2025-11-03@07:08:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«Abdurrahman dan Auf»:

    Rahotanni sun bayyana cewa Ƴan ci rani 40 daga kudu da saharar Afrika sun mutu, sakamakon  kifewar kwale-kwale a kasar Tunisia, sai dai  an samu nasarar ceto wasu mutum 30. Kakakin ofishin masu gabatar da kara a Tunisia Walid Chtabri ne ya tabbatar da kifewar kwale-kwalen dake dauke da mutane 70 ‘yan kudu da saharar Afrika a Tunisia. Walid ya ce an gano gawarwakin ƴan ciranin 40 ciki har da jarirai, yayin da aka ceto mutane 30 da ransu, kuma dukkaninsu daga kasashen kudu da sahra suka fito. Gabar ruwan Tunisia na da nisan kilomita 145 tsakanin ta da tsibirin Italiya na Lampedusa, inda ya zama hanyar da dubban ƴan cirani ke amfani da ita wajen tsallaka wa zuwa Turai...
    Ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Najeriya (NRCS), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Italiya, ta kafa cibiyoyin Rage Haɗurran Bala’o’i (Disaster Risk Reduction – DRR) a makarantun sakandare guda biyu a Jihar Gombe, domin inganta shirye-shiryen kare kai daga bala’o’i da kuma ƙarfafa juriya a tsakanin matasa. Makarantun da suka amfana da wannan shiri su ne Ƙaramar Sakandaren Gwamnati ta Pilot da kuma Sakandaren Gwamnati ta Comprehensive, Deba. NLC ta sa zare da gwamnati kan yajin aikin ASUU An maka mahaifi a kotu kan cefanar da gidan ɗansa a Kano A yayin bikin ƙaddamar da cibiyoyin, ƙungiyar Red Cross ta raba kayan karatu da suka haɗa da jakunkuna masu ɗauke da bayanai kan DRR, littattafan rubutu, alƙalumma da kayan lissafi...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da Suka Kashe Malamin Jami’a October 20, 2025 Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Manyan Labarai Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi October 19, 2025
    Hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano ta sanar da fara aiki a hukumance da sabon kwamandan hukumar, Kwamanda Idris Mohammed Lawal.   Kwamanda Lawal ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta Kano ne biyo bayan tura shi da hukumar FRSC ta yi a ranar 3 ga watan Oktoba.   Ya gaji kwamandan Corps MB Bature, wanda ya yi ritaya a kwanan baya bayan ya kamala shekarun sa a aikin gwamnati.   Kafin sabon mukamin nasa, Lawal ya taba zama shugaban aiyuka na shiyyar a hedikwatar hukumar FRSC shiyya daya da ke Kaduna.     A jawabinsa na farko, sabon Kwamandan sashin ya nuna godiya ga rundunar Corps Marshal da Hukumar FRSC bisa amincewarsu. Ya yi alkawarin sadaukar da aikin...
    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
    Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na kimanin kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da Tinubun ya samu. “A yau, ga shi mun taru, domin yin nazari a kan waɗancan alƙawuran tare kuma da tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, abubuwan da muka samu su ne; sauye-sauyen da aka samu duk kuwa da irin ƙalubalen da ake fuskanta a wannan ƙasa. Wannan na nuna cewa, demokuraɗiyyarmu za ta...
    “Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi. Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar. “Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin...
    Mataimakin limamin Jumma’a a nan Tehran Sheikh kum Hujjatul Islam Kazen Sadiki bayan yayio Magana a kan al-amuran tsaron All..da kuma yadda bayin All..da kuma shidanun mutane zasu mutu da kuma yadda sakamakon ko wannansu a gaban All…/ Ya kuma ya gamanar fatahin garin KharramShahr dake kudancin kasar Iran kuma kan iyaka da kasar Iran, wanda dakarun kare juyin juya halin musulunci tare da sauran sojoji da mayakan sa kai suka kwace wannan garin daga hannun sojojin Sdam Hussain a rana irin ta yau wato 2 ga watan Khordod. Banda haka lamamin yana Magana kan littafan da aka buga dangane da wannan gagarumin fatahin da mutanen Iran suka sami a kan wannan garin. Wanda kuma daga wannan nasarar ne ta...
    Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN).   Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamatin, Ministan Sufuri, Sanata Said Alkali, ya jaddada muhimmancin shawo kan kalubalen hadurran da ke ci gaba da barazana da haddasa munanan asarar rayuka da dukiyoyi.   Alkali wanda ya jaddada bukatar a gaggauta kawo karshen wannan mumunan lamari, ya bai wa kwamitin mako guda ya gabatar da rahotonsa, inda ya jaddada cewa, tsaro da inganci su ne kan gaba a cikin manufofin gwamnatin Bola...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin  kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
    Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man.   “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha.   An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
    Hujjar mu a nan ita ce, kundin tsarin mulkin Nijeriya, sama yake da kowanne dan kasar da kuma sauran dokokin kasar, duba da cewa, kundin ya bayar da damar a yi Shari’ar a bisa adalci kuma a bayyane, ga wadanda ake tuhumar da aikata laifi. Bugu da kari, dole ne mu tuhumi matakan da mahukuntan kasar suka dauka na yiwa wadanda ake tuhumar Shari’ar a, asirce. Akwai dimbin tambayoyi a zukatan ‘yan Nijeriya wanda kuma suke bukatar amsa, misali, a ina ne aka cafke su? ta yaya ne, aka kama su? yaushe ne, aka gurfanar da su, a gaban Kotu? Shin an barsu sun dauki Lauyoyin da za su tsaya masu gaban Kotu? har tsawon wanne lokaci ne, suke ci...
    Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa. Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci. Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa. Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu...
۱