2025-08-06@12:22:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6168
«Giwa LG»:
Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi. Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku...
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere. A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban...
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki. Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano. Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su...
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu....
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki. Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran...
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yaba da ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya kai a Pakistan, wanda a sakamakon an bude wani sabon shafi na karfafa alaka mai karfin gaske tsakanin Iran da Pakistan da suke makwabtaka da juna. “Ziyarar shugaban kasar Pakistan na da matukar muhimmanci,” in ji Esmaeil Baghaei yayin...

Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69...
Kungiyar Hamas, ta musanta kalaman da wakilin Amurka Steve Witkoff, inda ya yi ikirarin cewa kungiyar ta bayyana aniyar ta na yin watsi da makamanta. Kungiyar ta tabbatar da cewa, tsayin daka da makamanta hakki ne na kasa kuma na shari’a matukar dai an ci gaba da mamaye Falastinu, kuma dukkanin dokoki na kasa da...
Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi da kuma takin zamani kyauta ga al’ummar mazaɓarsa. Da yake ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobin garin Goɗɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, Sanata Buba ya ce, “A bana, za mu yi allurar rigakafin dabbobi 85,000 a wannan yankin na Majalisar Dattawa.” Ya...
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin...
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana. Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk...
Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci...
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira...
Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu...
An nemi wata jaririya saoi kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar da ke shirya jarabawa kammala karatun sakandire a Afrika ta Yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2025, tana mai cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakon nasu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...

Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki,...
An nemi wani jariri sabuwar haihuwa an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririn ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarsa da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin. NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar. Shirin kashe N712bn kan...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a...
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki. “Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more...
Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne...
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai...
Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayar da umarnin bude jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai domin fara gudanar da karatu na yau da kullun. Umurnin sake bude jami’ar ya biyo bayan nazari sosai kan matakan tsaro da inganta ababen more rayuwa a jami’ar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa...
Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da kudurinta na yaki da zaizayar ƙasa, ambaliyar ruwa, da sauran matsalolin da suka shafi muhalli. Wannan bayani ya fito ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin kaddamar da babban shirin dashen itatuwa da za a shuka tsirrai miliyan biyar da rabi a faɗin jihar, wanda aka gudanar a...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari. Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar...
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati. Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta...
Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa. Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara....
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau,...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa. Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji...
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan...