2025-10-27@18:40:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7305

«juyin juya halin musulunci»:

    Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Bayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin. Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin. “Sun...
    A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a babban gidan adana kayan tarihi na “Palace Museum”, albarkacin cika shekaru 100 da kafuwar gidan tarihin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira da a kara babbar azama wajen kare gidan tarihin, a matsayinsa na wuri dake rike da matsayin kyakkyawar ma’adanar wayewar kai ta kasar Sin. Kazalika, a dai yau din, kamfanin dab’i na al’ummar kasar Sin, ya wallafa wani littafi na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mai kunshe da cikakkun bayanai, da fashin baki kan muhimman batutuwa da aka tattaunawa kan tsaron al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce hadin kai tsakanin kasashen Musulmi yana da matukar muhimmanci wajen kare muradunsu da tsaronsu, daga duk wani cin zarafi daga kasashen waje. Mista Pezeshkian ya yi wannan furuci ne a wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Oman Sayyid Hamoud bin Faisal al-Busaidi a Tehran yau Litinin. Da yake nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Oman, wacce ya ce ta kasance bisa girmama juna da kuma kyautatawa. Shugaban ya ce kasashen biyu ko yaushe suna goyon bayan junansu ta hanyar ci gaban yankin. Ya yaba da rawar da Oman ta taka a ci gaban yankin, musamman a fannin sulhu da kuma karbar bakuncin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Iran...
    Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da aikinsa a Fadar Élysée, yayin da kashi 84% suka nuna rashin gamsuwa da shi. Kiyasin farin jinin shugaban bai taba raguwa haka ba. Emmanuel Macron, wanda kwarin gwiwarsa ke ci gaba da durkushewa, yanzu ya ba wa kashi 54% na masu jefa kuri’arsa kunya a zagaye na farko na 2022. Rikice-rikicen da aka samu sakamakon rusa Majalisar Dokoki ta kasa, murabus, sannan sake nada Lecornu...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar.   Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
    Majalisar tsarin mulki a jamhuriyar Kamaru ta sanar da Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wata. Mista Biya ya lashe zaben da kashi 53.66% na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar shugabancin kasar a wa’adin mulki na takwas. Saidai babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi ikirarin lashe zaben, ya samu kashi 35.19% na kuri’un, a cewar alkaluman da aka samu daga cibiyar. Madugun ‘yan adawar ya yi fatali da sakamakon zaben da ya danganta da abin dariya. Rahotanni sun ce tarzoma ta barke a wasu sassan kasar da suka hada da Douala da Garoua bayan sanar da nasarar ta...
    Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.” Ban da haka, ta ce, “Huldar abota tsakanin Afirka da Sin wani misali ne na samun ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar...
    An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban. Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles, a wani ɓangare na shirin kamfanin na kyautata dangantaka da al’umma (CSR). Kamfanin ya tabbatar da bayar da kyaututtuka ga Jaruman Indomie — wani girmamawa na musamman ga matasan da suka nuna jarumta da Ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙasar. Taken bikin na bana shi ne “Jaruman da Ba a San Su ba”, inda fitattun matasa uku daga sassan Najeriya suka fito a matsayin zakaru, bayan sun...
    An naɗa Birgediya Janar Qarshi a matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Pakpour, ya fitar da wata doka da ta nada Birgediya Janar Seyyed Hujjatullah Ghoraishi a matsayin mataimakinsa na harkokin daidaitawa. Birgediya Janar Ghoraishi ya taba yin aiki a matsayin Mataimakin Ministan Tsaro na Farko da Mataimakin Harkokin Shiri da Tallafi a Ma’aikatar Tsaro. An nada Birgediya Janar Mohammad Reza Naqdi, wanda a baya ya yi aiki a matsayin Mataimakin Harkokin Daidaito na IRGC, a matsayin Babban Mai Ba da Shawara ga Babban Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments...
    Kobi ta ce, an samu buƙata daga wajen mutane bakwai, inda aka tantance su domin fafata neman sa’a, daga baya mutane uku suka janye suka bar mutane huɗu domin fafata neman nasara a zaɓen.   “Bayan gudanar da zaɓen, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Rtd) shi ne ya yi nasara.   “Za a gabatar da sakamakon nasarar da ya samu wa gwamnan domin amincewar da gabatar wa Gung-Zaar na farko takardar naɗinsa a matsayin Sarkin masarautar Zaar,” sanarwar ta shaida.   Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Sayawa ke zanga-zangar adawa da yunƙurin gwamnatin jihar Bauchi ta Bala Muhammad wajen naɗa musu wani a matsayin Sarkin masarautar Sayawa wato (Gung Zaar).   Masu zanga-zangar dai sun bayyana...
    Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru ya sake lashe zaɓen Shugaban Ƙasar domin fara wa’adi na takwas na shekara bakwai. Kotun Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta sanar cewa Mista Paul Biya mai shekaru 92 ya samu nasara ne bayan ya samu 53.66 na kuri’un da aka jefa a yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.19. Da haka biya zai ci gaba da mulki inda zai kammala sabon wa’adin yana dan shekara 99. Zuwa ƙarshen wa’adin, Biya wanda ya shekara 43 a gadon mulki tun 1982 zai cika shekara 50 a kan mulki. A halin yanzu shi ne shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya. Shi ne kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyu a tarihin...
    An Kammala bikini bada Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17, An Girmama Matasan da suka nuna hazaka Kuma wadanda suka kasance jakadun Najeriya. Wannan gagarumin biki ɗaya gudana a Lagos, Najeriya, a ranar 16 ga watan Oktoba, 2025: kamfanin Dufil Prima Foods, masu yin Indomie Instant Noodle suka shirya karkashin shirinsu na kyautata alaka da Al’umma na Kamfanin Indomie, sun tabbatar da bada Kyautuka ga Jaruman Indomie, wani mataki na daraja, wadanda suka nuna jarunta bisa ayyukan jarumtaka da sukayi, ta hanyoyi daban daban da suka kunshi kirkire-kirkire na yaran Najeriya. An gudanar da wannan taro a Legas, inda gasar karshe ta wannan shekarar, mai taken “Jaruman da ba a San Su ba” inda fitattun matasa uku ‘yan Najeriya wadanda...
    Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa.   Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar a lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a Ibadan a jihar Oyo a watan gobe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Labarai Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga...
      Kanar Uba ya ce, ‘yan ta’adda sun kutso cikin garin ne ta yankin Flatari sannan suka tsere da raunuka zuwa Dikwa “bayan sun sha ruwan wuta.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano October 26, 2025
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce wasu daga cikin mutanen da saba yabon tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin yake kan mulki, su ne suka fara yi masa ba’a tare da suka bayan ya sauka daga mulki. Da yake jawabi a wani taron “Lakcar Raymond Dokpesi” da Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta shirya a birnin Abuja, Gwamna Sule ya ce ya shaida da idonsa yadda wasu ’yan siyasa ke yabo da fadanci a gaban Buhari, amma daga bisani su sauya baki sheƙa da zarar shugabannin sun bar mulki. Ya ce, “Tun da na zama gwamna, na ga abin da son kai da kwaɗayi ke iya haifarwa. Na ga mutane suna zaune a gaban Shugaba Buhari...
      Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin.   Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano October 26, 2025
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita. “A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida...
    Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke. Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, tabbas  za su fuskanci Isra’ilawa da dukkanin karfinsu, kuma ba za su bar Isra’ila ta mamaye kudancin Lebanon ba,ko da kuwa hakan zai kai ga shahadarsu ne baki daya. Ya yi ishara da irin ayyukan wuce gona da iri da isr’ila ke yi akullum rana ta allaha  kan kasar Lebanon a kan idanun duniya, wanda hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar dakatar dayaki da...
    Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar. Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun ce sun adana amfanin gona tun shekarar bara suna jiran farashi ya tashi, amma hakan bai faru ba, illa ƙara faduwa da farashin ya yi. A watan Satumban 2024 Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofa na kwanaki 150 don shigo da hatsi kamar shinkafa, dawa, masara da alkama daga ƙasashen waje ba tare da biyan haraji ba, domin rage tsadar abinci. Amma wannan shigo da kaya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce.   Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi? NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu. Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki. Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami. Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai. An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida. “Da suka dawo...
    Wani ɗalibin Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya kashe abokinsa, wanda shi ma ɗalibi ne a jami’ar, sannan ya binne gawarsa a bayan gidansu. Wanda aka kashe mai suna Peter Mafuyai, ɗalibi ne da ke shekara ta uku a sashen hada-hadar kuɗaɗen banki. Dangote na shirin faɗaɗa matatarsa don zama mafi girma a duniya Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki Ana zargin Nanpon Timnan da ke ajin shekara ta biyu daga sashen karatun harkar noma, da kashe shi sannan ya binne shi a rami. Rahotanni sun bayyana cewar ɗaliban abokan juna ne sosai. An ruwaito sun fita ƙwallon ƙafa, daga nan suka wuce wani waje sannan suka dawo gida. “Da suka dawo...
    A ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1945, wato bayan da kasar Sin ta samu nasara a yakin kin harin mayakan Japan, kasar ta Sin ta karbi yankin Taiwan daga hannun Japanawa da suka yi rabin karni suna mamayar yankin, inda suke aiwatar da mulkin mallaka. Sa’an nan zuwa ranar 25 ga watan Oktoban bana, babban yankin kasar Sin ya gudanar da biki na musamman don tunawa da dawowar yankin Taiwan cikin harabar kasar. Dangane da batun, dimbin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban suna ganin cewa, bikin da aka shirya ya nuna nasarar da Sinawa suka samu a yakin duniya na biyu, kana ya shaida cewa, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za a iya...
    Matatar Dangote ta sanar da shirin ƙara ƙarfin sarrafa man fetur daga ganga 650,000 zuwa miliyan 1.4 a kowace rana, wanda zai sanya ta zama babbar matatar mai mafi girma a duniya. Shugaban kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Legas, yana mai cewa faɗaɗawar na nuna ƙwarin gwuiwa ga tattalin arziƙin Nijeriya da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mayar da ƙasar cibiyar sarrafa mai ta duniya. Dangote ya ce aikin faɗaɗawar “tana nuna amincewa da ƙarfin Afrika wajen tsara makomar makamashinta,” yana mai yabawa gwamnati bisa manufofi irin su Naira-for-Crude Policy da One-Stop Shop Initiative, waɗanda suka ƙarfafa zuba jari a ɓangaren mai. Ya kuma tabbatar da cewa matsalolin da suka...
    A baya bayan nan, kundin da aka amince da shi yayin cikakken zama na hudu na kwamitin kolin JKS na 20, ya tanadi tsare-tsaren musamman na fadada bude kofofin kasar ga sassan waje, da dora muhimmancin gaske ga samar da sabon yanayin hadin gwiwar cimma moriyar juna. A halin yanzu, a hannu guda ana ganin zurfafar sabon zagayen juyin-juya-halin fasahohi, da sauyi a ci gaban masana’antu, a gabar da duniya ke bukatar bude kofa da rarraba gajiya sama da duk wani lokaci a baya. A daya hannun kuma, tsarin daukar matakan kashin kai da kariyar cinikayya na dada kamari, kuma duniya na fuskantar yanayin rashin daidaiton ci gaba da gibi a fannin jagoranci. A wannan yanayi mai sarkakiya da duniya...
    Alhaji Aliko Dangote, na shirin faɗaɗa matatar mansa domin ta riƙa tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana. A halin yanzu, matatar tana tace gangar mai 650,000 a rana, amma Dangote, ya bayyana cewa suna shirin ƙara adadin cikin shekaru uku masu zuwa. Ba zan sake tsayawa takara ba, zan bai wa matasa dama — Dasuki El-Clasico: Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2 Ya bayyana haka ne yayin wani taro da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce faɗaɗa aikin zai sa matatar ta zama mafi girma a duniya. “Wannan shiri yana nuna yadda muke da cikakken shiri a Afirka da kuma dogaro da makomar Najeriya a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu,” in ji shi. Ya bayyana...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai October 26, 2025 Daga Birnin Sin Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya October 26, 2025
    Ya ƙara da cewa Basira ‘Yar Guda ta bayyana cewa za ta amince da aure ne kawai idan Idris ya mallaki gidansa na kansa, ba wanda yake haya ba. Wannan ne ya sa kotu ta dakatar da yanke hukunci domin bai wa Hisbah damar tabbatar da cewa an bi tsarin aure yadda ya dace da shari’ar Musulunci. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji October 26, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025
    Gyaran da aka fara ya yi daidai Nambobi suna ba da labarin wani ɓangare na labarin,  amma suna bayyana lamarin ne kawai, amma suna bayyana lamarin gaba ɗaya. A shekarar 2023, FIRS ta samu Naira Tiri liyan12.36, abinya zarce kuɗaɗen da ake tsammanin shigowa daga gare ta, har ma wuce kashi 7 na kuɗaɗen shigar da ake sa ran da ake zata kawo, hakan kuma shi yasa mafi kayu ɗin kuɗaɗen shigar da aka samu a tarihin tara kuɗaɗen haraji. A shekarar 2024, an kuɗaɗen shigar suka ƙaru da—Naira Titiliyan 21.7, ba kamar na shekarar 2023 ba , inda aka nsamu Naira Tiriliyan19.7. Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar Gwamnan Bauchi...
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin tafiya kasar Koriya ta Kudu, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 32, na kungiyar hadin-gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar, an gudanar da wani taron tattaunawa, mai taken “Shugabancin duniya da samun wadata tare a yankin Asiya da Pasifik” a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da jami’ar Yonsei  da gidan talabijin na YTN na Koriya ta Kudu suka shirya tare.   Yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce “CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da kasashen yankin...
    Kungiyar gwagwamaryar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa ba za ta bari Isra’ila ta samu wata hujja ta ci gaba da yaki a Gaza ba. Khalil al-Hayyah jigo a kungiyar ta Hamas, ya nuna gazawar gwamnatin Isra’ila na cimma burinta a Gaza kuma ya bayyana cewa kungiyar tana mutunta dukkan alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma ba kuma ba za ta bari makiya su sami hujjar ci gaba da yakin ba. al-Hayyah, shugaban ofishin siyasa na Hamas a Gaza, ya bayyana a wata hira da tashar Al Jazeera cewa gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma duk wani burinta a lokacin yakin kuma Hamas za ta yi duk mai yiwuwa don hana sake barkewar yaki. Da...
    A kwanan nan, wata manufa da aka zartas a yayin wani taron kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ta janyo hankalin al’ummun duniya, wato yadda kasar Sin take neman gaggauta dogaro da kai wajen kirkiro sabbin fasahohi, da zama mai jagorantar ci gaban masana’antun zamani a duniya. Inda dimbin kafofin yada labaru na kasashe daban daban ke ganin cewa, manufar ta nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora a bangaren raya kasa ta wata ingantacciyar hanya, da bunkasa fannin kimiyya da fasaha, wadda ita ma ta zame wa sauran kasashe abin koya. Hakika, a wannan zamani da muke ciki, kusan dukkan kasashe suna sa lura kan aikin raya sabbin masana’antu. Saboda ra’ayi na kariyar cinikayya ya haifar da...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja, lamarin da ya haifar da tsoro da fargaba a tsakanin mazauna yankin. An gano cewa tankar, wadda ta taso daga Legas tana kan hanyarta na zuwa Kano, ta kife ne da sassafe a garin Takalafiya da ke Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja. Majalisa ta amince a ƙirƙiro sabbin jihohi 6 a Najeriya Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Wani mazaunin garin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya shaida wa Aminiya cews lamarin ya faru kimanin kilomita biyu daga garin Lapai. Ya ce kwanan nan aka gyara hanyar NNPCL, amma hanyar ta fara lalacewa...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Kwamitin Haɗin Gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, ya amince da buƙatar ƙirƙiro sabbin jihohi guda shida. Wannan mataki na cikin abin da aka cimma a ƙarshen taron kwana biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu. Matsalar kashe-kashe a Nijeriya ba ta da alaƙa da addini — Femi Kayode Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum A cewar kwamitin, an tattauna kan buƙatu 69, ciki har da buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278. Daga cikin buƙatun ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.   Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
    Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa matsalar kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan ba ta da alaƙa da addini, illa dai ayyukan miyagu da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da la’akari da bambancin addini ba. Fani-Kayode ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a matsayin bako mai jawabi a taron cika shekaru 35 da kafuwar Cocin Anglican da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna. NSCDC ta yi alhinin mutuwar Kwamishinan Tsaron Gombe An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano Tsohon Ministan ya ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su dawo daga rakiyar mutanen da ke amfani da addini wajen...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya fadawa shugaban Amurka Trump cewa ya ci gaba da rayuwar cikin mafarkinsa! A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Isra’ila ta “Knesset”, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya, amma kalmomi biyu kacal da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Sayyed Ali Khamenei, ya furta sun isa su zame a matsayinsa mayar da martani. Ya zo cikin Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa: Alfaharin Shugaban Amurka cewa: “Hakika sun yi luguden wuta kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran tare da ruguza su, tabbas wannan da’awa ce kawai, amma Amurkawa su ci gaba da rayuwa cikin wannan ruɗunsu!” Martani mai ƙarfi...
    Ya ƙara da cewa Kaduna ita ce jihar da ta cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa a yarjejeniyar Malabo kan saka hannun jari a harkar noma. Shugaban AUDA–NEPAD a Nijeriya, Honarabul Jabir Abdullahi Tsauni, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da kuɗaɗen haɗin gwiwa da suka bai wa shirin damar faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar. A cewar Tsauni, an horar da ƙanana manoma 345 kan kyawawan hanyoyin noma da kuma dabarun noma masu jituwa da yanayin sauyin yanayi, ciki har da noman lambu na gida irin su tumatir, barkono mai zaƙi, masara, wake, da waken soya. Komashinan noma na Jihar Kaduna, Murtala Dabo, ya bayyana cewa wannan shiri ya nuna yadda Kaduna ke da niyyar mayar...
      Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
    Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Gombe, ta bayyana alhini bisa rasuwar Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (mai ritaya). Haka kuma hukumar ta bayyana jimami kan da ɗan sandan da ke tsaron kwamishinan, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, wadanda suka rasu a wani mummunan hadarin mota da ya afku ranar Juma’a. Sojoji sun daƙile harin ISWAP a Borno An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa  A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamandan hukumar, Jibrin Idris, ya ce rasuwar babban rashi ce ba ga iyalan mamatan kawai ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar...
    Aikin, wanda ke wakiltar tashar fitar da ɗanyen fetur ta farko da kamfanin Afirka mai zaman kansa ya bunƙasa a ƙasar, yana nuna babban jarin da ya wuce dala miliyan 400 a matakin farko, inda ake sa ran kuɗin zai ci gaba da bunƙasa har ya haura dala biliyan 1.3. GEIL, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Anthony Olusegun Adegbulugbe, wani sanannen malami kuma ƙwararren masani a fannin tsare-tsaren makamashi, yana da ƙwarewa mai sosai a tsawon shekaru masu yawa. Yana aiki a matsayin shugaban jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun, ya kuma kasance babban mai ba da shawara kan makamashi ga tsohon shugaba ƙasa, Olusegun Obasanjo. Haka kuma ya kasance shugaban shirin “National Gas to Power” na Nijeriya kuma ya...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan SC Bashir Adamu Jibrin, jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) da ya rasu a bakin aiki a kasuwar Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa. Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ne ya miƙa tallafin ga matar marigayin a ofishinsa, inda ya ce wannan taimako na nufin tallafa wa iyalan marigayin tare da taimaka musu wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu. Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ABU ta musanta zargin ƙera makamin nukiliya a ɓoye Ya shawarci matar marigayin da ta yi amfani da kuɗaɗen wajen kula da ilimi da walwalar ’ya’yanta, tare da jaddada cewa gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da...
    Wani rahoto na kafar watsa labarun Birtaniya ya bayyana cewa; Da akwai fiye da fursunoni 90 da suke yajin cin abinci a gidan kurkukun kasar Bahrain suna neman a sake su. Rahoton ya kuma ce, mafi yawancin fursunonin da suke yajin cin abincin suna babban gidan yarin kasar ne, kuma an kama su da yi musu hukunci ne bisa dalilai na siyasa. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da fursunoni a kasar Bahrain suke yajin cin abinci bisa nema a kyautata yanayin rayuwarsu a inda ake tsare da su, ko kuma neman a sake su ba tare da wani sharadi ba. Wani sauti na daya daga cikin fursunonin da aka dano daga cikin gidan kurkuku, ya bayyana cewa;...
    Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran  Ali Larijani ya bayyana cewa; Bayan da aka dauki shekaru biyu ana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi, wanda mutane 70,000 su ka yi shahada, wasu fiye da 100,000 su ka jikkata, suna son a rufe wannan laifin da taron zaman lafiya. Ali Larijani ya kara da cewa; Sun kashe al’ummar Falasdinu, sun hana shi abinci da ruwa, yanzu kuma suna son bayyana kawukansu a matsayin masu ceto da Falasdinawa, don haka wannan taron ba komai ba ne sai wasan kwaikwaiyo. Taron da aka yi a Sherm-Sheikh na Masar an yi shi ne a karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump wanda kasarsa ce ta kasance a gaba wajen bayar da makamai ga...
    Yana magana ko jawabi cikin hankali, amma kuma shawarwarin da yake badawa suna da matuƙar amfani wajen kawo gyaran wurare da dama. Mai ilimi, tsara yadda za’a ɓullo ma al’amura, mutunci ga kuma kwarjini da ƙwarewa An haife Kalu 5 ga Mayu, 1971, a Agbamuzu, a ƙaramar hukumar Bende ta Jihar Abia State, tarihin rayuwar Kalu ya fara ne daga aiki da kuma samun tallafin ƙaro ilimi. Yana da digirin digirgir PhD a tsarin al’umma da kuma karatun abinda da wayo ake koyonsa (Jami’ar Abuja), da kuma LL.M akan ta’addanci da taimakawa kan jin ƙai  (Distinction, daga Jami’ar Kalaba), da MBA daga Jami’ar Oɗford Brookes  (UK), da kuma LL.B (Hons.) daga Kalaba. Ya cigaba da karatu— halin yanzu yana karanta...
    A yau Asabar 25 ga wannan wata, ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar sun gudanar da liyafar murnar kebe ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, a dakin taro na Diaoyutai dake birnin Beijing. Wakilan bangarori daban daban na yankin Taiwan da na babban yankin kasar Sin masu halartar bikin murnar cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da safiyar wannan rana sun halarci liyafar. Direktan ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin da ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kiwon Lafiya Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello October 25, 2025
    “Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
    Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU,  ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar. A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta bayyana cewa labaran da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama. Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare — Zulum ’Yan sanda sun taimaka wa ’yan daba rusa gidaje — Al’ummar Shendam “Mun lura da wani faifan bidiyo da na’urar AI ta ƙirƙira, wanda wasu ke yaɗawa suna iƙirarin cewa ABU na ƙera makamin nukiliya a ɓoye. Wannan ƙarya ce babu gaskiya a cikinta,” in ji...
    Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta karyata wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu wajen wani shiri na sirri kan hada makamin nukiliya a Nijeriya. A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya fitar a ranar Asabar, jami’ar ta bayyana cewa wannan faifan bidiyon da aka samar ta hanyar na’urar kirkirar bidiyo, karya ne kuma an shirya shi ne don rikita jama’a da bata hakikanin manufar kasar wajen amfani da makamashin nukiliya. Umar ya jaddada cewa dukkan aiyukan nukiliyar Nijeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin lumana da kuma bin ka’idodin kasa da kasa kamar yarjejeniyar NPT da Pelindaba Treaty, wadda ta...
    Gungun kogiyoyin bada agaji sun yi gargadin cewa yanayin da rayuwar ke gudana a yankin gaza ya zarce yadda ake tsammani, duk da abin da aka kira da tsagaita wuta, kamar yadda majalisar dinkin duniya ta bayyana akalla falasdinawa 1.5 suka cikin bukatar gaggawa domin tsira da rayuwarsu. Duk da cika kwanaki 13 da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Gaza tsakanin Hamas da isra’ila, amma alumma suna cikin bala’I a yankin, duk da gargadin da ake yi akan haka,  sama dai kungiyoyin agaji 41 ne suka yi kira ga isra’ila ta janye killacewar da tayi wa yanki, kuma kotun duniya ta fitar da hukumce dole ne isra’ila ta bude kofofin shigar da kayan agaji zuwa yanki kuma ta tabbata...
    Ta hanyar aikinsa, Adeyemi yana nuna cewa ƙirƙira tana da ƙarfi sosai lokacin da take bauta wa bil’adama. Manhajarsa, wacce yanzu ake gwadawa a makiɗa da dama na manyan makarantu, ba kawai tana ba da damar samun ilimi bace, har ma da haɗa ɗalibai cikin zamantakewa, tana taimaka wa aiki ga ɗalibai masu rauni a gani bane kawai, su yi hulɗa da ƙwarin gwiwa a cikin ajujuwa da muhallin dijital. A wannan ma’anar, gudummawarsa ta kasance fasaha da ɗan’Adam: tana cike giɓi, faɗaɗa dama, kuma tana ƙalubalantar tunanin da aka saba game da naƙasa da ƙwarewa. Tafiyar Adeyemi tana nuna haɗin kai tsakanin ƙwarewar fasaha da shugabanci mai manufa. Bayan ya yi horo a Kimiyyar Kwamfuta a Coɓenant Uniɓersity, ya...
    Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne. Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya...
    Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
    Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin halartar taron shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pacific (APEC) karo na 32 a Koriya ta Kudu da kuma ziyarar aiki a kasar Koriya ta Kudu, an kaddamar da nuna muhimman shirye-shiryen talabijin da fina-finai na rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a membobin APEC. Za a watsa shirye-shiryen fiye da goma a manyan kafofin watsa labarai 22 a kasashe 14 na yankin Asiya da tekun Pacific, ciki har da Australia, Kanada, Chile, Indonesia, Koriya ta Kudu, Peru, Rasha, Thailand, da Amurka.   Babban darektan CMG Shen Haixiong, ya fada a cikin wani sakon bidiyo cewa, ana fatan wadannan shirye-shiryen talabijin da fina-finai za su...
    “Muna godiya ga sadaukarwar da sojoji da hukumomin tsaro ke yi. Wannan wasa tsakanin tsoffin ’yan wasan Barcelona da tsoffin ’yan wasan Afirka shaida ce ta nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu wajen dawo da zaman lafiya,” in ji shi. Tsoffin ’yan wasan Barcelona sun isa Nijeriya domin buga wasa da tsoffin ’yan wasan Afirka a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoba, 2025. Yayin da Matawalle ke tarbarsu a ofishinsa, ya miƙa saƙon maraba da fatan alheri ga tawagar a madadin Gwamnatin Tarayya da al’ummar Nijeriya, inda ya yi musu fatanalheri. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni An Sake Saka Sunan Osimhen A Cikin ‘Yan Takarar Kyautar Gwarzon Dan...
    Aƙidar Dr Bello abu ne mai saƙin gaske kuma akwai hikima a ciki sosai. Shi ne kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya wand aba wai sai kana da kuɗi mai yawa ba. Tsarinsa shi ne haɗa yi wa mutane aiki, ilimantar da su tared fda kuma tsugunar da su. Wannan mataki ne da yake tabbatar da an samun cikin gaggawa da kuma sauƙin gaske.. Daga Legas zuwa Kano, daga Ondo zuwa Kuros Riba, kungiyar CFDF tana tafiya da kayan aiki na tafi da gidanka da kuma rundunar likitoci masu tiyata na sa kai, masu aikin jinya, da ma’aikatan jinya. Kowace manufa asibiti ce mai motsi – duba marasa lafiya, yin hadaddun tiyata, da bayar da shawarwari da tallafin abinci mai...
    “Gudanar da harkokin kuɗaɗe ba bayar da taimako ba ne, haƙƙi ne.”  Ƙoƙarin Cike Gibi Tare Da Gina Makoma Mai Kyau Lokacin da OPay ya shiga fannin harkokin kuɗaɗe na zamani a Nijeriya, ƙalubalen ya kasance bayyane suke, kusan rabin yawan mutanen Nijeriya ba su da damar samun shiga harkokin kuɗaɗe. Waɗanda suka kafa kamfanin sun gano cewa yawancin ‘yan Nijeriya sun yin isa da bankuna, tsarin yana haifar da jinkiri, kuma tsarin yana da barazana mai yawa. OPay ta kasance mai sauƙin gudanarwa, wani tsarin kuɗi na wayar hannu da ya dace da rayuwar yau da kullum ba tare da tangarda ba. Daga biyan kuɗi ta walat zuwa biyan kuɗin kayayyakin more rayuwa, daga sayan katin waya zuwa mu’amaloli...
    Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, wanda Kwamishinan Ruwa, Alhaji Aminu Dodo Iya, ya wakilta, ya jaddada cewa sarautun gargajiya su ne ginshiƙin zaman lafiya da ci-gaban al’umma. Ya ce shugabannin gargajiya na taka rawa wajen haɗa kan jama’a da gwamnati, tare da tabbatar da ɗorewar cigaba a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Manyan Labarai Jami’ar ABU Ta Ƙaryata Zargin Ƙera Makamin Nukiliya A Asirce October 25, 2025 Labarai Hukumar Kare Ƴancin Masu Amfani Da Kaya (FCCPC): Tabbatar Da Adalci A Kasuwa October 25, 2025
    A shekarar 2008, Skales ya shiga gasar Zain Tru Search kuma ya lashe yankin ArewaTsakiya na gasar. A lokacin, ya riga ya saki waƙarsa ta farko “Must Shine”, wacce ta samu yawan fitowa a tashoshin Rhythm FM a Lagos, Jos, da Abuja. Ana tuna shi da burinsa na zama babban mawaƙi da sha’awar ilimi, ya ɗauki sunan mataki SKALES, wanda ke nufin “Seek Knowledge, Acƙuire Large Entrepreneurial Skills”. Daga baya ya koma Lagos, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar rikodi da Empire Mates Entertainment (E.M.E.) a shekarar 2009. Waƙarsa ta shekarar 2009 “Heading for a Grammy”, wadda take waƙar ƙarfafa kai, ta samu wahayi ne daga ƙalubalen rayuwarsa a wancan lokaci. Skales yana ɗaya daga cikin manyan mawaƙan da suka...
    Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta  jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba. A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 ...
    Hukumar Kwastam Ta Tara Naira Biliyan ₦658.6 A Watan Satumba — DG Na NOA Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo Wannan inganci ba wai alama kawai ba ce. Tun daga shekarar 2023, hukumar ta sauƙaƙa sama da Naira biliyan 10 na mayar da kuɗin masu amfani don sulhu kai tsaye, mai iya bin sawu wanda ke nuna cewa dawainiya da gaskiya za a iya auna ta da kuɗi, ba wai da alkawari kawai ba. Jarumta a Zamanin Intanet Wataƙila mafi girman ƙarfin gwiwar FCCPC ya bayyana ne a shekarar 2025 lokacin da ta ɗora tarar Dalar Amurka miliyan 22 kan Meta Platforms saboda ayyukan amfani da bayanai ta...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Bai kamata a yi mummunan amfani da kwamitin tsaron ba ko kuma a yi amfani da shi don dalilai na siyasa Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya bayyana cewa: An gwada Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sosai ta hanyar ayyukan ta’addanci da kuma amfani da dabarunta na siyasa. Ya ce: “Dole ne kwamitin tsaro ya cika nauyin da ke kansa da mutunci, inganci, kuma ba tare da son kai ba. Babu wani memba, komai karfi da zai iya amfani da wannan cibiyar ba bisa ka’ida ba ko kuma ya yi amfani da shi don dalilai na siyasa ko na bangare guda.” A jawabinsa a Majalisar...
    Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Yaƙin da aka ɗora wa Iran ya canza daidaiton da ke tsakanin Sahayonayya da Amurka Tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC), Hussein Ta’ib, ya ce: Yaƙin kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyya ta ɗora wa Iran, ba wai kawai bai cimma komai ga Isra’ila ba ne, har ma ya canza daidaiton dabarun Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila gaba ɗaya. A lokacin taron tattaunawa na 31 na ƙungiyar Jaruman Musulunci a Qom, Hussein Ta’ib ya ce: “Dakarun kare juyin juya halin Musulunci da sojojin Iran sun kalubalanci masu girman kai inda suka kai wani mataki cikin saurin na zarce lissafin...
    Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
    Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.” Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen. Sun ce suna da...
    A ƙarƙashin jagorancinsa mai hangen nesa, hukumar NUPRC ta zarce burinta na samun kuɗaɗen shiga har da kashi 84.2 cikin ɗari, tana motsawa da ƙarfafa tattalin arziki da sauyi mai zurfi a fannin masana’antar. A matsayinsa na shugaban farko na CCE, Injiniya Komolafe ya haɗa da ƙwarewa ta injiniya da fahimtar doka cikin ƙwarewa don inganta aiwatar da Dokar Masana’antar Mai (PIA), inda ya kafa tsare-tsaren kula da aiki bisa gaskiya, ɗorewa, da bin ƙa’idar ƙwarewar duniya. Jagorancinsa ya haifar da ci gaban fasahar zamani, inda aka gudanar da mafi fa’idar tsarin neman lasisi a tarihin Nijeriya, tare da aiwatar da manufar “Haƙowa ko Barin Filin” (“Drill or Drop”), wanda ya farfaɗo da filayen haƙar mai da suka daɗe a...
    Lokacin da Etuh ya zama wanda ake maganarsa  musamman ma idan an taɓo maganar Takin zamani,  masana’antar ta kama hanyar lalacewa saboda ‘yan baran da sun mamaye ta, ga kuma cuwa-cuwa da ta yi wa wurin katutu, lamarin da ke sa ba a iya gane manoman gaskiya. Duk da hakan ba ta sa Etuh ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen haɗa kan da ya yi da gwamnatin tarayya, Etuh ya taimaka wa tsarawa da kuma gabatar da lamarin Takin zamani na Shugaban ƙasa Bola Tinubu (PFI),lamarin da ya kawo gaggarumin ci gaban aikin gona, domin kuwa an samu raguwar farashi,ya kuma samar da wata kafa inda manoma suke samun Takin zamanin kai tsaye. Sakamakon haka ya sa yanzu...
    Rashin Biyan Yan-fansho Bisa Lokaci Ta tabbata a lokacin mulkin Kwankwaso, “yan fansho a Kano, kan jira tsawon Watanni zuwa Shekaru ba tare da an biya su hakkokinsu na barin aiki ba. Haka ɗan-jummai Ganduje, yakan dan fara biyan hakkokin “yan fanshon, sai kuma a ga ya watsar. Sai a dauki tsawon lokaci yana ɓaɓatun za a ci gaba da biya, amma sai a ji shiru. Sai aka wayi gari karɓar fansho, musamman giratuti, ya zama tamkar tafiya Lahira, yau ne? Gobe ne? Babu wata cikakkiyar amsa!. Haƙiƙa kwata-kwata babu tausai, mutane sun kwashe akasarin Shekarunsu na haihuwa suna masu hidimtawa ƙasa dare da rana, cikin yanayi na sanyi, ruwan sama da garjin rana, dole ne su fito, su aje...
    Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai. Sojoji Sun Kama Mutane 69 Masu Fasa Bututun Mai A Yankin Neja-Delta Sojoji Sun Lalata Matatun Mai 20 A Yankin Niger Delta A tsakiyar shekarun 1990, arzikin mai na Nijeriya yana samu wadata a wasu wurare amma ya zama ana barin al’ummomi masu arziƙin mai cikin talauci, gurɓawa, da kuma rashin muryar magana. Ga matashin Tompolo, yin shiru wannan bai zama zaɓi ba.   Gwagwarmaya Da...
    Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Gombe, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasu a hatsarin mota. Gwamnatin Jihar Gombe ce, ta sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Watsa Labarai, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Juma’a. Tinubu ya faɗa wa ’yan Najeriya dalilin sauya hafsoshin tsaro — ADC Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri Sanarwar ta ruwaito cewa Bello ya rasu a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota. “Gwamnatin Jihar Gombe na cikin jimamin sanar da rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), sakamakon a hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan hanyar Malam Sidi...
    Ya ce Hukumar Binciken Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) za ta jagoranci kwamitin, domin ita ce ke da ikon tattara bayanan ma’adinai na ƙasa baki ɗaya.  “NGSA ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna bisa gaskiya da bayyana bayanai, tare da yin kira da a gudanar da binciken tabbatarwa mai zaman kansa,” in ji shi. Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar zai ƙara goyon bayan masu zuba jari a sashen ma’adinai na Nijeriya, tare da faɗaɗa bayanan kimiyyar ƙasa, wanda zai taimaka wajen haɓɓaka tattalin arzikin ƙasa ta hanyar albarkatun ma’adananta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Yayansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri October 24, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Majalisar Abinci Mai Gina Jiki ta Jihar Jigawa 774, inda ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na yaki da rashin abinci mai gina jiki da inganta yalwar abinci a fadin jihar. An gudanar da kaddamarwar ne yayin ziyarar Mrs. Uju Rochas-Anwuka, mai bai wa Shugaban Kasa shawara ta musamman kan lafiya ( Karkashin Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), wacce ta je Jigawa domin kaddamar da shirin Nutrition 774 da ke karkashin shirin sabunta kudurori na Renewed Hope Agenda. Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa ta kasance gaba a yaki da matsalar, tare da kafa shiri na musamman da aka yi wa lakabi da Masaki tun a 2020 domin fadakar da al’umma a...
    Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani. Aminiya ta ruwaito yadda shugaban ƙasa ya sauya hafsoshin tsaron da ya naɗa shekaru biyu da suka wuce. Gwamnan Bauchi ya naɗa ɗan uwansa a matsayin sabon Sarkin Duguri ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba tsammani bayan jita-jitar yunƙurin juyin mulki. “Ko da yake shugaban ƙasa yana da ikon yin irin waɗannan sauye-sauye, amma mum damu da wannan mataki biyo bayan...
    Gwamna Raɗɗa ya ƙara da cewa wannan zaman sulhu da ɓarayin daji da ake yi al’umma ce take yi ba wai gwamnati ba, ita gwamnati tana iya yin sulhu da ɗan bindigar da ya tuba ya yarda da zaman lafiya kuma ya ajiye mukaminsa. A cewarsa, rawar da gwamnati take iya takawa shi ne, ta ƙarfafa zaman lafiya, sannan ta tabbatar an bi doka da oda a cikin al’umma. Ya ce abubuwa da gwamnati ke lura da su shi ne, al’umma ta mori zaman lafiya domin bunƙasar tattalin arziki da sauran su.  Tunda farko a jawabinsa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Hon. Nasiru Mu’azu Danmusa ya bayyana cewa Gwamna Raɗɗa ya rage ƙarfin harkokin rashin tsaro a Jihar Katsina....
    Ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP a Kaduna tana cikin haɗin kai da zaman lafiya, inda ya bayyana batun tsige shugaban a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rikici da tashin hankali a cikin jam’iyyar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa October 22, 2025 Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025
    Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri. Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a. Ƙungiya ta tallafa wa ɗaliban makarantar masu buƙata ta musamman a Gombe ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa A yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, ya shawarci sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar. A nasa jawabin, sabon Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya...
    Hammayo ya shawarce shi da ya gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci tare da haɗa kan ƙabilu don tabbatar da zaman lafiya. A baya-bayan nan ne Gwamna Bala Mohammed ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin masarautu 13 a jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Sauya Hafsoshin Tsaron Nijeriya October 24, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Sake Kama Sowore Bayan An Bayar Da Belinsa October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu October 24, 2025
    Ƙungiyar Arewa Unity Women in Media, ta kai tallafi Makarantar Masu Buƙata ta Musamman da ke Gombe, domin taimaka wa gwamnati wajen kula da rayuwar ɗaliban da ke da buƙata ta musamman. Tallafin ya ƙunshi gidajen sauro, bargo da tabarmi, wanda aka raba wa ɗaliban a lokacin bikin miƙa kayan tallafin. ’Yan sanda sun kama ɗalibi da ya soki Gwamnan Neja ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Shugabar ƙungiyar, Lois Hassan daga GMTV Gombe, tallafin na da nuna kulawa da ƙauna ga ɗaliban, tare da tabbatar musu cewa al’umma ba ta manta da su ba. Ta ƙara da cewa ƙungiyar Arewa Unity Women in Media ƙungiya ce mai zaman kanta da ke gudanar da...
    Rundunar ’yan sanda ta kama wani matashi ɗan shekara 29, mai suna Abubakar Isah Mokwa ɗalibi da yake karatun digiri na biyu a tsangayar Tattalin Arziki na Noma a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja. An kama ɗalibin ne bisa zarginsa da sukar Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago. Rahotanni sun ce an an kama Abubakar Mokwa ne a wajen harabar jami’ar da yake da masauki a Lapai a ranar Alhamis bayan wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya caccaki gwamnan kan rashin aikin yi. ’Yan sanda sun sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu...
    Tawagar kamfanin na Rano Air a wurin ganawa da gwamnan, ta haɗa da Babban Manajan (Ayyuka), Abah O. Godwin; da Accountable Manager Alhaji Lawal Sabo Bakinzuwo; da Shugaban Sashin Ayyuka na ƙasa Bashir Abdullahi Wudilawa; da Shugaban Sashin Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Auwal Sulaiman Ubale. Jami’an kamfanin sun tabbatarwa gwamnan cewa kamfanin na Rano Air zai samar da nagartacciyar hidima abar dogaro, mai inganci kuma mai haba-haba ga kwastomomi, ta yadda za a samu sauƙin tafiye-tafiyen kasuwanci da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar da Arewa Maso Gabas baki ɗaya. “Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan ci gaba, inda ya bayyana hakan a matsayin wata shaida kan yadda Jihar Gombe ke da zaman lafiya da kwanciyar...
    Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshin bisa gudunmawar da suka bayar. Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, haɗin kai wajen tsaron Nijeriya. “Shugaban ƙasa ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da su tabbatar da cewa sun cancanci nadin da aka musu ta hanyar nuna ƙwarewa, faɗakarwa, da zumunci wajen tsaron ƙasa,” in ji sanarwar. Sanarwar ta bayyana cewa dukkanin sabbin naɗin za su fara aiki nan take. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ɗan’uwa Ya Kwaƙule Idanuwan Ƙanwarsa Don Yin Tsafin Neman Kuɗi A Bauchi October 24, 2025 Labarai Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule October 24, 2025...
    ’Yan Sanda sun sake kama dan gwagwarmaya kuma mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, bayan wata kotun Majistare da ke Abuja, ta bayar da belinsa.  An sake kama Sowore bayan kotu ta bayar da belinsa tare da wasu mutum 12 a ranar Juma’a. Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike Alƙalin kotun, Abubakar Sai’id ne, ya bayar da belin Sowore da wasu mutum 12 da aka tuhuma da tayar da hankalin jama’a, sakamakon zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin. Lauyan Sowore, Tope Temokun, ya zargi ’yan sanda da yin amfani da karfi, inda suka yi awin gaba ba tare da wani bayani ba....
    Mahaifin Rukayya, Muhammad Adamu mazaunin ƙauyen Bayan Dutse da ke Wailo, a gundumar Kubi cikin ƙaramar hukumar Ganjuwa a ranar 17 ga watan Oktoba ya kai rahoton caji ofis ɗin Soro ya ke shaida cewar wani matashi mai suna Auwal Dahiru mai shekara 17, ya kai farmaƙi wa yarsa da ƙoƙarin kasheta da kwaƙule mata idanuwanta.  Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil a ranar Litinin, ya ce, lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin cikin gaggawa a ƙarƙashin Baturen ɗansanda da ke kula da caji ofis ɗin Soro, CSP Aliyu Mohammad Goni, sun kai agaji inda lamarin ya faru. A lokacin da aka ɗauki Rukayya zuwa asibitin koyarwa na...
    Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ya fitar a ranar Jumma’a. An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike A cewar sanarwar, an nada Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin Ƙasa, a matsayin Sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa. An kuma naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin...
    Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar. Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda ya kamata. An kama Sakataren APC na mazaba a Yobe kan zargin aikata kisan kai Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027 Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin PDP. Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taronta na kasa a watan Nuwamba a birnin Ibadanna  Jihar Oyo, amma wasu rahotanni na cewar magoya bayan Wike...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu October 24, 2025 Manyan Labarai Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma October 24, 2025 Manyan Labarai An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya October 24, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025 Sanata Uba Sani: Mai Haɗa Kan Al’ummar Da Suka Rarrabu October 24, 2025 Manyan Labarai Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma October 24, 2025 Manyan Labarai An Kafa Cibiyoyi 296 Na Koyon Fasahar Zamani A Faɗin Nijeriya October 24, 2025
    A shekara biyu kaɗai,ya yi ƙoƙarin maida Jihar Kaduna da aka sani da rarrabuwar kai, yanzu ta koma tsintsiya ɗaya sanadiyar hakan. Yin gyara ta hanyar ci gaba Gwamna Sani ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 2023 ba a matsayin wanda ya iya lamarin siyasa sosai ba, sai dai mai son kawo agyara. Aikinsa na farko ba siyasar bace —mutane ne yafi maida hankali kansu. Ya fara ƙaddamar da lamarin gaggarumin ci gaban ƙauyuka ta yadda abin ya zama a kowace ƙaramar hukumar akwai aikin da ake yi.Gina hanyoyi, asibitoci,  makarantu, kasuwanni an fara gigginasu a ƙananan hukumomi  23 . Cikin ci gaban daya samu sun haɗa da: Haɓaka ƙananan asibitoci 225 inda aka mayar da su matsayi...
    Kafin ya zama gwamna, ya kasance Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, inda ya yi ƙaurin suna wajen yin adalci, kwanciyar hankali da kuma zurfin fahimtar shugabanci. Wannan gogewa ta aikin doka, ta zama ginshiƙin nasararsa na gudanarwa. Kazalika,ya ba shi damar daidaita hangen nesa da tuntuɓa tare da yin taka- tsan-tsan wajen aiwatar da ayyukansa. Ajandarsa Ta “MORE Agenda” Ajandarsa ta ayyukan da yake ƙuzun aiwatarwa, ƙarƙashin “MORE Agenda”, Gwamna Oboreɓwori, ba wai kawai taken ba ne; tsari ne na aiki wanda ya ƙunshi kowane ɓangare na ayyukan da son aiwatarwa ƙarƙashin mulkinsa A Ƙarƙashin Jagorancinsa: An kammala ayyukan tituna sama da 513 da suka shafe kusan kilomita 1,500, ban da kuma waɗanda ake kan ci gaba da gudanarwa a...
    Rundunar ’Yan Sandan jihar Yobe ta ce ta cafke wani shugaban mazaba na jam’iyyar APC a karamar hukumar Karasuwa bisa zarginsa da hannu a kisan wata mata. Rundunar ta ce ta samu nasarar ce a binciken da take yi kan wata gawar da aka gano a kusa da Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a makon da ya gabata. Gwamnan Neja ya ba dukkan iyalan wadanda suka kone a gobarar tankar mai N1m Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027 A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ’yan sanda daga sashin karamar hukumar Bade sun kama wani mutum mai suna Abdulmumini Garba, mai shekaru 60, dangane da mutuwar matar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC Uku Da Wasu October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji October 24, 2025 Manyan Labarai Nnamdi Kanu Ya Sake Bayyana A Kotu Ba Tare Da Lauya Ba, Zai Kare Kansa Da Kansa October 24, 2025
    ‘Yan sandan kasar Ghana sun sanar da cewa tserato da wasu ‘yan Najeriya 57 da aka yi faskwaurinsu, haka nan kuma wasu mutane 5 da suke aikata laifuka ta hanyar sadarwar na “Internet” Jami’an ‘yan sandan sun kwace nau’ra mai kwakwalwa 77 da wayoyin hannu 38, sai kuma wasu motoci 2, akwatin talbijin 3, da kuma wasu na’urori da suke amfani da su a yaudarar mutane. A ranar Larabar da ta gabata ne jami’an ‘yan sandan kasar ta Ghana su ka sanar da kai farmakin a birnin Accra a ranar Laraba 22 ga watan nan na Oktoba. Shekarun mutanen da ake amfani da su wajen yaudarar mutane ta hanyar internet suna a tsakanin 18 zuwa 26,tuni kuma an kai su...
    Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗaya ga duk iyalin da ya rasa ɗan uwa a gobarar tankar man da ta faru a garin Essa, Karamar Hukumar Katcha. Haka kuma, ya ba da tallafin naira dubu ɗari biyar ga kowanne daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin da abin ya shafa, inda ya tantance tare da ganawa da shugabannin al’umma da mazauna yankin. Tinubu ya bukaci sabon shugaban INEC ya gudanar da zaben gaskiya a 2027 NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? Wannan sanarwa ta fito ne daga Sakataren...
    MDD ta bayyana cewa a tsakanin kowadanne mutanen Gaza  4, daya daga cikinsu yana fama da yunwa. Mai Magana da yawun kungiyar Agaji ta tarayyar turai, May Musa Sayegh, ta yi ta’aliki akan wannan adadin na masu fama da yunwa a Gaza, inda ta ce; Wannan shi ne hakikanin abinda yake faruwa a kasa, kuma ya shafi mata manya da ‘yan mata da kuma kananan yara masu yawa.” May Musa Sayegh ta fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; Sakamakon hare-hare na tsawon shekaru biyu da kuma rashin samun damar shigar da kayan agaji,musamman a arewacin Gaza aka fada cikin wannan halin. Sayegh ta kuma ce; ta fuskar kiwon lafiya, al’amurra suna kara tabarbarewa, domin mutane suna rayuwa cikin bakin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƙarfin Niyyar Manzon Allah (SAW) Da Matakinsa Na Aƙlul A’ala October 24, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Tafka Ɓarna A Kasuwar Shuwaki, Ta Ƙona Fiye da Rumfuna 500 A Kano October 24, 2025 Manyan Labarai Gwarzuwar Shekarar 2025 Sanata Oluremi Tinubu October 24, 2025
    Kungiyar ‘yan wasan kokawar Iran na gargajiya na matasa ‘yan kasa da shekaru 23, ta lashe kambun duniya bayan da ta samu lambobin yabo mafi yawa. Kungiyar ta Iran ta sami lambobin zinariya 3, da azurfa 1 da kuma tagulla 2. ‘yan wasan da Iran da su ka sami kyautar zinariyar sun hada Iman Muhammadi mai ajin nauyi kilio 72, da Gulam Ridha Farakhi mai ajin nauyi kilo 87 da kuma Fardin Hidayati mai ajin nauyi 130. Wanda ya  sami azurfa kuwa shi ne Sajjad Abbaspur mai ajin nauyi kilo 60, sai kuma wadanda su ka sami tagulla da su ne Ahamd Ridha Muhsin Najad mai ajin nauyi 67,sai Abul Fadal Muhmadim ai ajin nauyi 82. Kungiyar ta Iran ta...
    “Shirin gwamnan na aiwatar da sabon tsarin albashi duk da ƙalubalen tattalin arziki ya nuna tausayinsa, gaskiya, da girmama kimar ma’aikata,” in ji shugabannin kungiyoyin.   Kungiyoyin sun kuma yaba da kokarin gwamnatin wajen gyara da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya inda suka bayyana gyaran da sabunta azuzuwan karatu a dukkan kananan hukumomi 23, amincewa da tsarin ritaya bayan shekaru 65 ko shekaru 40 na aiki ga malamai, da kuma dawo da sama da naira miliyan 500 na ajiyar ( ENDWELL) da aka rike a baya, a matsayin muhimman nasarori.   Ma’aikatan sun kara jinjina wa dawowar tsarin biyan gudunmawar adashin gata na malaman makaranta wato (ENDWELL) na kowane wata, inda suka bayyana cewa tsarin yana taimakawa wajen inganta...