Kasar Iran Ta Ce; Ta’addancin Isra’ila Kan Qatar Laifi Ne Da Ke Barazana Ga Tsaro Da Zaman Lafiya
Published: 10th, September 2025 GMT
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan kasar Qatar laifi ne da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya
Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kakkausar murya ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan kasar Qatar, tana mai jaddada cewa, harin da aka kai kan tawagar kungiyar Hamas da ke tattaunawa da kuma janyo shahadan Falasdinawa da ‘yan Qatar, babban laifi ne da kuma keta dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, wannan harin ta’addanci na nuni da cewa, cin zarafi ne da keta ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya, da kuma ka’idojin dokokin kasa da kasa, gami da muzanta hurumin kasar Qatar a fili. An yi nuni da cewa, hakan na nuni da irin hatsari da ta’addancin yahudawan sahayoniyya yake da shi, wanda baya ga laifukan kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye, tana kuma kara fadada ayyukan wuce gona da iri a yankin baki daya, lamarin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin da na kasa da kasa ta hanyar da ba a taba ganin irinsa ba.
Sanarwar ta jaddada cewa, Amurka da sauran kasashen da ke goyon bayan ‘yan sahayoniyya a siyasance, da kudi da kuma na soja, abokan tarayya ne a cikin laifuffukan wannan gwamnati, kuma wajibi ne su dauki nauyin wannan cin zarafi da keta haddi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Farkon Martanin Gwamnatin Siriya Kan Tofin Allah Tsinen Harin Da Isra’ila Ta Kai Kan Yankunan Kasarta September 10, 2025 Mahangar Imam Khamenei: Mummunar manufar Amurka ce tasa tattaunawa da ita ba ta da amfani September 10, 2025 Me yasa za mu je Gaza a cikin jiragen ruwa na tawagar “Sumoud” na duniya? September 10, 2025 Aragchi Ya Gana Da Grrosi da Kuma Takwaransa Na Kasar Masar September 9, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari Kan Jagororin Hamas A Doha September 9, 2025 Kasashen Larabawa Da Na Duniya Sun Yi Allawadai Da Harin Isra’ila Doha September 9, 2025 Iran Ta Yi Watsi Da Zarge-Zargen Kasashen Larabawa Game Da Tsibiran Kasar A Tekun Farisa September 9, 2025 Iran Da Masar Sun Tattauna Kan Gaza Da Shirin Iran na Nukiliya September 9, 2025 Isra’ila Ta Kai Hare-hare A Wasu Wuraren Soji A Kasar Siriya September 9, 2025 Hamas Ta Yi Tir Da Gazawar MDD Kan Kisan Kare Dangin Isra’ila A Gaza September 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje, da masu goyon bayanta na yankin suka aikata a El Fasher da kuma sauran wurare a cikin Sudan.
Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaro da ya sanya takunkumi mai tsauri ga dukkan kasashe da daidaikun mutane da Majalisar ta sani wadanda ke bayar da kudi ga RSF, samar mata da makamai, ko samar mata da mafaka, sannan a fara bincike kan kisan kiyashin da ake yi wa mazauna El Fasher don ci gaba da kokarin daukar mataki. Ya kara da cewa “‘yan bindiga suna yin barazanar kashe mutane a kullum rana ta Allah.”
Wakilin na Sudan ya yi kira da a tabbatar da an aiwatar da kudurorin Majalisar Tsaro na 2736 da 1591, “kamar yadda shaidu a Darfur suka tabbatar da cewa wasu ƙasashe maƙwabta sun shiga cikin kisan fararen hula don tallafawa ‘yan bindiga.”
Bugu da ƙari, Al-Harith ya yi kira da a goyi bayan taswirar da gwamnatin Sudan ta gabatar wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta dogara ne akan dakatar da yaƙi na dindindin da kuma kwance damarar makamai na ‘yan bindiga, sannan kuma su mika wuya.
Idris ya fayyace cewa ba za a yi tattaunawa da RSF ba har sai sun ajiye makamansu su kuma sun daina kai hari kan al’ummar Sudan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci