2025-06-15@09:59:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 42

«yahudawan Sahyoniyya»:

    Da yake tuna tarihin siyasarsa a matsayin daya daga cikin gwamnonin adawa a farkon shekarun 2000, Tinubu ya sake jaddada matsayinsa a matsayin mai kare dimokradiyyar jam’iyyun adawa.   Ya kuma mika godiyarsa ga magabacinsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa yadda ya fahimci tare da gyara abin da ya bayyana a matsayin “kuskuren zaben 1993,” wanda aka yi imani da cewa, Cif Moshood Abiola da Alhaji Babagana Kingibe ne suka lashe amma gwamnatin soja ta soke zaben. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Myanmar Min Aung Hlaing, sun mikawa juna sakon murnar cika shekaru 75, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 75 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar, bangarorin biyu sun bi ka’idoji 5 na zama tare cikin lumana, da kuma tunanin Bandung, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwar samun moriyar juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, sun kuma kasance abun koyi a fannin sada zumunta tsakanin kasa da kasa. Ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da Myanmar, don gaggauta raya hadin gwiwa mai...
    Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.   Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...
    Miliyoyin alhazai ciki har da ’yan Najeriya ne suka taru a Dutsen Arfa domin tsayuwa a yayin Aikin Hajjin bana duk da tsananin zafin ranar da ake fama da shi a kasar Saudiyya. Ministan Aikin Hajji na kasar dai ya shawarci mahajjatan da su kasance a cikin tantinansu tun daga tsakain karfe 10 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, saboda tsananin zafin rana. Ko a ranar Lahadi sai da Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasar (NCM) ta yi gargadin cewa zafin zai iya kai wa ma’auni 47, inda ta shawarce su da su dauki matakan kariya. Musulman Kudancin Kaduna sun yi taron addu’ar zaman lafiya Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano To...
    Yau Alhamis 9 ga watan Zul Hijja, ita ce ranar da miliyoyin Musulmi da ke aikin Hajji a kasar Saudiyya ke hawan Arfa, wato daya daga cikin shika- shikan aikin Hajji. Maniyyata kusan miliyan biyu daga fadin duniya ne ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin, wanda ya kunshi dawafi da zaman Mina da tsayuwar ta Arfa da kuma jifar shaidan. A washegarin ranar ne kuma sauran Musulmai a duk fadin duniya su ke shagulgulan Sallar layya. Hukumar lura da aikin hajji ta Saudiyya ta ce yanayin zafi zai kai maki 45 a kwanakin da ake tsaka da aikin na hajji.
    Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
    Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin Falasdinawan na shirin yin amfani da ziyarar ne wajen farfado da kiran samar da kasar Falasdinawa. Wani jami’in Isra’ila ya shaidawa tashar talabijin ta CNN a ranar Juma’a cewa gwamnatin sahyoniyawan ba za ta hada kai da hukumar Falasdinu ta PA ba da ke neman karbar bakuncin tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya. Jami’in ya bayyana ziyarar a matsayin tsokana, yana mai...
    Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen. Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen cewa: Kariyar tsaron sararin samaniyar sojojin Yemen za ta mayar da jirgin saman makiya ‘yan sahayoniyya abin izgili a cikin kwanaki masu zuwa. Al-Mashat ya jaddada cewa: Sojojin kasar Yemen za su iya tunkarar jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya ba tare da haifar da wata illa ga...
    Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da yin kutse cikin Masallacin Al-Aqsa, yayin da kungiyar Hamas ta yi kira da a kalubalance su Daruruwan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a safiyar yau Alhamis suka kutsa cikin harabar Masallacin Al-Aqsa, karkashin kariyar da ‘yan sandan gwamnatin mamayar Isra’ila, yayin da ake ci gaba da kiraye-kirayen gudanar da taron gangami da kuma jaddada rashin amincewa da keta hurumin alkiblar musulmi na farko, kuma daya daga cikin Masallatai masu daraja na al’ummar musulmin duniya.  Majiyoyin daga Qudus sun ba da rahoton cewa: Tsagerun yahudawan sahayoniyya mazauna matsugunai da dama sun gudanar da rangadi masu tayar da hankali a harabar Masallacin Al-Aqsa mai albarka, ciki har da gudanar da ibadar Talmud da raye-rayen neman tsokana.
    Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya  masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa. Birnin Qudus ta gabas dai nan ne masallacin Al-aksa yake, kuma nan ne Falasdinawa suke da dama. Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
    An dai haifi Dakta Mubarak a Unguwar Hausawa Masallacin Murtala, da ke Karamar Jukumar Kumbotso ta Jihar Kano a Nijeriya. Ya yi karatun Firamare a Hausawa Model ta Jihar Kano; ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya ta jeka ka dawo a Kano; daga nan ya tafi zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudi, inda a nan ne ya samu digiri na farko. Ya samu digiri na biyu a fannin noma da gandun daji; sannan ya samu digirin-digirgir kan Agro Paris Tech, Paris, a Kasar Faransa, ya sake yin karatun digiri na biyu a fannin sanin yanayi, Amfanin Kasa da Ayyuka na Muhalli; ya kuma samu digirin-digirgir a Jami’ar Paris a fannin Ecology. Ya yi aiki a...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
    Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa. Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038. An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana. Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025. An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
    Mahajjata hudu – daya daga Maroko sauran kuma daga Sifaniya – sun isa kasar Saudiyya a kan dawakai a wannan makon da ya fice don gudanar da aikin Hajjin 2025, wanda hakan ke tunatar da al’ummar Musulumi tsarin zuwa aikin hajji a shekaru da dama da suka gabata. Mahajjatan sun isa zuwa kasar Saudiyya ne ta kan iyakar Al Hadithah da ke Al Qurayyat, inda jami’an gwamnati suka tarbe su tare da duba lafiyarsu, da kuma basu abubuwan sha don jinjin irin tafiyar da suka yi ta tsawon makonni. Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe Nijeriya Ta Yi Asarar Naira Biliyan 118 Sakamakon Barnatar Da Iskar Gas A Watanni 2 Hotunan yadda suka...
    Hukumar jin daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta miƙawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON kuɗi sama da Naira biliyan 6 a matsayin kuɗin jigilar maniyyatan jihar na 2025 na zuwa Saudiyya. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Labbo a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse, ya ce hukumar ta raba tare da sayar da kason kujerun aikin Hajji sama da 1,000 na jihar ga ƙananan hukumomi 27 ga mahajjata. Sojoji sun kama jami’an tsaro da ke haɗa baki da ’yan ta’adda ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe  Umar Labbo ya bayyana cewa, hukumar ta kammala shirye-shiryenta da suka haɗa da biza ga maniyyatan jihar, inda a yanzu...
    Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    “Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi. El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC. Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba. “Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar  nauyi ne da ya rataya a wuyan  hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
    Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta bullo da tsarin da kowanne maniyyaci zai san masaukinsa a kasa mai tsarki tun daga nan gida najeriya. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shalkwatar hukumar dake Dutse. Yana mai cewar, wannan shi ne karon farko da hukumar ta bullo da tsarin domin maniyyaci ya san masaukinsa a nan gida kafin zuwa kasa mai tsarki. Game da batun kudade kuwa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma kaddamar da kwamitin canjin kudaden guzuri na maniyyata domin samun saukin canji yayin aikin Hajjin. Ya ce an kafa kwamitin ne domin  bibiyar maniyyata kan canjin kudin guzuri, kasancewar wasu batagari na...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis. A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya taimakawa juna. Imam Khamenei ya yi nuni da cewa, akwai makiya da suke adawa da fadada alaka a tsakanin kasashenmu biyu, kuma wajibi ne a shawo kan wadannan munanan manufofin, kuma a shirye Iran take ta yi hakan. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ci...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya. Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027. Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi. “Mutanen Arewa suna da wayewar...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    Hukumar kula da agaji ta MDD (OCHA) ta bada sanarwan cewa, gwamnatin HKI a yankin yamma da kogin Jordan ta kori Falasdinawa a gidaje 5 a yankin bayan sun rusa gidajensu. Hukumar ta kara da cewa wadanda HKI ta rusa gidajensu a yankin sun hada da yara 19 da da iyayensu 33 maza da mata 6. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto OCHA na cewa tun watan Maris da ya gabata zuwa yanzu, HKI ta rusa gidaje da gine-ginen Fafalsadinawa kimani 100 a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da gabacin birnin Qudus da kuma sauran yankuna, da sunan an gina gidajen ba bisa ka’ida ba. Banda haka suna kwace gonakin Falasdinawa don ginawa sabin...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar ta Shuja’iyya.Dama tun da safiyar Laraba wasu Falasdinawan 50 sun yi shahada a wannan unguwa ta Shuja’iyya dake cikin birnin Gaza. Wasu majiyoyin Falasdinawa sun ambaci cewa: Sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi a kusa da masallacin; UMMU HaBIBAH, da kuma kasuwar sayar da kekune a yankin Qaizan a kudancin Khan-Yunus. A gefe daya,majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa; Da akwai Falasdinawa miliyan...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da  tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan  kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami horo da ilimi kan yadda ake aiwatar da aikin Hajji domin dacewa wannan ibada da suka kashe makudan kudade don gannin sun aiwatar da ita. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, za a wayar da kan alhazai da kuma koya musu yadda za su kula da kansu da kuma yadda za su aiwatar da aikin Hajji bisa ga koyarwar addini. Ya ce, ana gudanar da...
    Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46 a duniya, ta aika sako cikin shafinta na yanar gizo inda take goyon bayan kungiyoyin Hamas da Hizbullah na kasar Lebanon sannan tana allawadai da kuma aibata HKI kan kissan yara da take yi a Gaza.   Gwamnatin kasar Amurka dai tana ganin kanta a matsayin kasa wacce take gaba wajen kare hakkin fadin albarkacin baki, amma idan al-amarin ya shafi HKI sai ta nuna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
    Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino. Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda...
    Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari. An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain. A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya. A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
    Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan.   Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.   Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya.   Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama.   Babban bako na musamman ya jaddada...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane  300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
۱