Leadership News Hausa:
2025-09-18@05:29:04 GMT

Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai

Published: 8th, March 2025 GMT

Barkewar Cutar Lassa: Masana Sun Bayyana Hanyoyin Kare Kai

Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC

Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar.

A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar mutane akalla sama da 1,000.

Haka nan kuma, a shekarar 2018 an sake samun bullar cutar a kasar, inda mutane sama da 1,500 suka kamu da cutar, sannan adadin wadanda suka kamun sun doshi kashi 20 cikin 100.

Kwana-kwanan ne, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin fadin jihohi 11 cikin mako shida daga 3 zuwa 9 ga watan Fabrairun 2025, bayan barkewar cutar a 2024, da sama da mutum 4,726 da suka kamu da cutar, inda dama daga cikinsu suka mutu.

Har wa yau, a rahotonta na baya-bayan nan, game da cutar zazzabin Lassa, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar da sun kamu da cutar a jihohi 11 da suka hada da; Ondo, Taraba, Edo, Benuwe, Gombe, Kogi da kuma Ebonyi, inda ta ce; adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da kashi 19.4 cikin 100, daga kashi 17.5 cikin 100, duk dai a cikin shekarar 2024.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, kashi 73 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, sun fito ne daga Jihohin Ondo, Edo da Bauchi, in Ondo ke kan gaba da kashi 34 cikin 100, sai Edo da kashi 21 cikin 100, Bauchi kuma da kashi 18 cikin 100, inda ta bayyana cewa; adadin adadin kananan hukumomi 63 da ke cikin jihohi 11, sun tabbatar da kamuwa da cutar.

Har ila yau, NCDC ta kara da cewa, ba a samu rahoton ko mutum guda cikin ma’aikatan lafiya da ya kamu da cutar a cikin wannan makon ba. Kazalika, jinkirin gabatar da kararraki, ya taimaka wajen karuwar mace-macen da tsadar kudin magani da kuma karancin wayar da kan al’umma.

 

Matakan Da Aka Dauka

Domin magance barkewar cutar, NCDC ta ce; ta farfado da sakatariyar da ke kula da tsarurrukan da suka shafi wannan cuta ta zazzabin Lassa ta kasa (IMS), domin samun daidaito a ayyukan.

Ta kara da cewa, ta yi hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Cibiyar Bincike ta Kasa da Kasa da wasu Cibiyoyin, don bunkasa hanyoyin gane cutar da kuma magance ta ba tare da wani bata lokaci ba.

Sannan, hukumar ta bukaci ‘yan Nijeriya da su dauki matakan kare kawunansu da suka hada da kula da tsafta, gujewa cudanya da berayen da ke dauke da cutar da kuma neman magani da wuri da zarar an ji alamu kamar na zazzabi, ciwon makogwaro da kuma zubar da jini babu gaira babu dalili.

Hukumar ta NCDC, ta kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan wajen kamuwa da cutar, musamman ta hanyar adana abincin da aka rufe a cikin kwantena yadda ya kamata, don hana bera shiga. Kazalika, ta karfafi ‘yan Nijeriyan da su rika sanar da su tare kuma da daukar matakan kare kawunansu da sauran ‘yan’uwansu.

Hanyoyin Da Za A Bi Don Kare Kai

A wata hira ta musamman da aka yi da jaridar Blueprint, wani Farfesa a fannin cututtuka masu yaduwa da kwayoyin halitta a sashen nazarin halittu na Jami’ar Adeleke, Oladipo Kolawole ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya su inganta tsarin sa ido, domin ganowa da kuma bayar da rahoton bullar wannan cuta ta zazzabin Lassa.

Ya ce, kamata ya yi a tabbatar an samu wadataccen sinadarin ‘ribabirin’, wanda shi ne maganin cutar zazzabin Lassan na farko, wanda hakan zai karfafa tare da taimakawa wajen warkar da masu dauke da cutar.

A cewar Farfesa Kolawole, gwamnatin tarayya karkashin Hukumar NCDC, na taka muhimmiyar rawa wajen daidaitawa tare da sa ido da ganowa da kuma mayar da martani a dukkanin fadin wannan kasa.

Ya kuma jaddada cewa, don gujewa barkewar zazzabin Lassa, ‘yan kasar za su iya daukar matakan kariya da dama, kamar gujewa cudanya da beraye, adana abinci da sarrafa shi yadda ya kamata, kasancewa cikin tsafta, gujewa cudanya da wadanda suka kamu da cutar da kuma wayar wa jama’a kai a koda-yaushe, domin kai kawunansu asibiti da wuri.

Kazalika, don rage barkewar cutar zazzabin Lassa a jihohi kamar su Edo, Ebonyi, Ondo da kuma Bauchi, Farfesan ya bayyana cewa, za a iya daukar matakai da dama da suka hada da karfafa tsarin sa ido da shigo da al’umma ciki, domin samun hadin kai da kuma kokarin daukar matakan kariya.

 

Wadane Matakai Ya Dace Gwamnati Ta Dauka

Wani likita mazaunin Birtaniya, a makarantar Chebening, wanda kuma ya kafa gidauniyar kiwon lafiya ta yara, Dakta Christian Inya Oko, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kara zuba kudade tare da aiwatar da tsare-tsaren da za su taimaka wajen shawo kan wannan cuta ta zazzabin Lassa yadda ya kamata. Ya ce, ya rasa abokansa likitoci da dama sanadiyyar wannan cuta, baya ga sauran ‘yan Nijeriya da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce, “Bayan mutuwar abokaina likitoci uku tare da wasu ‘yan Nijeriya sama da 800 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, na kadu matuka da jin rahoton NCDC na baya-bayan nan. A rahoton shekara ta 2024, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta bayar da rahoton kusan mutum 1300 da aka tabbatar da sun kamu da cutar, kashi 16.3 cikin 100 na mace-mace, wato mutum 214 da suka mutu a jihohi 28.

Jihohin Edo, Ondo da Bauchi ne ke kan gaba a jerin sunayen, yayin da Taraba, Ebonyi, Enugu da Filato, su ma suka bayar da rahotanni marasa dadi. A cikin mako na shida na 2025, an samu mutuwar mutum 80 cikin mutum 413 da suka kamu da cutar a jihohi 28 tare da karin mutuwar mutum 10 a cikin wannan makon.

“Idan aka yi la’akari da wannan kididdigar, akwai bukatar kara ingancin matakan da ake amfani da su wajen kokarin dakile wannan cuta ta zazzabin Lassa. Zazzabin Lassa, wani muhimmin al’amari ne da ya shafi lafiyar al’umma a Nijeriya da ake fama da shi”, in ji shi.

Dakta Oko ya yi nuni da cewa, ya kamata a samar da hanyoyin horar da ma’aikatan kiwon lafiya a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da na sauran manyan makarantu, don ganowa da magancewa da kuma kaucewa ire-iren wadannan kwayoyin cututtuka. Marasa lafiyan da aka gano suna dauke da cutar, ya kamata a ba su kulawa ta musamman, ta hanyar ba su magunguna da sauran abubuwan da suka dace, har sai sun warke.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: wannan cuta ta zazzabin Lassa da suka kamu da cutar cutar zazzabin Lassa sun kamu da cutar bayar da rahoton kamu da cutar A kamu da cutar a da aka tabbatar barkewar cutar mutuwar mutum yan Nijeriya bayyana cewa Nijeriya da

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya ta bayyana sabbin mutanen da suka mutu sakamakon harin Suweida

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Siriya (SOHR) ta bayyana wasu sabbin fararen hula tara da aka ci zarafinsu a lokacin abubuwan da suka faru a Suweida a watan Yulin da ya gabata.

Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta bayyana cewa, wadanda aka kashen da suka hada da mata biyu, an kashe su ne a filin wasa a lokacin da wasu ma’aikatun tsaro da na cikin gida na gwamnatin rikon kwarya suke lardin na Suweida, tare da halartar mayakan ‘yan kabilar Larabawan Bedouin.

Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta ce adadin mutanen da suka mutu a watan Yulin da ya gabata a tsakanin al’ummar Druze a Suweida ya kai 1,592, yayin da adadin wadanda suka mutu tun safiyar Lahadi 13 ga watan Yuli, sakamakon arangama, da kisa a fili, da kuma harin bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai ya kai 2,047.

Hukumar da ke sa ido kan lamarin ta yi bayanin cewa, “a ci gaba da bincike, akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu, ganin cewa akwai wadanda suka bace daga irin wadannan abubuwan da har yanzu ba a tantance makomarsu ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A  HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta