An yi Gargadi game da karkatar da kayyakin aikin Cibiyar Gyaran Hali Ta Kiru
Published: 7th, February 2025 GMT
Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar.
A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a wannan cibiyar.
Cibiyar da aka sabunta za ta ƙunshi abubuwan more rayuwa na zamani, waɗanda suka haɗa da dakunan kwanan dalibai, asibiti, wurin shakatawa, wuraren aikin kafinta da walda, ɗakin cin abinci.
Kwamishina Amina ta yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Ana sa ran kammala aikin gyaran nan ba da jimawa ba, daga nan ne za a bude cibiyar domin ci gaba da gudanar da ayyukanta.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gyara
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA