Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwata Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Zirin Gaza
Published: 7th, September 2025 GMT
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada suna da yawa a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza a jiya Asabar
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da gwabza kazamin yakin da take yi a zirin Gaza a rana ta 701, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkatan wasu, da suke cikin masifar yunwa da kuma tilastawa Falasdinawa sama da miliyan biyu gudun hijira, a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru da kuma ci gaba da goyon bayan Amurka.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka auka wa unguwanni da dama da makamai masu linzami, inda suka kashe Falasdinawa 58 tun daga wayewar garin jiya kadai, ciki har da mata da kananan yara.
Asibitin Hamad ya ba da rahoton shahadan Falasdinawa 10 tare da jikkatan wasu sama da 70, yawancinsu masu neman agaji saboda da yunwa a arewacin zirin Gaza.
Unguwar Sheikh Radwan da titin Al-Jala’a a cikin birnin Gaza an sha fama da hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin Isra’ila da jirage masu saukar ungulu suka yi, baya ga harin bama-bamai da aka kai kan wasu gine-ginen zama a gabashin tafkin Sheikh Radwan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Tunusiya Ya Jaddada Bukatar Raya Nahiyar Afirka Ta Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikinta September 7, 2025 An Kaddamar da kungiyar tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka September 6, 2025 Araghchi ya Tattauna da takwarorinsa na kasashen Girka da Slovenia da Saliyo September 6, 2025 Gaza : Adadin Wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila cikin sa’o’I 24 ya karu September 6, 2025 Kungiyoyin gwagwarmaya sun fusata da barazanar Isra’ila na bude “kofofin jahannama” a Gaza September 6, 2025 Iran ta aike da kayayyakin jin kai tan 100 zuwa Afghanistan September 6, 2025 Ammar Hakeem ya gana da larijani a nan birnin Tehran . September 6, 2025 HKI Ta Kashe Falasdinawa 50 A Harin Da Takai A Yankin Gaza September 6, 2025 An yi Kira Ga El-rufai Da Ya yi Hattara Da Kalamansa September 6, 2025 An Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Shirin Amurka Na Kwace makaman Hizbullah. September 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji.
“Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza.
Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.”
Sanarwar ta karyata ikirarin CENTCOM cewa “kusan kasashe 40 da kungiyoyin kasa da kasa suna aiki a Gaza,” yana mai jaddada cewa ainihin adadin kungiyoyin da ke ba da agajin jin kai bai wuce 22 ba, “yawancinsu suna fama da cikas da kuntatawa saboda matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanya.”
Haka kuma ta soki shiru da CENTCOM ta yi game da laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi a kullum tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.
“Shirun da rundunar sojin Amurka ta yi a gaban wadannan laifukan na yau da kullum, yayin da take aiki don yada labaran da ba su da tushe game da rundunar ‘yan sandan Falasdinu, ya nuna cikakken son kai ga mamayar Isra’ila da kuma rashin sahihancinta a matsayin wacce ya kamata ta kasance mai shiga tsakani,” in ji sanarwar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci