2025-11-02@10:43:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6422

«Alhaji Haruna Maiyasin»:

    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba waɗanda ke kashe mutane ba gaira ba dalili. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a yau a wajen bikin yaye sabbin jami’an tsaron cikin gida (Community Watch Corps – CWC) guda 100, a karo na uku...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da Naira biliyan 5.8 domin biyan haƙƙin tsoffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a jihar. Kwamishinan kuɗi na jihar, Mohammed Abatcha Geidam, ya ce wannan mataki na nuna yadda gwamnatin ke ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikatanta, musamman waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban...
      Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)...
    Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya ce afuwar shugaban ƙasa ya yi masa, ta ba shi kwarin guiwar yin wata sabuwar tafiyar siyasa. Ya bayyana cewa ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda jagorancinta ya yi watsi da shi lokacin da ya fi bukatrsu. ’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina...
    Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da...
    Dakta Umar Kabir Yusuf-Bakatsinen da ya kirkiro manhajar Masjid Suite da ke sada zumuncin hada masallaci da masallata Daga Ibrahim B. Surajo Dakta Umar Kabir Yusuf matashin manazarci ne dan asalin Jihar Katsina da yake zaune a kasar Amurka wanda ya kirkiri wata manhaja mai suna Masjid Suite. A cikin hirar da ya yi...
    ’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP...
    Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya fice daga jam’iyyar PDP. Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah, ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook na ainihi, kodayake bai bayyana dalilin ficewar gwamnan daga jam’iyyar ba. Har ila yau, bai bayyana ko Gwamna Diri zai koma APC...
    Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya kai ziyarar ba-zata ta duba aiki a Asibitin karbar Haihuwa na Imamu Wali, na Marmara, da kuma Asibitin Sabon Bakin Zuwo. Ya kai ziyarar ce domin tabbar bin umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na wucin gadi wajen sauya...
    Ya ce manufofi da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da tattalin arziƙin ƙasa da tafiyar da gwamnati, abin da ya sa zai yi wuya a kayar da shi a 2027. “Babu wani ɗan siyasa a yau da zai iya ƙalubalantar Shugaba...
    Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar.  Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya...
    Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia...
    Jagoran ’yan adawa na kasar Kenya kuma tsohon Firaministan kasar, Raila Odinga, ya mutu yana da shekaru 80 a lokacin da yake karɓar magani a ƙasar Indiya, kamar yadda majiyoyin asibiti da ’yan sanda suka tabbatar a ranar Laraba. Rahotanni daga Asibitin Devamatha da ke Kerala, kudancin Indiya, sun ce Odinga ya samu bugun zuciya...
    Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci. Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan...
    Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa. Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da...
    Rundunar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da aikin ceto har sai duk waɗanda aka sace sun kuɓuta kuma an dawo da zaman lafiya a jihar. Mohammed Gana Alhaji, wanda ya yi magana a madadin al’ummar Patigi, ya gode wa sojojin bisa ƙoƙarinsu na yaƙi da rashin tsaro da kuma kare al’ummar yankin. A ranar...
    Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ‎ ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi...
    Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta sanar da cewa, sake gina Gaza na bukatar dala biliyan 70, kuma a halin yanzu ana bukatar dala biliyan 20 domin fara ayyuka a cikin shekaru masu zuwa. UNDP ta yi tsokaci game da abin ta kira alamomi masu kyau game da samar da kudade don...
    Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya. Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya.   Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta...
      Daga nan sai kakakin ya ce, “Ba zai yiwu bangaren Amurka ya nemi tattaunawa a bangare guda, alhali a daya hannun yana barazanar kaddamar da sabbin takunkumai kan kasar Sin ba. Wannan ba ita ce hanya mai dacewa ta gudanar da cudanya da Sin ba.” (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin...
    Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama...
    A zaman na ranar Talata, lauyan masu shigar da kara, Salisu Muhammad-Tahir, ya shaida wa kotun cewa biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Abubakar da Odlyne, ba a samu gabatar da su a gaban mai sharia ba duk da kokarin tilasta musu halartar zaman.   Muhammad-Tahir ya ce “Mun yi iya bakin kokarinmu don tabbatar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025 Labarai An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa October 14, 2025 Manyan Labarai Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar...
    Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.” A cikin wani sako a shafinsa...
    Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa ɗaruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi.   Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazaɓar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare...
    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai yi shawara game da yiwuwar amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin masalaha a yankin Gabas ta Tsakiya. Trump ya ce zai yi aiki tare da sauran kasashen duniya game da wannan batun. Ya bayyana hakan ne ga ga manema labarai a kan hanyarsa ta komawa Amurka daga...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad ta yi maraba da sako Falasdinawa kusan 2000 daga gidajen yarin Isra’ila, tare da cewa jarumtakar mayakan gwagwarmaya da hadin kan al’ummar Falasdinu ne ya haifar da wannan babbar nasara. A cikin wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ziyad al-Nakhalah ya fitar ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar tsagaita bude...
    Shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ya rusa majalisar dokoki ta ƙasar a yayin da rikicin soja ke ƙara ƙamari tare da neman hambarar da gwamnatinsa. A ranar Talata ya sanar da rushe majalisar Dokoki ta Ƙasar, a daidai lokacin da ake fama da tarzomar soja da ta tilasta masa tserewa daga ƙasar. A cewar wata sanarwa...
    Majalisar Wakilai ta gayyaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da bankunan kasuwanci domin amsa tambayoyi kan yadda suke cirar cajin kudade barkatai daga asusun masu ajiya. Majalisar ta gayyace su ne bayan kudurin da Honorabul Tolani Shagaya ya gabatar kan abin da ta kira ‘cirar cajin kudade barkatai babu bayani ba,’ da bankuna suke yi daga...
    Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar...
    ’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar...
    SP Shiisu ya ce bincike na ci gaba domin gano musabbabin ɓarkewar rikicin. Ya kuma yi kira ga jama’a da su ƙara haɗa kai da jami’an tsaro da kuma gaggawar bayar da rahoto idan suka lura da wani abin da zai iya janyo rikici, domin kauce wa zubar da jini. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan...
    Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki. Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya yi gargaɗin cewa dogaro da soja kaɗai, ba tare da inganta rayuwar jama’a ba, zai ƙara haifar da rikice-rikice. Ya ƙara da cewa ingantacce  tsaro na ƙasa yana farawa ne idan gwamnati ta ƙirƙiro damarmakin samun aiki da kuma mayar da amincin jama’a ga gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan...
    Allah Ya yi wa Shugaban hukumar Zavbe ta Jihar Yobe (SIEC) Dakta Mamman Mohammed rasuwa sakamakon gajeriyar jinya. Marigayi Dokta Mohammed, likita ne kuma ƙwararren ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jihar Yobe da ke Damaturu a ranar Litinin. Za a yi Sallar Jana’izarsa a yau talata 14 ga Oktoba, 2025, a...
    Shugabannin kasashen Amurka, Masar,Katar da Turkiya da su ka halarci taron na “ Herm-Sheikh” a kasar Masar sun sanya hannu akan yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza. A jiya Litinin ne dai aka bude taron na Kasar Masar, wanda kuma ya sami halartar Fira ministan kasar Pakistan da kuma shugaban kasar Faransa.  Da yake gabaatar...
    Mai bai wa shugaban kasar Iran  shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa. Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a...
    “Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari...
    Rahotanni sun bayyana cewa wani ƙazamin faɗa ya barke tsakanin wata ƙabilar Palasɗinawa masu ɗauke da makamai da ƙungiyar Hamas a yankin zirin Gaza bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila. A ranar Litinin da aka fara musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila ne rahotanni suka ɓulla game da faɗan da ya ɓarke tsakanin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba.   Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA...
    Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye. Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na...
    Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today...
      Dangane da gamsuwa kan nasarorin da Sin ta samu a bangaren raya harkokin mata, kaso 72.8 na masu bayar da amsa a nazarin daga kasashe maso tasowa, sun yaba da kokarin Sin na horar da mata sana’o’i da tallafawa raya harkokin da suka shafe su. Game da nasarorin da aka samu a kasar Sin...
      A matsayin birnin dake karbar bakuncin taron, Dunhuang mazauni ne ga wurare 3 dake cikin jerin wuraren gargajiya na hukumar UNESCO da kuma wuraren kayayyakin gargajiya sama da 260, wanda kuma ke nuna hadaddun dabarun da aka dauka a shekarun baya-bayan nan da nufin kare al’adun gargajiya yayin da ake bunkasa birnin. (Fa’iza Mustapha)...
    Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana...
      Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin...