Ana Zargin Jami’in Sibil Difens Da Harbe Abokin Aikinsa A Abuja
Published: 9th, September 2025 GMT
Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel, mai shekaru 45, sun ce suna zargin abokin aikinsa ne ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi a wani otel da ke Abuja.
Matar marigayin ta ce alamu sun nuna an kashe mijinta ne, saboda an samu raunukan harbin bindiga a kafaɗunsa.
Gini Ya Rushe A Jigawa, Mutum 1 Ya Rasu, 7 Sun Jikkata Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A DuniyaTa kuma bayyana cewa an ba su labarai daban-daban uku kan yadda aka ce mijinta ya mutu, lamarin da ya sa suke zargin ana ƙoƙarin rufe gaskiyar abin da ya faru.
Kakakin rundunar ’yansandan birnin tarayya, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.