Isra’ila tace Ta Yi Kokarin Kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Yakin Kwanaki 12 Da Kasar Iran
Published: 7th, September 2025 GMT
Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar da cewa ta yi kokarin mai matsayi mafi girma a kasar Iran, wanda kuma ya kasa kaiwa na sarara.
Kazt ya bayyana haka wa tasoshin talabijin ta Chennel 13, Kan da kuma Channel 12, kan cewa sun yo kokari har sau 2 amma bayayan da ke hannummu sun kasa tabbatar da abunda muke nema. Yace da mun sami da mun kasheshi tuni.
Bayanan da gwamnatin HKI ta bayyana a yau, bayani ne mai muhimmanci wanda zai yi tasiri a duk wata karawa da ita nan gaba. Kuma JMI zata kara tanadi na kare Jami’an gwamnatin kasar mafi koli daga mafi sharrin mutane a doron kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Kirayi E3 Su Koma Kan Hanyar diblomasiyya Saboda Wanin Haka Ba Zai Yi aiki Ba September 7, 2025 Iran: Zahra Kiyani Ta Lashe Lambar Zinari A Gasar Wushu A Karon Farko September 7, 2025 Jiragen ‘Drons’ Na kasar Yemen Sun Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Ramon A Isra’ila September 7, 2025 Wilayati Yace, Yenci da Tsaron Kasar Iraki Na Da Matukar Muhimmanci Ga Iran September 7, 2025 NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai September 7, 2025 An Gudana Da Zanga zanga Adawa Da Ziyarar Shugaban Amurka a Kasar Malesiya . September 7, 2025 Za’a Fara Taron Makon Hadin Kai Karo Na 39 A Nan Tehran September 7, 2025 Dubban Mutane ne Suka Gudanar Da Zanga-zanga A Birnin London September 7, 2025 An Rufe Kamfanin Kera Makamai Na Isra’ila Dake Birtaniya. September 7, 2025 Araqchi: Suna Ci Gaba Da Musayar Sakonni Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani September 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje 1,300 a yankin Gush Etzion, kudu da Gabashin Urushalima da ta Mallake, wanda hakan ke nuna wani sabon ci gaba da fadada matsugunai ba bisa ka’ida ba a fadin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
A cewar tashar talabijin ta Isra’ila Channel 14, Kwamitin tsare-tsare da Gine-gine na musamman da ke kula da matsugunan da ke Gush Etzion ya amince da wannan shawara a farkon wannan makon, inda ya shafi unguwar Har HaRusim, wadda ke kusa da matsugunan Alon Shvut, kudu maso yammacin Gabashin Urushalima da aka Mallake.
Shirin bai shafi gidaje ba kawai, har ma da gina makarantu, wuraren jama’a, wuraren shakatawa, da kuma babbar cibiyar kasuwanci da aka yi niyya don yi wa al’ummomin da ke makwabtaka hidima.
Majalisar Yankin Gush Etzion ta yi maraba da wannan mataki, tana mai ganin hakan a matsayin martani ga karuwar bukatar mazauna yankin.
Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake da ita game da ayyukan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.
Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta amince da wasu kudirori biyu da nufin hade Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma yankin Ma’ale Adumim.
Irin wadannan matakai za su ware Gabashin Kudus daga yankunan Falasdinawa da kuma raba Yammacin Kogin Jordan zuwa yankuna biyu daban-daban, don haka za su kawo cikas ga yiwuwar hadewar kasar Falasdinu.
Majalisar Dinkin Duniya da yarjejeniya kasa da kasa sun sha nanata cewa matsugunan Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, gami da Yarjejeniyar Geneva ta Hudu.
Bugu da kari, kungiyar kare hakkin dan adam ta Peace Now ta bayyana shirin E1 a matsayin “mummunan rauni” ga samar da Falasdinu, tana mai jaddada cewa aiwatar da shi zai kawo cikas ga yunkurin kafa kasar Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci