2025-10-15@14:48:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 105

«Muharram shi»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin yaki na ” Drone” ya cilla kan wata mota a kan titi a garin Jarjoun da Iqlim Attuffah inda suka kashe mutane 3 sannan wasu kusa da motar guda 4 sun ji rauni. Majiyar yahudawan ta bayyana cewa sun kashe wani kwamandan kungiyar Hizbullah ne, amma shaidu a yankin sun tabbatar da cewa duk wadanda HKI ta kashe ba mayakan kungiyar Hizbullah ne ba. Wannan...
      Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi.     Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin.     Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta.  ...
    Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026. Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan...
    Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci...