Kwamitn Tsaron MDD ya amince da bullar yunwa a zirin Gaza
Published: 28th, August 2025 GMT
Dukkan mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, in ban da Amurka, sun goyi bayan ayyana bullar yunwa mafi muni a yankin zirin Gaza ta hanyar rahoton kungiyar Integrated Food Security Phase Classification (IPC), wata kungiya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.
Kasashe 14 da daga cikin 15 da suka amince da hakan, sun ba da tabbaci a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka yi bayan taron da suka yi a wanann Laraba, kasa da mako guda bayan da hukumar ta IPC ta fitar da wani rahoto mai tayar da hankali game da halin da ake ciki na yunwa a zirin Gaza da kewaye.
Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar daga baya ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila take kaddamar da yakin kisan kare dangi tun daga watan Oktoba na 2023 a Gaza.
Yakin ya kashe Falasdinawa kusan 62,900, ko dai ta hanyar wuce gona da iri ko kuma amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, inda Isra’ila ta hana shigar da duk mahimman kayan abinci cikin yankin Zirin Gaza.
Har ila yau, ta haifar da yanayin da ke tilastawa ‘yan Gaza da ke fama da yunwa yin tururuwa a kusa da wuraren rarraba abinci, inda kuma sojojin Isra’ila ke bude musu wuta da gangan.
Kasashen sun amince da sanarwar IPC da ta shelanta yunwa a Gaza a matsayin abin da aka haddasa da gangan, wanda kuma bisa dokokin kasa da kasa wannan yana a matsayin laifin yaki ne.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wata babbar tawagar jami’an tsaron Sudan ta ziyarci Somaliya August 28, 2025 E3 za su gabatar da bukatar dawo da takunkuman MDD a kan Iran: Reuters August 28, 2025 Shugaban Rwanda ya musunta zargin sojojin kasarsa da hannu a rikicin Congo August 28, 2025 ASUU: Gwamnatin Najeriya ba ta aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba August 28, 2025 Iran da Rasha Sun Zasu Hadakai A fagen Watsa Labarai August 27, 2025 IRGC Sun Halaka Yan Ta’adda 13 A Yankin Sistan Baluchestan August 27, 2025 Zanga-Zanga Ta hana Wakilin Amurka Ziyara A Kudancin Lebanon August 27, 2025 Hamas: Isra’ila Tana Rike Da Gawawwakin Falasdinawa 726 August 27, 2025 Isra’ila Ta kashe Falasdinawa Fiye da 1000 A Yamma Da Kogin Jordan August 27, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za Su Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda August 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye.
A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran dangane da goyon bayan da suke bawa Falasdinawa a gwagwarmayansu da HKI.
Dangane da shawarorin da aka gabatar a taron OIC, Iran tana godiya kasashen musulmi da wadanda ba musulmi kan shawarorin da suka gabatar, don warware rikicin Falasdinawa, daga ciki har da “New York Declaration” ta samar da kasashe 2. Da wasu da dama. Amma JMI tana ganin kafa kasashe biyu bazai warware rikicin ba. Tana ganin gudanar da zaben raba gardama, a kasar wanda zai hada da dukkan falasnawa a ko ina suke a ciki da wajen kasar, don zabawa kansu tsari dairin gwamnati da suke su ta demucradiyya. Irab tana ganin samar da kasar Falasdinu a dukkan fadinkasar wacce take da dukkan birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar ita ce mafita. Yahudawan da suke son zama su zauna wadanda suke son tafiya su koma kasarsu ta asalali.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci