Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar
Published: 12th, September 2025 GMT
A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha babban birnin kasar Qatar, ba tare da ambaton sunan Isra’ila ba. TY kuma jaddada wajabcin daina kai irin wadannan hare-hare da kuma nuna cikakken goyon baya ga ga ‘yancin kasar Qatar.
A nata bangaren, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kwamitin sulhu bayani kan koken na Qatar, inda ta jaddada cewa, harin na Isra’ila ya bude wani babi ne mai hadari a cikin wannan rikici mai muni.
Mataimakin Sakatare-Janar ta kara da cewa “dole ne dukkan bangarorin su dauki matakin kiyaye yunkurin da ake yi na samo hanyoyin tsagaita bude wuta,” tana mai gargadin cewa “duk wani mataki da zai kawo cikas ga tattaunawar yana raunana duk kwarin gwiwa kan hanyoyin da aka dogara da su ne don magance rikice-rikice.”
A nasa Wakilin Rasha a kwamitin sulhun ya ce abin da ya faru a Doha ba wani lamari ne da ya auku ba zato ba tsammani, illa dai hakan sakamakon kawai na rahin hukunta Isra’ila.
Ya kara da cewa Moscow ta yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar Qatar, yana mai gargadin cewa matakin da Isra’ila ta dauka zai haifar da babbar illa ga tsaro da zaman lafiyar duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar September 11, 2025 Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu September 11, 2025 Qatar Ta Bukaci A Gurfanar Da Netanyahu A Gaban Kuliya Don Fuskantar Adalci September 11, 2025 Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba September 11, 2025 Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita September 11, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari Da Makamai Mazu Linzami A Wasu Yankuna Na Yamen September 11, 2025 Shugaban Najeriya Ya Bada Da Umarnin Karya Farashin Kayan Abinci September 11, 2025 Iran Tayi Tir Da Harin HKI A Yamen Da Kuma Kashe Yan Jarida September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Qatar Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura.
An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin.
Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma.
Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai.
Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama.
Tun daga watan Oktoban 2023, hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza sun kashe a kalla Falasdinawa 64,964 tare da jikkata sama da 165,312, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Yayin da ake fargabar wasu dubbai na karkashin baraguzan gine gine.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci