2025-09-18@06:29:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 109

«kiwon Tarwadar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
    Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek. Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza. Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15. A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan...
    Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
    Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.   Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.   Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.   Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
    A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma  kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....