Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja
Published: 7th, March 2025 GMT
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon fashewar wata tankar mai da ta tashi a Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata filayen noma a cikin unguwanni.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƙaramin Rami da ke ƙaramar hukumar Mashegu da misalin ƙarfe 6:30 na yamma.
Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya afku ne lokacin da wata motar ɗaukar kaya ta yi yunƙurin kaucewa wasu munanan hanyoyi.
Waɗanda fashewar ɗin ta rutsa da su sun haɗa da: Rafiatu Sahabi da Ramlat Shehu da Rashida Abdullahi da Raliya Abdulrahman da Zainab Ahmed, Zuwaira Idrisu da kuma Maryam A. Nura.
Wata mata mai suna Maimuna Isah ta samu raunuka kuma tana karɓar magani a cibiyar kula da lafiya matakin farko na Saho Rami.
Motar tankar dai ta kife ne ta zubar da man cikinta a kan titi, inda man ya kwarara zuwa wani rafi da ke kusa inda manoman rani ke aikin noman shinkafa.
An bayyana cewa man da ya zube ya ci karo da wani famfunan ruwa da manoman ke amfani da su, lamarin da ya sa gobarar da ta koma kan tankar da ta kai ga fashewa.
Gobarar ta mamaye filayen noma ta kuma gurɓata rafin, inda ta ƙona manoma da dama da kuma ƙone gonakin shinkafa da kayan lambu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fashewar tankar mai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026
Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT a cibiyoyin Bwari da kuma duba ɗakin gwajin jarrabawa JAMB a kwamfuta.
Alausa ya bayyana cewa, daga watan Mayu ko Yuni na 2026, duka ɓangarorin tambayoyin da aka saba na WAEC da NECO, na rubutu da na gwaje-gwaje, za su kasance a komfuta gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa wannan matakin na daga cikin manufar gwamnatin na magance matsalar satar jarabawa.
Gwamnatin Kano Ta Biyawa Ɗalibai 119,903 Kudin Jarrabawar NECO Da NBAIS WAEC Ta Kwace Lasisin Makarantu 574 Sakamakon Satar AmsaMinistan ya kuma sanar da cewa an kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Daraktan JAMB, Prof. Ishaq Oloyede, wanda zai duba tsarin jarabawar Nijeriya gaba ɗaya, inda aka ce sakamakon binciken zai fito nan da ƙarshen watan gobe. Alausa ya yaba da ingancin gudanar da jarabawar UTME ta 2025 da JAMB, wanda ya bayyana a matsayin “matsayi na duniya” kuma yana cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
A cikin jawabinsa, Oloyede ya bayyana cewa UTME ta 2025 tana ɗaya daga cikin mafi kyawun jarabawar da aka taɓa gudanarwa, inda ya kuma bayyana cewa duk wani zargin rashin dacewar cibiyoyin jarabawa yana buƙatar hujja mai ƙarfi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp