Za’a Gurfanar Da Mutane 40 A Gaban Kotu Kan Zargin Yin Barazana Ga Tsaron Kasa A Tunisiya.
Published: 4th, March 2025 GMT
A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama suke daukarta a matsayin bi ta da kullin siyasa.
Wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an diflomasiyya da yan siyasa da lauyoyi da kuma yan jarida dake sukar salon mulkin shugaban kasar Kais Saied.
Zargin yi wa tsaron ƙasa zagon kasa da kuma shiga kungiyar yan ta’adda zai fuskanci hukunci mai tsananin, ciki har da hukuncin kisa.
Tun a shekara ta 2023 ne ake tsare da wasu , yayin da da dama kuma suka tsere zuwa kasashen ketare.
Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis don nuna adawa da shari’ar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta zargi Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kin yin adalci wurin ayyuka da raba mukamai tsakanin Arewa da Kudancin Kasar nan.
Wadannan zarge-zarge suka sa fadar Shugaban Kasa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan kafofin yada labarai Bayo Onanuga mayar da martani ga kungiyar ta ACF.
Ko wadanne irin martani fadar shugaban kasar ta mayar ga kungiyar?
NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan