2025-12-12@16:52:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 508
«kimiyya da fasaha»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
Hukumar kulada jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta shirya fara shirin wayar da kai da ilmantarwa ga maniyyata aikin hajjin bana. Shugaban hukumar, Malam Salihu Abubakar, zai kaddamar da shirin ne a Cibiyar Wayar da Kai ta Alhazai da ke Dogarawa, shekkwatar karamar hukumar Sabon Gari. “Shirin horon wayar da kai yana nufin ilmantar da maniyyata kan dukkan muhimman abubuwan da suka shafi aikin hajji,” in ji shi. Wadannan sun haɗa da ilimin sanin ka’idojin shari’ar Musulunci da dokokin aikin hajji, da kuma warware matsalolin da ka iya tasowa domin tabbatar da sauƙi da ingantaccen hajji ga dukkan maniyyata. Ya kuma bayyana cewa dukkan maniyyata, da waɗanda ke son yin rijista kafin ranar karshe...
Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala. Da zarar shugabannin jam’iyyar sun amince, ni na shirya fara aiwatar da aikin kiranyesa,” in ji Waiya. Taron ya samu halartar shahararrun mutane, ciki har da Alhaji Lawan Husaini Dala, shugaban NNPP na Dala; da Alhaji Dayyab Ahmad Maiturare, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, da Hon. Suraj Kwankwaso, da sauransu.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan. Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya. Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama. Babban bako na musamman ya jaddada...
An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar Birnin Dabo. An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania Sai dai tun a jiya Juma’a ce mai magana da yawun ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗin cewa ’yan ta’adda na shirin kai hari a jihar saboda haka jama’a su ƙauracewa duk wani taro da shiga cunkoso. Daga bisani...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane 300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
