Dangote ya ƙulla yarjejeniyar gina kamfanin taki na dala biliyan 2.5 a Habasha
Published: 29th, August 2025 GMT
Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5.
Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis.
Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya.
Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar da tan miliyan uku na takin zamani a kowace shekara.
“Wannan aikin zai samar da ayyukan yi ga ’yan ƙasa, ya tabbatar da wadatar takin zamani ga manomanmu da suka daɗe suna fama da ƙalubale.
“Sannan zai zama mataki na musamman a yunƙurinmu na cin gashin kai wajen samar da abinci,” in ji Abiy.
A watan Yuni, Aliko Dangote ya shaida cewa nahiyar Afirka za ta iya zama mai isar wa kanta da takin zamani cikin shekaru 40 bisa tsarin faɗaɗa masana’antarsa ta dala biliyan 2.5 da ke Legas.
A halin yanzu dai, Afirka na shigo da fiye da tan miliyan shida na takin zamani a kowace shekara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara
A ƙalla fasinjoji 17 ne suka rasa rayukansu bayan wata motar haya ta faɗa cikin wata gada da ta ruguje a kan titin Gwalli da ke ƙaramar hukumar Gummi, jihar Zamfara.
A cewar hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zamfara, hatsarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da motar ɗauke da kaya da fasinjoji ta faɗa cikin gadar da ta ruguje. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SRC Isah Aliyu, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Kwamandan FRSC na jihar, CC Aliyu Magaji, wanda ya ziyarci wurin hatsarin, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa da asarar rayukan, inda mafi yawansu mata ne. Ya ce hatsarin ya biyo bayan nauyin da aka ɗora wa motar fiye da ƙima da kuma tafiya da daddare.
Hukumar ta gode wa mazauna yankin da suka gaggauta taimakawa wajen ceto wasu daga cikin waɗanda hatsarin ya rutsa da su. Kwamanda Aliyu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Zamfara da al’ummar Gummi, tare da yin kira ga direbobi su rika bin ƙa’idojin hanya da kuma guje wa tuƙa mota da dare domin kare rayuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp