2025-11-03@04:54:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 114
«Coup Yayin da»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
“Gwamna ya fice daga gidan, kuma muna jiran sabon shugaban riko ya iso. “An sauya duka jami’an tsaro, amma komai yana tafiya cikin kwanciyar hankali a yanzu,” in ji majiyar. A halin yanzu, al’ummar Fatakwal na ci gaba da harkokinsu ba tare da wata matsala ba. A ranar Talata ne, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas, sakamakon rikicin siyasa da addabi jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.” Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza. Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu. A lokacin yarjejeniyar, an yi musayar wasu fursunonin Isra’ila da Falsɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila. Sai dai har yanzu kimanin mutum 59 daga cikin fursunonin Isra’ila suna hannun Hamas, kuma ana zargin rabinsu sun mutu. Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta amince da harin da Isra’ila ta sake kai wa Gaza, inda ƙasashen biyu suka sha alwashin yaƙar Hamas, ‘yan tawayen Houthi...
Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Nacewa Ga Samun Ci Gaba Mai Inganci Yayin Ziyararsa A Guizhou
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar LASEMA ta bayyana cewa tawagarta ta fara aikin ceto da bincike tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin agaji. Haka kuma, an tura manyan motocin tono ƙasa don taimakawa wajen share baraguzan ginin da kuma ceto duk wanda ya maƙale a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba. Badr Abdul’adhy, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar Falasdinu gabanin yin taron kasashen larabawa a birnin alkahira. Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya ce; “Hanya daya tilo ta kawo karshen yawan fadace-fadace, shi ne a cusa wa Falasdinawa fatan jin cewa,abinda suke mafarki da shi mai yiyuwa ne a aikace,wanda shi ne kafa ‘yantacciyar kasarsu.” Haka nan kuma ya ce; Shirin da Masar take da shi na sake gina Gaza, mai yiyuwa...
Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
“Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi. Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu. A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga irin jagoranci Babangida a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa. Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya. Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka...
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina. AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuna cewa, an kai harin ta’addanci a wani sansanin PMF da ke cikin al’umma, inda aka ce, ‘yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu da CEC hudu.
Alƙalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aikewa wanda ake ƙara takardar umarni ta wasu hanyoyin sannan ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
Shugaban Max Air reshen Kano, Bello Ramalan, ya tabbatar da cewa duk fasinjoji sun tsira cikin koshin lafiya kuma ya nemi afuwar jama’a kan abin da ya faru. Hukumar binciken hatsarin jiragen sama ta Nijeriya (AIB) na gudanar da bincike kan musabbabin lamarin, wanda ake zaton ya faru ne sakamakon matsalar taya. Max Air ya tabbatar da cewa za ta tallafa wa fasinjoji wajen dawo musu da kayansu yayin da bincike ke gudana.
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Kabiru Bala ya roki Majalisar Dokoki ta kasa da ta yi gyare-gyaren doka don ware cibiyoyin ilimi daga zama hukumomi masu samarda kudaden shiga. Ya yi wannan roko ne a wajen bikin yaya=e dalibai karo na 44 da aka gudanar a dandalin Mamman Kontagora da ke Samaru a Zariya. Shugaban jami’ar ya ce idan haka ta faru, jami’o’in za su mayar da hankali ne a matsayin manyan cibiyoyin kawo ci gaban kasa. Ya yi nuni da cewa Jami’ar Ahmadu Bello kamar yadda jami’o’in Najeriya da dama ke fuskantar kalubalen kudi don tallafa wa manufofinta na ci gaba da zamanantar da ayyukanta. Farfesa Bala ya yi magana ne game...