Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000
Published: 28th, August 2025 GMT
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta sanar da ƙarin kuɗin yin Fasfo, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa wannan sabon tsari zai shafi aikace-aikacen da ake yi ne kawai a cikin Nijeriya.
Sabon tsarin ya ƙayyade kuɗin fasfo na shafuka 32 mai ingancin shekaru biyar a kan N100,000, yayin da na shafuka 64 mai ingancin shekaru goma zai kasance N200,000. Sai dai an bayyana cewa kuɗin da ake biya ga ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba su sauya ba, inda ake cajin $150 ga shafuka 32 da $230 ga shafuka 64.
Hukumar ta ce wannan mataki na da nufin kare inganci da sahihancin Fasfon Nijeriya tare da tabbatar da cewa ƴan ƙasa suna ci gaba da samun damar amfani da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Umara Zulum ya sanar da fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba a wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa, wannan matakin wani ɓangare ne na babbar ajanda na bunƙasa masana’antu da kuma kawar da dogaro da jihar kan yi na kason da gwamnatin tarayya ke bayarwa duk wata.
Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a EkitiZulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rangadin duba masana’antar robobi ta Borno da ke cikin yankin masana’antu na Maiduguri.
“Ina farin cikin lura cewa mutanen Jihar Borno ba za su sake sayen kayan robobi daga wasu wurare ba, kun ga an sayar da kayayyakin ga ƙasashen maƙwabta da sauran jihohi a cikin Najeriya.”
“Za mu zuba jari sosai a masana’antunmu, don haka nan gaba kaɗan, gwamnatin Jihar Borno ba za ta sake dogara da asusun tarayya ba don ayyukanta na yau da kullum,” in ji Zulum.
Gwamnan ya bayyana cewa masana’antar ta fara fitar da kayayyakinta ga ƙasashen waje, tare da jigilar kayayyakin filastik da aka gama zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Chadi da Jamhuriyar Kamaru.
Zulum ya lura cewa an fara gina cibiyar ne a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Kashim Shettima, amma an farfaɗo da ita a matsayin wani ɓangare na shirin murmurewa da ci gaban gwamnatinsa.