’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo
Published: 3rd, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama mutane 95 da ake zargi da ayyukan ƙungiyoyin asiri.
An kama mutanen ne a wani farmaki da aka kai kan masu aikata laifukan da suka shafi kungiyoyin asiri a garin Benin City da kewaye a makon da ya gabata.
Kwamishinan ’yan sanda, Monday Agbonik, ya bayyana cewa an gurfanar da 64 daga cikin wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyoyin Maphites, Eiye, da Aye kuma ake zarginsu da kisan gilla da aka yi kwanan nan a rikicin kungiyoyin asiri.
Kayan da aka ƙwato sun hada da bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga guda mai tashi daya, da harsashi 24.
’Yan sandan sun shawarci iyaye da su kula da ayyukan ’ya’yansu kuma sun gargadi matasa da kada su shiga kungiyoyin da ba bisa ka’ida ba wadanda ke kawo hatsari ga rayuwarsu.
Bincike na ci gaba da gudana kan sauran wadanda ake zargin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda kungiyar asiri zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Nijar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa
Kasashen Iran da Nijar sun gudanar da taron kwamitin hadin gwiwa kan tattalin arziki.
An gudanar da taron ne a gefen taron baje koli na Iran 2025, karo na bakwai na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda aka fara a birnin Tehran a ranar Litinin.
Mohammad Atabak, ministan masana’antu, ma’adinai, da kasuwanci na Iran; da Mohammad Ali Dehghan Dehnavi, shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta Iran; da Sahabi Oumarou, ministan mai na Nijar, ne suka halarci taron.
Da yake jawabi a wajen taron, Atabak ya ce, bayan shafe shekaru 13 da aka shafe ana aikin kwamitin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar, “Muna fatan inganta dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashenmu biyu ta hanyar wannan takardar hadin gwiwa.”
Dehghan Dehnavi ya jaddada cewa, an gudanar da tattaunawa mai zurfi a cikin kwanaki biyun da suka gabata, inda masana suka yi nazari tare da musayar wasu tanade-tanade na hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar.
Ya ci gaba da cewa kwararrun da suka halarci taron sun amince da ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Iran da Nijar a bangarori da dama.