Tafiya Sallah Ta Kubutar Da Shugabannin Kungiyar Hamas Daga Kisan Gillar Gwamnatin Mamayar Isra’ila
Published: 12th, September 2025 GMT
Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha
Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin ta Channel 12 cewa, kwana guda bayan kaddamar da shirin kawar da ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, rahotanni na nuni da cewa harin bai yi nasara ba, sakamakon matakin da shugabannin Hamas suka dauka na yin sallar azahar tare da ficewa daga dakin tattaunawar.
Wani abin ban mamaki shi ne, shugabannin Hamas sun bar wayoyinsu a cikin dakin tattaunawar, lamarin da ya bata leken asirin Isra’ila da cewa har yanzu shugabannin na nan a wurin da aka kai harin.
An kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami 12 da jiragen yaki 15, kuma babban makasudinsa shi ne kashe manyan shugabannin Hamas Khalil al-Hayya, Zaher Jabarin, da Khaled Meshaal.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici September 12, 2025 Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran September 12, 2025 Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa September 12, 2025 Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran September 12, 2025 Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar September 11, 2025 Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci