’Yan bindigar da suka sace ma’aurata a Katsina na neman N600m
Published: 28th, August 2025 GMT
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa.
Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda.
Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shiAn sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata.
A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su.
Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kira ɗan uwan Halimat, Malam Ibrahim, ta wayar Anas domin neman kudin fansa Naira Miliyan 600.
Sai dai iyalan sun bayyana cewa ba za su iya biyan wannan kuɗi ba.
Radda ya dawo daga hutu saboda hare-haren ’yan bindiga a KatsinaGwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya dawo daga hutun jinyar da yake yi a ƙasashen waje, sakamakon sabbin hare-haren ’yan bindiga a jihar.
A ranar Laraba, gwamnan ya kai ziyara ta’aziyya ƙauyen Gidan Mantau, a Karamar Hukumar Malumfashi, inda ’yan bindiga suka kashe masallata a wani masallaci a ranar 19 ga watan Agusta.
Shaidu sun ce harin ya auku ne a lokacin da jama’a ke yin sallar Asuba.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya, bayan da mutanen yankin suka yi musu kwanton-ɓauna, tare da kashe mutanensu sannan suka ƙwace musu makamai da babura.
Hakazalika, an ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙone sama da mutum 20 a gidajensu lokacin da suka sake kai hari Gidan Adamu Mantau, a Unguwar Yar Mai Dabo, Makera da kuma Burdigau.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hare hare Ma aurata Radda yan bindigar
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.