Shugaban Majalisar Wakilai Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Shugaban Kamfanin Albabello
Published: 5th, February 2025 GMT
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima.
Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban.
Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma gina makarantun firamare da sakandare da dama don inganta ilimi; da masallatai, domin ci gaban al’umma.
Hakazalika, a yayin rayuwarsa marigayin ya dauki nauyin bayar da tallafin karatu ga dalibai don yin karatu a Najeriya da kasashen waje, da sauransu.
Dr Tajuddeen, ya yi addu’a ga Allah SWT dayYa ji kan marigayi Alhaji Bala Abdulwahab, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure rashin.
Alhaji Bala Abdulwahab, wanda shi ne wanda ya assasa kamfanin Albabello Trading Company Limited da ke Zariya, ya rasu ne a ranar Litinin 3 ga watan Fabrairun 2025, yana da shekaru 68.
Daga Salihu Tsibiri
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Rasuwa Shugaban Majalisar Wakilai
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta bayyana cewa wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ce a filin jirgin sama na Kano ta boye jakunkunan ƙwayoyi a cikin kayan matafiyan.
An kama shugaban ƙungiyar, Ali Abubakar Mohammed (wanda aka fi sani da Bello Karama), tare da wasu abokan aikinsa.
Hukumar ta ce mutanen ukun ba su da laifi kuma an zalunce su ne kawai.
An saki su ne bayan bincike da kuma ƙoƙarin diflomasiyya na tsawon makonni.
Lamarin ya tayar da hankali kan tsaro a filayen jirgin sama a Nijeriya da yadda masu aikata laifuka ke amfani da fasinjoji marasa laifi.
Hukumar ta ce za a ɗauki ƙarin matakai don hana faruwar irin wannan lamari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp