Araghchi ya caccaki kasashen Turai kan yin biris da cin zarafin Amurka da Isra’ila kan Iran
Published: 12th, September 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku suka dauka na yin biris da batun harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran a baya-bayan nan, da kuma barazanar da suke yi na maido da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka soke, lamarin da yake ganin zai kara ta’azzara halin da ake ciki.
Araghchi ya bayyana hakan ne a daren Alhamis a wata tattaunawa ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres. Ya jaddada aniyar kasar Iran na kare hakki da muradun al’ummarta bisa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kasashe mambobinta da su yin da Allawadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan cibiyoyinta na nukiliya.
Da yake karin haske kan tsarin hadin gwiwa na Iran wajen yin cudanya da hukumomin kasa da kasa, Araghchi ya yi la’akari da shawarwari masu ma’ana da nufin cika wajibcin kiyaye tsaron kasar Iran, musamman ma dangane da cin zarafi na baya-bayan nan da kuma keta hurumin kasar da aka yi.
Ya jaddada muhimmanci kan kasashen Turai da mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya su amince da ci gaba da warware lamurra ta hanyar diflomasiyya.
Araghchi ya kuma yi tsokaci kan halin kunci a bangaren ayyukan jin kai da ake fama da shi a Falasdinu, inda ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa tare da bayyana hakan a matsayin wani abin damuwa a duniya.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada wajabcin aikin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya da kuma MDD ciki har da babban sakataren MDD, na dakile irin wannan ta’addanci da kuma magance bala’in da ke faruwa a Gaza.
Ya kuma yi Allah wadai da harin ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wa Qatar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Venezuela ta yi gargadi game da karuwar sojojin Amurka a cikin tekun Caribbean September 12, 2025 Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar September 12, 2025 Al-Houthi: Sakamakon samun goyon baya Isra’ila tana ci gaba da aikata laifuka a yankin September 12, 2025 Kasashen Iran da Tunisiya sun amince da fadada alaka yayin da FM Araghchi ya ziyarci kasar Tunisiya September 12, 2025 Rundunar Sojin Iran Ta Bayyan Cikekken Goyon Baya Ga Kasar Qatar September 11, 2025 Shugaban Iran Yace Makiya Suna Son gwara Kan Musulmi Don Sace Arzikinsu September 11, 2025 Qatar Ta Bukaci A Gurfanar Da Netanyahu A Gaban Kuliya Don Fuskantar Adalci September 11, 2025 Hamas Ta Ce Hare-Haren Isra’ila A Doha Ba zai Sauya Kome A Gaza Ba September 11, 2025 Iran Tace IAEA Ta Amince Da Sabuwar yarjeniya Da Ita September 11, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari Da Makamai Mazu Linzami A Wasu Yankuna Na Yamen September 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yi Allah wadai da Araghchi ya da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.