tare. Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa ’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta bana Minista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari...
    Zanga-zanga ta ɓarke a yankin Numan da ke Jihar Adamawa, kan zargin sojoji da kashe wasu mata a garin Lamurde. Mata sun fito zanga-zangar ne sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin kabilu Bachama da Chobo. An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji A lokacin zanga-zangar an ruwaito cewar mata bakwai ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata. Shaidu sun ce sojoji sun buɗe musu wuta yayin da suke tare hanya, suna zargin rundunar da goyon bayan wata ƙabila. Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta musanta wannan zargi. Ta ce dakarun sun yi artabu ne da wasu ‘yan bindiga a...
    Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari. Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna. Dubban mutane ne suke guduwa domin tserewa lugudan makaman roka da ake harbawa daga Cambodia. Kazalika Thailand ma na ci gaba da kai wa Cambodia hare-hare ta sama. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana kyautata tsammanin zai gana da  shugabannin kasashen biyu ta wayar tarho, wanda ya matsa musu lamba aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yulin da ya gabata. To sai dai ministan...
    Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara. Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba. Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Dantawaye ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, kuma tawagar musamman ta rundunar ce ta kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri a Unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada. Ya ce binciken farko ya...
    Al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana farin ciki bayan samun labarin kashe fitaccen ɗan bindiga da ya dade yana addabar yankin gabashin jihar, Kacalla Kallamu. Rundunar Sojoji ta 8 ta hallaka jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen haɗin gwiwa da aka kaddamar a ƙaramar hukumar Sabon Birni. Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka Wata majiyar soja da ta tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata ta bayyana samamen a matsayin “babbar asara ga cibiyar ’yan bindigar Bello Turji,” tana mai cewa Kallamu shi ne babban na hannun daman Turji. A...
    Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe. Sai dai ba a bayyana sunan dalibin ba. DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka Majiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma...
    Daga Aminu Dalhatu Uwargidar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, murna bisa nadin ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife na  Jihar Osun. Nadin ya kasance wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 10 na Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II akan karagar mulki na Ooni Ife, wanda ya jawo sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassan kasar nan. A wata sanarwa da sakatariyar yada Labarai ta Uwargidar Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta bayyana karramawar da aka yi wa Sanata Oluremi a matsayin abin yabawa, inda ta ce karramawar ta yi daidai da jajircewarta wajen ci gaban kasa, tallafawa mata, da kuma gudummawarta...
    A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat. Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar. Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.
    Tehran tana daukar bakwancin taron kwamitin bincike da ci gaban na kungiyar BRICS karo na 7Th wanda ya nuna irin yadda kasar Iran take ci gaba a cikin ilmin bincike da kuma na ci gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu taron na fadar cewa kasar Iran ta na samun ci gaban a zo a gani a bangaren ci gaban ilmin zamani a fannoni daban-daban. Wannan kuma ya bayyana cewa, wannan ya nuna irin ci gaban da kasashen BRICS suke samu wanda zai babu damar sauya duniya, ko samar da sabuwar duniya tare da kasashen global South, ko kasashe masu tasowa. Labarin ya kara da cewa wannan ya nuna irin yadda kungiyar BRICS take kokarin ganin...
    Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar shugaba Bola Ahmed Tinubu na aika sojoji zuwa kasar Benin saboda tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan yunkurin juyin mulki wanda wasu sojoji suka yi a cikin yan kwanakin da suka gabata. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawan Sanata Godwill Alpabio ne ya karanta bukatar shugaban a gaban majalisar ya kuma sami amincewarsu da baka ba tare da an kada kuri’a ba. Kafin haka dai shugaban Tinubu ya rika ya aika sojojin sama zuwa kasar ta Benin wacce take makobtaka da Najeriya daga yamma cin kasar, sai dai saboda cika bukatar kundin tsarin mulkin kasar na bukatar samun amincewar Majalisar shugaban ya rubuta mata yana neman amincewarta....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan kare dangi ga Najeriya. Ko wannan ziyarar da tawagar Amurka ta kawo zai kawo karshen matsalar tsaron da Najeriya ke ciki? NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
     Ministan makamashi na Iran Abbas Ali Abadi ya bayyana cewa; A halin yanzu Iran tana da ilimin aikewa da sanadarori cikin sararin samaniya da za su samar da hadari domin yin ruwan sama Ministan makamashin na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban majalisar shawarar musulunci ta Iran  a jiya Talata ya ce; Aiki da aka yi a tsakanin gwamanti da majalisar dokoki da kuma cibiyoyin kwararru, shi ne ya kai ga samar da hukumar da take sanya idanu akan sauyin yanayi wanda ke iya samar da hadari da kuma yin ruwan sama. Ministan ya yi Ishara da cewa sun bi matakai hudu domin ganin an isa wannan matsayin; Na farko dai shi ne; Amfani da na’urorin Radar domin...
    Marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce kamata ya yi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tura ɗansa, Seyi Tinubu, zuwa Jamhuriyar Benin domin “kwantar da” yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba. Soyinka ya soki matakin Tinubu na tura dakarun rundunar Sojojin Sama ta Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi domin kifar da Shugaba Patrice Talon daga mulki. Ya yi wannan jawabi ne a bikin bayar da kyaututtuka na shekara karo na 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas ranar Litinin. Fitaccen marubucin ya tuna yadda ya ga jami’an tsaro masu makamai sosai suna gadin Seyi Tinubu a Legas. Ya ce: “Shugaba Tinubu bai...
    Marubuci kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya ce kamata ya yi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tura ɗansa, Seyi Tinubu, zuwa Jamhuriyar Benin domin “kwantar da” yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba. Soyinka ya soki matakin Tinubu na tura dakarun rundunar Sojojin Sama ta Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi domin kifar da Shugaba Patrice Talon daga mulki. Ya yi wannan jawabi ne a bikin bayar da kyaututtuka na shekara karo na 20 da Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta shirya a Legas ranar Litinin. Fitaccen marubucin ya tuna yadda ya ga jami’an tsaro masu makamai sosai suna gadin Seyi Tinubu a Legas. Ya ce: “Shugaba Tinubu bai...
    Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana. ’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru a rukunin rahoton jarida da kuma na talabijin mafi daraja a bana a Najeriya. Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato Hanafi ya lashe rukuni na rubutu bisa labarinsa mai taken: “Bincike: Dan jarida ya samu ayyuka biyu da takardun bogi na Oluwole.” Wanda ya zo na biyu...
    Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar. Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar. Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta Bukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta. Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka....
    Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta bada tabbacin ci gaba da kulawa da harkokin rigakafi da kiwon lafiya baki daya. Shugaban karamar hukumar, Builder Muhammad Uba ne ya bada wannan tabbacin lokacin taro da ake gudanarwa a kowace rana kan al’amuran rigakafin cutar Polio da aka gudanar a fadar Hakimin Birnin kudu. Yace karamar hukumar zata kara da bada fifiko wajen tallafawa harkokin rigakafi domin dakile yaduwar cututtuka a yankin. A don haka, Builder Muhammad Uba ya bukaci iyaye su kara himma wajen bada hadin kai da goyon baya ga jami’an lafiya a duk lokacin da ake gudanar da rigakafi. A jawabin da ya gabatar mai kula da al’amuran rigakafi na yankin, Malam Abubakar Alhassan Garki...
    Faransa ta tabbatar da sa hannunta wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin. Fadar gwammnatin faransa ta Élysée ta ce bisa bukatar hukumomin Benin ta bayar da “goyon baya ta fuskar bayar da bayanai da dabaru” ga sojojin Benin a matsayin martani ga yunkurin juyin mulki da aka dakile a karshen makon da ya gabata. Sanarwar ta ce Emmanuel Macron ya yi hadin gwiwa” da “musayar bayanai da kasashen yankin,” in ji daya daga cikin masu ba shi shawara ga manema labarai, a cewar AFP. Shugaban Faransa ya yi magana a ranar Lahadi da takwaransa na Benin, Patrice Talon, wanda sojoji suka nemi su hambarar, da kuma shugaban Najeriya da kuma kasar Saliyo. Kasar Saliyo ce ke rike da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta yi maraba da bayannan cewa an cire sunantsohon firaministan Burtaniya Tony Blair daga wadanda ake tunanin zasu jagoranci Gaza a shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump a Gaza. Jaridar Financial Times ta ruwaito a ranar Litinin cewa kasashen Larabawa da na Musulmi ne suka nuna adawa da shigar da M.Blair cikin “hukumar rikon kwarya” da Trump ya bayyana a matsayin wani bangare na shirinsa na zaman lafiya a Gaza. Tony Blair ya sha suka a faɗin duniyar Musulmi saboda rawar da ya taka a mamayar da Amurka ta jagoranta a Iraki a shekarar 2003, wanda daga baya aka gano cewa kawai zarge-zargen karya ne. Wani Jami’in Hamas, Taher al-Nunu, ya ce rahotannin...
    Karin bayani na tafe
    Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ayyana dokar ta-baci a yankin, kwana biyu bayan yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Jamhuriyar Benin. Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da haka a yayin zaman majalisar tsaro ta hukumar karo na 55 a Abua. Touray ya ce daukar matakin ya zama dole domin shawo kan barazanar da juyin mulki ke wa tsarin dimokuradiyya a yankin, wanda ke bukatar matakan zuba jari na gagagwa domin tabbatar da tsaron al’umma. A yayin jawabinsa ga ministoci da manyan jami’an gwamnati da ke halartar taron, ya bayyana yadda yawaitar samun juyin mulki  a Yammacin Afirka ke barazana ga tsaro da zaman lafiya a yankin. Sojoji sun kashe...
    Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranr litinin da ya gabata. Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara da cewa kungiyar kasashen AES sun tilastawa jirgin sauka a Bobo Dioulasso na Burkina Faso bayan zargin cewa jirgin ya keta hurumin sararin samaniyar kasar ba tare da izini ba. A halin yanzu dai ana saran za’a warware matsalar da ke tsakanin kasashen biyu sannan jirgin zai kama hanyarsa zuwa kasar Portigal kamar yadda aka tsara. Labarin ya kara da cewa, jirgin ya tashi daga...
    Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa Muhsin Umar Chiroma wanda aka fi sani suna SKD Arewa, xaya ne daga cikin matasan mawaqan zamani da ludayinsu ke kan dawo wajen tashe, musamman a shafukan sada zaumunta. A hirarsa da Aminiya, saurayin mawaqin ya bayyana abin da ya xauki hankalinsa har ya yi wata waqa da ya yi wa laqabi da suna ‘Arewa’. Muhsin wanda ya fi qwarewa a fagen waqoqin ‘Gambara’, da aka fi sani da Hip Hop, bayyana wa Aminiya cewa, halin da Arewacin Nijeriya ya shiga na rashin tsaro shi ne jigon waqarsa. A cikin waqar haziqin mawaqin, ya yi tsokaci a kan yadda shugabanni a Arewa suka yi biris da halin da talakawa...
    Gwamantin Nigeria ta aike da jiragen yaki zuwa kasar Benin domin taimaka wa gwamnatin farar hula domin dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar. Aikin da jiragen yakin su ka fara yi, shi ne shimfida ikonsu a sararin samaniyar kasar Benin a ranar Lahadin da ta gabata,adaidai lokacin da sojoji da suke biyayya ga shugaba Patrice Talon su ka fafatawa da sojojin da suke kokarin mayar da doka da oda. Ofishin shugaban kasar ta Nigeria, Ahmad Tininu ya kuma yi bayanin cewa; Daga cikin ayyukan da sojojin na Najeriya su ka yi a tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Benin masu biyayya ga gwamnati, shi ne sanya idanu da kuma zama cikin ko ta-kwana domin aikewa da sojoji...
    A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci. Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”. Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da...
    Daga Aliyu Muraki  Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ce a taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna kwanan nan.   A cewarsa, gwamnonin Arewa sun amince cewa kowace jiha za ta rika bada gudummawar Naira Biliyan Daya a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudin da zai taimaka wajen magance...
    Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni. Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan. Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun ...
    Daga Isma’il Adamu Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe karin mukaman siyasa a zaben shekarar 2027, ciki har da na shugaba kasa da gwamnan Jihar Katsina. Sabon shugaban jam’iyyar da aka rantsar a Jihar Katsina, Alhaji Armaya’u AbdulKadir ne ya bayyana haka a zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Katsina. Ya ce jam’iyyar, wacce ta ba da muhimmanci ga ilimi, walwalar jama’a, karfafa matasa da ci gaban abubuwan more rayuwa, ta kara samun farin jini a wajen jama’a saboda ingantaccen jagoranci da wakilcin da take bayarwa ta hannun mambobinta da ke rike da  mukamai a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya. “Masu zabe sun ga abin da jam’iyyarmu ke aiwatarwa. ‘Yan majalisa da sauran wadanda...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Sakkwato (ASUU-SSU), ta zargi Mataimakin Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor) da kin bin umarnin Gwamnan Jihar Sakkwato game da sauke Bursar da ya kai lokacin ritaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Sakkwato a ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025, ƙungiyar ta ce Gwamna Dr. Ahmed Aliyu Sakkwato, wanda shi ne Visitor na Jami’ar, ya amince da buƙatarsu na tabbatar da bin dokokin Jami’ar ta hanyar amincewa da ritayar Bursar ɗin. ASUU-SSU ta bayyana cewa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Sakkwato ya aika da takardar umarni mai lamba HS/ADM/101/VOL-1, ɗauke da kwanan wata 18 ga Nuwamba 2025, wadda ta umurci Bursar ya miƙa ragamar ofis ga jami’in da ya fi kowa...
    Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka – Ecowas – ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin jiya Lahadi, ta ce “Shugaban Ecowas, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar ya amince da tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Benin nan take. Dakarun sun kunshi sojoji daga kasashen Najeriya da Saliyo da Cote d’Ivoire da kuma Ghana. Kuma za su taimaka wa gwamnati da kuma dakarun Jamhuriyar Benin wajen kare martabar kundin tsarin mulki da na kasar ta Benin.” Rahotanni daga jamhurriyar Benin na nuni da cewa an kama sojoji da dama bayan wani yunƙurin juyin mulkin da bai...
                Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa. Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na  jihar Sokoto. Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba. Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzamu na dakarun sun fada kan matatar man fetur na Haifa a HKI har sau biyu a yakin kwanaki 12 da ta fafata da Iran a cikin watan Yunin wannan shekara. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Ali Mohammad Naeini kakakin dakarun ya na fadar haka a jiya Lahadi a wani taro, ya kuma kara da cewa makaman har’ila yau sun kashe jami’an hukumar leken asirin HKI MOSAD har 36 a wani hari kan ginin hukumar a cikin yakin. Naeini, ya kara da cewa HKI ta yi kuskuren lissafi a lokacinda ta farwa kasar Iran da yaki a cikin watan Yunin...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan makaranta har 100 daga cikin wadanda yan ta’adda suka sacesu a wata makarantar cocin Khatolica a cikin jihar Naija. Kafin haka an ce yara kimani 50 sun tsere daga hannun yan ta’addan bayan an sacesu. Tashar talabijin ta ‘Chennel TV ‘ ta bada labarin cewa sakin yan makarantan, amma bata nuna hotunansu ba kuma bata yi wani karin bayani ba. Sannan kungiyar kiristoci ta Najeriya...
    Firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani ya bayyana cewa gwamnatinsa bata tushe asusun kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Ansarallah ta kasar Yemewn ba. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran IP ya nakalto sudanina cewa gwamnatinsa tana kokarin hana tasowar wani riki a yankin sannan da kuma kaucewa duk wani rikicin siyasa a cikin gida ne, tare da wasu matakan da ta dauka. Yace babu wani shiri na daukar Hizbullah da Ansarullah a matsayin kungiyoyin yan ta’adda. Y ace kasar Iraki bata adawa da wadan nan kungiyoyi sannan basa da kadarori a kasar wadanda za’a kwace ko a hanasu amfani da su. Y ace matsayin Iraki a kan wadan nan kungiyoyi da kuma palasdinu baya canzawa. Kungiyar...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba. Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.   Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na buƙatar abubuwa masu yawa kafin su iya ɗaukar wannan nauyi, banda batun samar da dokar samar da wadannan ‘yansanda, akwai batun samar da kayan aiki da horo da sauran abubuwa da ake bukata don gudanar da dawainiyar ‘yansandan. NAJERIYA A YAU: Abun Da Masu Ruwa Da Tsaki Ke Yi Na Dakile Laifuka A Wurin Matasa DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin...
    Jami’an Rundunar Leƙen Asiri ta musamman a Jihar Kwara sun cafke wani tsohon ɗan gidan yari mai suna Godday Agaadi da bindiga ƙirar AK-47. An kama Emmanuel Okah ne bayan an same shi da bindigar AK-47 da harsashi guda 25 a jikinsa, a lokacin da yake sanye da kayan ’yan sanda. Dubunsa ta cika ne yana ƙoƙarin satar talotalo a unguwar Omu Aran da ke ƙaramar hukumar Irepodun. Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya bayyana a taron manema labarai a ƙarshen mako cewa binciken da jami’an suka gudanar ne ya kai ga cafke Agaadi. An kama sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulki a Benin An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja Ya ƙara da...
    Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma. Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa ƙasar cikin rudani. Gwamnatin Benin ta ce ta shawo kan lamarin bayan wasu sojoji sun bayyana a talabijin na ƙasar cewa sun kifar da Shugaba Patrice Talon. Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan juyin mulki a ƙasar Guinea-Bissau. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da kama sojoji kusan 12, ciki har da shugabannin yunƙurin da bai yi nasara ba. Talon, tsohon ɗan kasuwa mai shekaru 67,...
    Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba. Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya. Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati. Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa. Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da ya ɓace a Neja Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sun kuma ayyana Laftanar Kanar Tigri Pascal a matsayin Shugaban gwamnatin soja. Daga baya gwamnatin Benin ta sanar da cewa sojojin ba su yi nasarar yin juyin mulkin ba. Rahotanni sun nuna cewa jiragen yaƙin Najeriya sun shiga ƙasar domin kare dimokuraɗiyya, duk da cewa babu cikakkun bayanai ba....
    An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun hallaka mutum 4, sun sace mata 4 a Sakkwato Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin An gano gawarsa ne da safiyar ranar Lahadi. Rahotanni sun nuna cewa an ƙone al’aurarsa, sannan an samu kwalin ashana a gefen gawarsa. Shugaban al’ummar yankin, Malam Mahmud Dalhatu Iya, ya shaida wa Aminiya cewa iyalan mamacin sun riga sun gano gawar kuma an riga an binne...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa. Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani na kungiyar, Khalil al-Hayya, ne ya bayyana hakan inda yake cewa idan mamayar ta kare, za a sanya wadannan makaman a karkashin ikon gwamnatin kasar Falasdinu.” Ofishinsa ya fayyace cewa kalmar “ƙasa” tana nufin “ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta” mai cikaken iko. “Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa game da kwance makamai tsakanin kungiyoyi daban-daban da masu shiga tsakani, kuma yarjejeniyar tana cikin farkon...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin A cewarsa, “Sun ratsa gefen gari suka dinga shiga gida-gida. Sun harbe mutane huɗu; uku sun mutu nan take, na huɗu kuma ya rasu a asibiti.” Ya ƙara da cewa bayan harin, sojoji sun isa garin wanda hakan ya sa maharan suka tsere, amma duk da...