2025-09-18@02:33:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 56
«Dokar Kare Hakkin Yara ta»:
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce. Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno. Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba....
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa rikicin Gaza ya kara kamari, inda ya yi gargadin cewa kusan shekaru biyu na killacewar Isra’ila da kai hare-haren bama-bamai sun yi illa ga lafiyar yara, ilimi.. “Bayan kusan shekaru biyu na abubuwan ban tsoro lamarin ya yi tasiri ga, kowane bangare na rayuwar yara,” inji Tess Ingram, manajan sadarwa na UNICEF na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka,. “Yara ba su da isasshen abinci da za su ci, ba su da ruwa mai tsafta, a kullum suna kokari su tsira daga hare-haren bama-bamai da ke ci gaba da yin barazana ga rayuwarsu. Cututtuka suna yaduwa, kuma yara sun rasa shekaru uku na zuwa makaranta,”. Share...
Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ke shafar maƙogwaro da hanyoyin numfashi, kuma tana iya hallaka mutum idan ba a yi saurin ɗaukar mataki ba. Rigakafi shi ne babban mataki wajen hana yaɗuwar cutar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 12; ciki har da yara huɗu ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo. Hatsarin ya auku ne lokacin da wata tankar gas mai lamba T 16716 LA, mai ɗauke da rubutun NUPENG, ta ƙwace daga kan hannunta ta afka wa wata motar fasinja. Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Motar na ɗauke da mambobin Ikklisin Jehovah’s Witness daga Jihar Anambra zuwa ƙauyen Agwa da ke Jihar Imo. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da mutuwar manyan mutane takwas da wasu yara huɗu, yayin da wasu...
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar rashin ɗa’a daga wani rukunin magoya bayan tsohon gwamna kuma Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta kira da suna “Badaru Boys.” Sanarwar ta zargi wannan rukunin da haddasa rikice-rikice a wuraren tarukan siyasa, tare da yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi. Ta bayyana cewa hakan ya faru a wurare da dama ciki har da Majiya, Gumel da kuma zaben cike...
Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” ta bayyana cewa: An tauye hakkokin yaran Gaza na ‘yancin samun ilimi, kuma makarantu sun zama matsugunan ‘yan gudun hijira Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana a jiya Juma’a cewa: An tauye hakkokin yara a zirin Gaza tun daga hakkin samun ’yancin ilimi, inda a yanzu haka makarantu sun zame matsugunan ‘yan gudun hijira, saboda an rusa musu gidaje ko lalata musu, yara ba su da wurin koyon ilimi. Kungiyar ta kara da cewa “fiye da yara 700,000 a Gaza ba su da ilimin boko.” Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fada a jiya Juma’a cewa sanarwar da Katz ya yi na kara kai...
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya. Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin. Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin. Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa...
Jami’ar kasa da kasa a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Kananan Yara masu fama da yunwa a Gaza suna mutuwa sannu a hankali Inger Ashing, shugabar kungiyar Save the Children, ta tabbatar da cewa: “Yaran Gaza da ke fama da yunwa sun kai ga mataki mai tsanani,” inda ta bayyana dalla-dalla kan mutuwarsu a hankali, kuma sun kai ga matakin da ba su iya yin kuka. Inger Ashing ta fadawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba cewa: Yunwar da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a Gaza a makon da ya gabata, ba wai kawai “kalmomi ne na fasaha ba,” ta kara da cewa: “Lokacin da babu isasshen abinci, yara suna fama da rashin abinci mai...
Daga cikin wadannan alkaluman na yara miliyan 1.65 sun kasance suna a jihohin Zamfara, Bauchi, Sokoto, Borno, Kebbi, Kano, da kuma wadanda kuma suke a jihohin da Kungiyar ta MSF ke gudanar da ayyukanta kuma jihohin da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro. Bugu da kari, akasarin kungiyoyi, sun yi ittifakin cewa, batun kula da lafiya, abu ne, da ya kamata matan Gwamatin uku na kasar, su bayyana dokar ta baci a kai. Wannan rashin ayyana dokar ta bacin a fannin, mussaman a Arewacun Nijeriya, za a iya cewa, babbar gazawar rashin iya gudanar da shugabanci na gari ne, inda a Katsina irin wannan sakacin, mussaman na gazar samar wa yaran abinci mai gina jiki, ya bayyana karar...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai. Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma...
“Jerin sunayen yaran Gaza da ke mutuwa “, dole ne a tabbatar da ba a kara yawansu ba. Shin wadannan sunayen yara kanana da hotunan su ba za su iya tada hankalin bangarori masu rikici ba? Akasarin kasashen duniya sun yarda cewa “shawarar samar da kasashe biyu” ita ce mafitar warware matsalar Falasdinu, kuma amincewa da kasar Falasdinu wani muhimmin mataki ne na aiwatar da wannan shawara. Kwanan nan, an gudanar da babban taron kasa da kasa kan warware matsalar Falasdinu da aiwatar da shawarar “samar da kasashe biyu” a hedkwatar MDD da ke birnin New York, inda ministocin harkokin wajen kasashe 15 suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, suna nuna niyyar amincewa da kasar Falasdinu. A yanzu,...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba. Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu. Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta...
Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa. Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba. Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala....

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan jin kai da dama da suka yi balaguro zuwa yankunan da ake fama da rikici, da bala’o’i, da wuraren yaki a duniya, kuma dukkansu, ba tare da togiya ba, sun amince cewa, ba su taba ganin wani yanayi mai kama da abin da ke faruwa a Gaza ba. Abu Khalaf ya yi nuni da cewa: Mutanen yankin Zirin Gaza sun fara fama da yunwa, sannan...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Muhammad Farah, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida kan kasafin kuɗi mai la’akari da bukatun yara, inda ya gabatar da wasu alkalumma masu tayar da hankali dangane da rayuwar yara a jihar. Farah ya ce jihar Kano na da yara fiye da miliyan 6 da rabi da ke ƙasa da shekaru 18, wadanda da dama daga cikinsu na...
Hukumar bayar da agajin gaggawa a Gaza ta ce aƙalla mutum 10, ciki har da ƙananan yara guda shida ne suka rasu a sanadiyar harin da Isra’ila ta kai ta sama a Gaza a safiyar Lahadi. An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin Nuseirat’s al-Awda, inda wani likita ya ƙara da cewa sun yi jinyar wasu mutum 16, ciki har da ƙananan yara guda bakwai. Wani ganau ya ce jirgi mara matuƙi ne ya harba makami mai linzami a kan dandazon mutanen da suka yi layi riƙe da jarkunansu domin ɗibar ruwa daga wata tankar ruwa a sansanin ƴangudun hijira na al-Nuseirat. Har zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar tsaron Isra’ila ba ta ce komai ba kan batun. Wani faifan...

Magance Matsalar Yara Da Ba Sa Zuwa Makaranta: Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Shirin Ciyarwa A Makarantun Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara. Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da rugujewar sassan ilimi da samar da haɗin gwiwa, kamar Bankin Duniya ta hanyar shirin AGILE da kuma UNICEF. A kwanakin baya Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha tare da haɗin gwiwar UNICEF, sun kafa wani kwamitin fasaha na shugabannin hukumomin da masu ruwa da tsaki domin ziyartar mananan hukumomi 14, da tantance yaran da ba su zuwa makaranta, da kuma tabbatar da shigar su makarantu. ...
Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro. A cewar kungiyar, jihohin su ne Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano. Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata. Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja...
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa. Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa. Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada. Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar hanya. Indomie tun da dadewa tana da kaimin ciyarwa da abincin dake gina jiki da kuma cincidar Mafarkin kowanne yaro. Wannan dandalin na Indomie AI Career Generator ya tunkari wannan manufa, na taimakawa yara su fahimci ƙarfin gwiwarsu, su yi manyan mafarkai, kuma su san cewa makomarsu tana gab da su. “Indomie ta tallafa wa yarada dama wajen girma, koyo, da zama ababen Alfahari. Tare...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
Yawan Yaran da ba su zuwa makarantun boko a Nijeria wadanda suka kai kimanin su miliyan 18.3, hakan ya nuna cewa, wannan adadin na Yaran, kusan daidai yake da yawan alumomin da ke a kasashen Norway, Singapore, da Cuba. Wannan ba wai batu ne, na matsalar da ake fuskanta a bangaren ilimin boko kadai ba, domin matsala ce, da ke bukatar a ayyana dokar ta baci tare da samar da daukin da ya kamata daga bangaren gwamnati da kuma sauran alomomin kasar. Misali, wata kungiya mai kare rajin Yara, mai zaman kanta da ake kira da, Sabe the Children ta bayyana cewa, sama da Yara1,600 a shekarar 2014, aka sace a makarantun su, wadanda sace su din, ya zama tamkar,...
A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC). An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da haɗin gwiwar Save the Children. A cewar, wakilin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Salisu Baba Lawal shirin zai shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 a faɗin jihar. “Wannan shiri na Gwamnatin Jihar Kaduna ne tare da haɗin gwiwar abokan ci gaba da masu aiwatar da ayyuka,” in ji shi. “Gwamnatin Jihar Kaduna ta samo lamunin tallafin kudi domin aiwatar da wannan shiri da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.6 cikin duk yara 1,000, adadin da ya yi kasa sosai cikin jerin kasashen duniya, dake rukunin masu al’ummun dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shiga. Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata,...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing. Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina kasa da za su raya hanyar gurguzu mai sigogin kasar Sin. A game da bikin ranar yara ta duniya da za a yi a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, ya taya musu shiryawa murna a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya mika sakon gaisuwa ga dimbin yara jagororin, da masu dora su a kan hanya, da bangarensu na...
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama. Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su da masaniyar irin wahalar da iyayensu ke sha wajen ganin sun samar musu da rayuwa mai inganci. Lallai ya kamata ƴan majalisa su matsala ƙaimi a samar da wani yanayi ga yara musamman wajen kare su daga faɗawa ƙangin talla ko bautar aikatau ko kuma zama ƴan jagorar masu bara, hakan kuwa zai faruwa ne idan aka aiwatar da dokar kare ƴancin yara. Daga...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Najeriya tana cikin ƙasashen da suka fi yawan yara a duniya, a cewar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Sai dai a cewar Hukumar ta UNICEF, kusan rabin wadannan yara suna fuskantar kalubale, kama daga cin zarafi zuwa rashin samun kulawa da dai sauran su. Wadannan matsaloli da yara suke fuskanta dai sun dade suna ci wa masu ruwa da tsaki tuwo a kwarya. NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu” Yayin da ake bikin Ranar Yara, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kan halin da ya...
Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana. Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci. Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih...
Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
Cutar Mashaƙo ta ɓarke a unguwar Tukur-Tukur da ke garin Zaria ta jihar Kaduna, inda ta yi sanadiyar mutuwar yara biyu. Wannan ɓarkewar ta haifar da damuwa game da shirye-shiryen kiwon lafiya a Nijeriya. Abdulazeez Suleiman daga ƙungiyar Northern Elders Forum ya tabbatar cewa mutuwar ta faru cikin sa’o’i 48 bayan bayyanar alamun cutar. “Wannan ɓarkewar da ta biyo bayan wata irinta ‘yan watannin da suka gabata – inda ta kashe mutane huɗu – yana nuna gazawar tsarin kiwon lafiya da rashin isasshiyar allurar rigakafi a yankunan karkara,” in ji Suleiman. Cutar Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wacce ke haifar da kumburin maƙogwaro da wahalar numfashi. Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 520 — Gwamnatin Kano Kisan Mummuken...

‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
‘Yan gudun hijira a Sudan sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su ceto yara da tsofaffi daga mummunan kangin da suka shiga An gwabza kazamin fada a kusa da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka yi ruwan bama-bamai kan birnin da na manyan bindigogi, inda suka kashe fararen hula akalla 35. Sojojin Sudan sun samu nasarar dakile wadansu daga cikin wadannan hare-hare, amma duk da haka sun janyo hasarar rayukan bil’adama da na dukiya. Sannan sojojin Sundan sun kuma kwace iko da birnin Bara da ke Arewacin Kordofan, kofar Nyala a Kudancin Darfur. Dakarun kai daukin gaggawa sun yi wa birnin kawanya...
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama. Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata...
Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai. Daga karshe hukumar...
Hukumar da take kula da hakkin bil’adama ta MDD ta bayyana cewa; Mafi yawancin wadanda yaki ya rutsa da su a Gaza mata ne da kananan yara. Mai Magana da yawun hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Rafina Shamdsani ce ta bayyana hakan a wurin taron hukumar da aka yi a birnin Geneva tana mai kara da cewa; Atsakanin watan Maris zuwa Aprilu na wannan shekara ta 20205 da ake ciki kadan, Isra’ila ta kai hare-hare har sau 224 akan gidajen mutane da kuma hemomin da ‘yan hijira suke ciki. Har ila yau, hukumar ta kara da cewa; suna ci gaba gudanar da bincike akan wasu hare-hare 36 da sojojin Isra’ilan su ka kai da aka tabbatar da ya...
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Sannan kuma jami’in ya yi Allah wadai da tauye hakkin yara da ake yi da gangan a Gaza, ya kuma bukaci masu karfin fada a ji a duniya da su dauki mataki. Ya kara da cewa an toshe alluran rigakafi 180,000 na rigakafin yara masu mahimmanci, da na’urorin saka jariran da ba...
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa. Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya kasar na kashe kudaden yaran kasar da ba a kai ga haihuwarsa ba. “Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kudaden yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kudin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce....
Yara mata kimanin 74,452 ne suka amfana da tallafin kudi karkashin shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) a kananan hukumomi 19 na jihar Kano, wanda ya kunshi rukuni na farko da na biyu. AGILE wani shiri ne na Bankin Duniya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wanda aka kirkira don inganta damar samun ilimin sakandare ga yara mata masu shekaru tsakanin 10 zuwa 20. Shirin yana daukar matakai da dama domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga yara mata, ciki har da gina da gyara makarantu, da bayar da tallafin kudi ga iyalai masu karamin karfi, da yakar al’adu da ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, da karfafa yara mata fasahar zamani, da kasuwanci, da...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa. Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin....
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa. Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan. Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan. Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto ‘yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil’adama bisa nasarar ceto yaran. Ya ci gaba da cewa ta’addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis. Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...