2025-09-18@05:31:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 109
«bayyana cewar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa hukumomin tsaro na kara ɗaukar matakan daƙile matsalar a Kauru, Kachia da sauran yankunan da abin ya shafa. Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi Ya gargaɗi duk masu bai wa ’yan ta’adda mafaka ko goyon baya da su daina, domin hukuma za ta ɗauki matakin ladabtar da su. Sanatan...
Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar. An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa. Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shiga Tattaunawa Karkashin Matsin Lamba
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da...
Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar. A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a wannan cibiyar. Cibiyar da aka sabunta za ta ƙunshi abubuwan more rayuwa na zamani, waɗanda suka haɗa da dakunan kwanan dalibai, asibiti, wurin shakatawa, wuraren aikin kafinta da walda, ɗakin cin abinci. Kwamishina Amina ta yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano. Ana sa ran kammala aikin gyaran nan ba da jimawa ba, daga nan...
Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17. Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba. Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci. Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar. Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye. Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali,...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56. Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949). Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960). Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021). Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.” Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba. Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.” Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya...
Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...