2025-09-18@08:34:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 108
«hadar kayayyaki»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, kuma ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a shekaru takwas a jere. A shekarar 2024, an fuskanci karuwar rashin tabbas da rashin zaman lafiya a waje, duk da haka hukumar kwastam ta samar da hidimomi mafi kyau domin saukake da sa kaimi ga inganci da daidaiton yawan...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
“Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in ji sanarwar. Tabbas! abin da manoman suka fada gaskiya ne, domin ko a shekarar 2018, karin harajin da Amurka ta kakkaba a kan kayayyakin kasar Sin, ya janyo kasar ta Sin wadda a baya ita ce ta fi shigo da wake na Amurka, ta sanya karin harajin kashi 25 cikin 100 na ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa. Kuma a yanzu ma, Sin...
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar Sin ta ce za ta kai kara ga kungiyar WTO, gami da daukar matakan da suka wajaba wajen kare moriyarta. A ganin kwararru masu nazarin al’amuran duniya, dalilin da ya sa sabuwar gwamnatin kasar Amurka daukar matakin nan na sanya karin haraji shi ne domin neman tilastawa sauran kasashe su biya kudi, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sassanta matsalar tattalin arziki da...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor. Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu. Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Mota Ta Kwace A Legas Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya...
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.55, shekaru 8 a jere ke nan ana samun wannan ci gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....