Sallar Juma’a: MURIC ta nemi a sauya ranar naɗin Sarkin Ibadan
Published: 7th, September 2025 GMT
Ƙungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Kasa (MURIC) ta buƙaci kwamitin shirya bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan da ya soke ranar Juma’a, 26 ga Satumba, da aka shirya gudanar da bikin.
Ƙungiyar ta ce wannan rana za ta iya hana ɗaruruwan Musulmi gudanar da Sallar Juma’a da suke yi a kowane mako.
Shugaban MURIC na ƙasa, Farfesa Ishaq Akintola, ya yi wannan kira cikin wata sanarwa da aka aika wa manema labarai a ranar Asabar.
Farfesa Akintola ya ce sau biyu irin wannan matsala ta taɓa faruwa a baya: lokacin da aka yi bikin miƙa sandar sarauta ga marigayi Olubadan Oba Akinloye Owolabi Olakulehin da kuma lokacin da aka kaddamar da sabuwar hanyar Iseyin zuwa Ibadan — duka a ranar Juma’a, inda aka samu tangarɗa har Musulmi suka kasa gudanar da Sallar Juma’a.
Yadda ’yan Arewa suka yi Maulidin bana a Ibadan Mauludi: Ƙungiyoyin addini sun nemi gwamnati ta sassauta dokar hana hawa babur a GombeYa zargi Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo kan abin da ya kira yunƙurin mayar da ranar Juma’a a matsayin rana ta bukukuwan Kiristoci. Ya ce MURIC ba za ta amince da irin wannan take haƙƙin Musulmi ba.
Saboda haka, ya buƙaci kwamitin shirye-shiryen bikin da ya mayar da ranar Juma’a 26 ga Satumba a matsayin ranar addu’o’in Musulmi domin girmama sabon Olubadan, Oba Rashid Adewolu Ladoja, ko kuma a ɗage bikin zuwa Asabar 27 ga Satumba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Naɗin sarauta Sallar Juma a ranar Juma a
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.