2025-11-21@23:04:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11826
«bunkasar tattalin arzikin»:
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci saboda yawaitar sace-sacen ɗalibai da malamai a Najeriya. Atiku, ya yi wannan kira ne bayan harin da “yan bindiga suka kai yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Maharan sun sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic. Har yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba. Harin ya auku ne bayan sace ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka a Ƙaramar Hukumar Maga, a Jihar Kebbi, lamarin da ya nuna yadda rashin tsaro ya...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci. Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa A ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya. Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a. Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa Sakkwato, sun nesanta shi da...
Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare. Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta “An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris. Ya...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa. Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure. Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis...
Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja Mai magana da yawun rundunar a jihar, Bright Edafe, ya ce ’yan sanda sun samu ƙorafi a kan faston bisa zargin lalata, fyade da cin zarafi. Ya ce a ranar 17 ga watan Nuwamba, an kama wanda ake zargi a harabar cocinsa. Edafe...
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar. Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a. ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Shugaban Sashen bayar da Agaji na Ƙaramar Hukumar, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula, amma bai bayar da cikakkun bayani ba. Sai dai a cikin wata sanarwa, Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Abubakar Usman, ya ce bayan samun bayanan sirri tun da farko, gwamnati ta bayar...
’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar. ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Wata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin. Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu. Sakataren cocin, Josiah...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru. Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba. Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al’umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban. Ya kuma ce...
Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya. Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya ƙunshi ’yan majalisa da masu kare hakkin dan’adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula. An shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet. Masu magana a wajen sun haɗa...
Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace. Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba. Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani...
Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka sace a cocin. Shugaban al’umma kuma Olori Eta na Eruku, Cif Olusegun Olukotun, wanda mutane huɗu daga cikin danginsa suka kasance cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida. Olukotun ya ce yana cikin coci tare da mutane biyar na danginsa lokacin da lamarin ya faru, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin yaran da yake kula da su ya tsere...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar a Kano, wanda Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta shirya. Haka zalika ɗaliban sun nemi a mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci. Haka kuma, sun buƙaci a aiwatar da dokokin kare haƙƙin yara tare da ba da dama ga daidaito tsakanin jinsi, musamman a fannin ilimin ’ya’ya mata. Bugu da ƙari, sun koka...
Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bai wa Jihar Kaduna, musamman wajen ci gaban harkokin noma da sarrafa amfanin gona. Ya ce kafa Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da African Quality Assurance Centre (AQAC) ya ɗaga martabar jihar a matsayin jagora wajen ci gaban sarkar samar da kayayyakin noma da kuma faɗaɗa damar fitar da su ƙasashen waje. Shugaban Ƙasa ya yaba da wannan...
Daga Khadijah Aliyu Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu samari bakwai da ke shiga irin ta mata da aikata badala a wani shahararren gurin nishadi da ke kan titin Zoo Road a karamar hukumar Kano Municipal. Yayin tabbatar da faruwar lamarin ga Rediyon Nijeriya, Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, ya ce an kama samarin da ke kasa da shekaru 23 bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa. Mai bayar da bayanan ya sanar da cewa mmatasn da aka fi sani da ‘Yan Daudu, suna yawan zuwa wurin, inda ake zargin cewa motocin mutane daban-daban ke zuwa su ɗauke su. Sheikh Mujahid ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa matasan sun...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin tallafin hadin gwiwa na kowace shekara domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwo na Gargajiya ta Afirka (CORET) tare da haɗin gwiwar ECOWAS sun hada matasan da aka horar da su da manyan abokan holda don bunkasa kiyo da bunkasa yawan madara a jihohin Kaduna da Jigawa. A yayin zaman karawa juna sani a Kaduna, Koodinetan Aikin na CORET Dr. Umar Ardo Abdul, ya ce an shirya wannan zama ne domin haɗa matasan da aka horar da su da masu ruwa da tsaki a harkan kiyo da bunkasa yawan madara na gwamnati da masu zaman kansu, domin a horas da su hanyoyin samun aikin yi da kuma bunkasa yawan madara. Wannan shiri na daga cikin Aikin ECOWAS na karfafa samar da ayyukan yi ga matasa...
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin. BBC
Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar da sunayen sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar matasa, wanda hakan ya ƙara yawan ma’aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin. Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta mayar da tsohon mataimakin firaministan ƙasar kuma ministan makamashi, Dotto Biteko da tsohon shugaban majalisar ƙasar, Tulia Ackson ba. Sai dai hankali ya fi karkata ne kan naɗin ƴar shugabar ƙasar, Wanu Hafidh a matsayin mataimakiyar ministar ilimi, sannan ta naɗa surikinta, Mohamed Mchegerwa a matsayin ministan lafiya a cikin sababbin ministocin. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugabar ƙasar ta kafa kwamitin bincike...
Daga Khadijah Aliyu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 1, irinsa na farko a tarihin jihar. Za a gabatar da kudurin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamban 2025. Wasiƙar, wadda Kakakin Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya karanta a zaman majalisar, ta bayyana cewa gabatar da kasafin ya yi daidai da sashe na 121 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, wanda aka yi wa gyara. Gwamna Yusuf ya bayyana cewa yawan kasafin da ya karu sosai na nuna ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen sabunta birane, da haɓaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a...
Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani. A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, CSP Nafi’u Abubakar Kotarkoshi ya sanya wa hannu, maharan ɗauke da makamai masu ƙarfi sun kutsa makarantar inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke bakin aiki. Duk da ƙoƙarin jami’an, an ruwaito cewa maharan sun haye katangar makarantar suka kuma yi awon gaba...
Shugaban kasar rasha vladmir putin ya bayyana cewa ba zamu ja baya daga ayyukan soji da muke yi a kasar Ukrain ba, bayan rahoton da fadar kremlin ta fitar dake nuna cewa dakarunta sun kutsa cikin kasar ukrain suna kusa da birnin Kupiansk mafi mahumimmanci a kasar A loakcin ziyara da babban kwamanda kasar rasha ya kai a wajen da ke cikin yakin Ukrain putin yace yanzu haka dakarun rasha sun kewaye rundunoni 15 na kasar Ukrain a garin Kupiansk, za su bada dama ga sojojin kasar su mika makamansu kuma su yi saranda Kakakin fadar kremlin Dmitry peskov ya fadi cewa putin ya karbi rahoto game da karbe kula da ikon garin Kuoansk . Wannan bayani yazo ne bayan...
Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyan cewa yanayin da yankin sahel da sauran kasahen dake makwabtaka da shi kullum yana kara yin tsananin sosai, kamar kai hare-haren ta’addanci da kuma matsalar da ta shafi mai a kasar mali suna mummunan tasiri a yankin. Haka zalika yayi gargadin cewa kungiyoyin masu iykirarin jihadi masu yankurin kafa daular musulunci a yankin sahara ISGS...
Rahotanni daga birnin Tehran sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadawa masana tattalin arziki cewa Tehran a shirye take na yi duk wata yarjejeniya idan dai za’a tsage gaskiya, kuma iran ta kara karfafa dakarunta wajen kasancewa cikin shirin ko ta kwana musamman ma bayan yakin kwanaki 12 da aka kallafa mata. Wadannan kalaman sun nuna kyakkyawar niyar iran na tattaunawa sai dai bata yarda da shirin Amurka na tattaunawa kai tsaye ba, bugu da kari dabarun siyasar iran shi ne ta amince da bin hanyoyin diplomasiya amma kuma tana ci gaba da nuna adawrta ga isra’ila Janyewar da Amurka ta yi a yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 tasa an shiga zaman dar-dar don...
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta. Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun zarta iyakar aka yi...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yarjejeniyar Alkahira tsakanin Iran da IAEA ba ta da inganci Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Iran ta sanar da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) cewa: Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar, yana mai nuni da cewa yarjejeniyar ta rasa rawar da take takawa a matsayin tsarin hadin gwiwa tsakanin Iran da IAEA. Da yake mayar da martani ga kudurin da kwamitin Gwamnonin IAEA ta dauka kan Iran, Araqchi ya ce: “Sun sanar da IAEA cewa Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar.” Ministan harkokin wajen Iran ya kara da cewa: “Yarjejeniyar Alkahira ta rasa rawar da...
Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale. Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara a 2027 — NNPP Za a aurar da marayu 200 a Zamfara “Matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin ta shafi Musulmi da sauran al’ummomi baki ɗaya,” in ji shi. Fafaroman ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a lokacin da yake barin gidansa na Castel Gandolfo a Vatican, inda aka tambaye shi...
Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar da ke Gusau. Ya ce an gudanar da cikakken bincike da tantancewa kafin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin, domin tabbatar da cewa auren ya kai ga mutanen da suka fi buƙatar taimako na haƙiƙa. Sakataren ya ƙara da cewa, hukumar za ta ba wa amaren kayayyakin tallafi da kayan amfani na gida domin taimaka musu su fara sabuwar rayuwarsu cikin sauƙi da kwanciyar...
Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU. IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Aminiyar ta ruwaito cewa, ɗaliban sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai da shugabannin ƙungiyar a jami’o’in Bayero da kuma North West —Mudassir Adamu Musa da Asahabulkhair Labaran Usman —suka jagoranta. Ɗaliban sun bayyana cewa yajin aikin da ƙungiyar ASUU...
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka. Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta. An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci A cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi. Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da...
Ministan wuraren tarihi da yawon bude ido da sana’o’in hannu na iran Sayyid Ridha Salihi Amiri ya bayyana cewa: A Halin yanzu Iran tana da wuararen tarihi 20 da ake yi gani, da kuwa wasu 28 da suke a karkashin hukumar dake kula da kayan tarihi ta MDD ( Unesco). Ministan na Iran wanda ya ziyarci wani wurin tarihi a garin Zanjan a yau Alhamis, ya yi Ishara da muhimmanci shigar da wuraren a karkashin hukumar dake kula da kayan tarihi ta duniya. Haka nan kuma ya bayyana cewa da akwai wasu wuraren na Iran da nan gaba za a yi rijistarsu a karkashin hukumar Unesco ta MDD. Idan kuwa aka yi hakan, to za ta zama ita ce ta...
A zana da kotun ta yi a birnin Abuja a yau Alhamis, mai shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin cewa mai shigar da kara ya gabatar da kwararan dalilai akan yadda jawaban da Kanu ya rika watsawa su ka ingiza mambobin haramtacciyar kungiyar ” IPOB” su ka kai wa jami’an tsaro hari a yankin kudu maso gabashin kasar. Mai shari’ar ya bayyana Kanu a matsayin wanda ya shirya ayyukan da su ka kai ga yin ta’addanci. A 2009 ne dai Kanu ya fara watsa shirye-shiryen Rediyo Bi’afara daga London, da yake Magana da ‘yan kungiyarsa ta IPOB. Tun da fari dai Alkalin ya bayar da umarnin a fitar da Nnamdi Kanu daga cikin kotun sabdoa abinda ya kira rashin da’a...
Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da makamai da suke karakaina a yankin. Gwamnatin ta Kwara ta dauki wannan matakin ne bayan wani lokaci kadan daga kustawa cikin wata majama’a da masu dauke da makamai su ka yi a Eruku dake karamar hukumar Ekiti. Mazauna yankin dai sun fada cikin frigici da razana haka nan kanan hukumomin da suke makwabtaka. An bayar da umarnin a rufe makarantun kwana na Irepodun saboda rahotanni...
Mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hizbullah Mahmud Kumadhi ya bayyana cewa: Bayan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kasa murkushe gwgawarmaya a Falasdinu, yanzu ta kuma kai wa kudancin Lebanon hare-hare. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto Mahmud Kumatiy ana cewa; Abinda ‘Yan mamaya suke yi, shi ne kokarin shimfida ikonsu a cikin wannan yankin na yammacin Asiya baki daya, sai dai hakan ba za ta faru ba. Muhammad Kumadhi ya kuma jaddada cewa; ko kadan Hizbullah ba za ta taba ajiye makamanta ba, ko kuma ta kauce daga kan godaben gwagwarmaya komai tsananin matsin lambar Isra’ila.” Mataimakin shugaban ofishin siyasa na Hizbullah ya kuma ce; Hzibullah kungiyar gwgawarmaya ce ta kasar Lebanon, kuma ta musulunci,aikin da yake...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara. Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas. Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa...
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Lamarin ya faru kasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30. Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin waɗannan hare-haren. Ɗaya daga cikin...
Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin. Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin. Sai dai yayin da ake tsaka da bikin,...
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta. An fitar da wannan sanarwa ce a shafin x na micheal achimugu daraktan kula da hulda da jama’a da kula da fasinjoji, ya kara da cewa wannan hukumci ya sanya adadin kamfanonin jiragen sama da aka ci tara sun kai guda 7 a wannan shekarar ta 2025 Hukumar NCAA ta zargi kamfanin jiragen sama na Qatar airways a watan satumban shekarar da muke ciki da take dokokin kula da...
a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila ya kashe a harin na jiya laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana bayan mutane akalla 77 da suka jikkata, Hamas ta karyata zargin cewa dakarunta ne suka fara bude wa sojojin Isra’ila wuta da ya kai ga sun kai harin, kungiyar ta bayyana zargin a matsayin shaci fadi, kuma isra’ila tana son fakewa da shi ne don kare hare haren da...
Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da kara a hukumance ga majalisar dinkin duniya. Wannan bukata ta zo ne adaidai lokacin da sojojin Isra’ila suke kai hare hare kan fararen hula dake jawo asarar rayuka, kuma yake jawo fargaba game da ci gaba da hara-haren israila na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai lamba 1701, Isra’ila ta kai hare hare a lokuta daban daban a kudancin labanon kuma yayi sanadiyar mutuwar...
An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar, Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi adaidai lokacin da kasashen musulmi suke fuskantar matsalolin aladu da tasirin kasashen yamma a tsarin zaman takewarsu da tashe tashen hankula na siyasa musamman ma kan yankin falasdinu. Kasashen biyu suna da matsaya daya na dogon lokaci a bangaren abincin Halal, aladun musulunci da kuma ilimin Addinin, don haka wannan tattaunawar da aka yi an sake sabunta alakar ne bisa ababen girmama wa na musulunci da...
Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu. Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha. “Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini...
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran wani ma’aikacinsu, HFS Abba Datti, game da gobarar. A cewarsa ba tare da ɓata lokaci ba suka tura jami’ansu daga hedikwatar hukumar zuwa wajen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su. NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda Isra’ila ta yi wa kisan gilla. Sojojin Isra’ila sun kuma tabbatar da kai hari kan al-Mawasi a Khan Younis, kudancin Gaza. Isra’ila ta kai hare-hare uku daban-daban a birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa da kuma kudancin Khan Younis, a cewar hukumar Falasdinawa. Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare 393, inda suka kashe akalla Falasdinawa 290 tare da raunata...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne. Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.” Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi...
Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman ma game da rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kwamishinan harkokin siyasa, da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta AU Bankole Adeoye, ya ce dole ne kungiyar ta AU ta jagoranci duk wata tattaunawa ta zaman lafiya a nahiyar, yana mai jaddada muhimmancin amfani da ka’idojin warware rikicin Afirka a bisa tafarkin Afirka. Adeoye ya kara da cewa, “Mu a matsayinmu na kungiyar Tarayyar Afirka, ba mu yarda...
Kamfanonin labarai na Reuters da AFP sun rawaito cewa Amurka ta shawarci Ukraine ta amince da Crimea da sauran yankunan da Rasha ta mamaye mata da kuma rage girman sojojinta zuwa rabi kamar yadda yake kunshe a sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. Ukraine ta sami sabuwar, wacce ke bukatar Kiev ta mika yankunan dake karkashin ikon Rasha da kuma rage yawan sojojinta zuwa 400,000 kamar yadda jami’an Amurka da aka sakaya sunansu suka shaida wa Reuters da kamfanin dillancin labarai na AFP. Shirin ya kuma tanadi Ukraine ta mika dukkan makamai masu kaiwa nesa. Bayanai sun ce da alama shirin ya maimaita sharuddan Rasha wadanda da Ukraine ta sha watsi da...
Sudan ta yaba da kokarin zaman lafiya da Amurka da Saudiyya suka yi na dakatar da zubar da jini a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, Majalisar Mulkin Sojan Sudan ta yi maraba da “kokarin Saudiyya da Amurka na kawo zaman lafiya mai ga Sudan.” Ta gode wa Washington da Riyadh saboda “sha’awarsu da kuma ci gaba da kokarinsu na dakatar da zubar da jinni a Sudan” kuma ta tabbatar da shirin Sudan na yin tattaunawa da kasashen biyu “don cimma zaman lafiyar da al’ummar Sudan suka dade suna jira.” Wannan sanarwar ta zo ne jim kadan bayan da Shugaba Donald Trump ya ce Amurka “za ta fara dubi lamarin Sudan” bisa bukatar Yarima Mohammed...
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO) cewa ba zai kare kambunsa a kan Wardley ba. Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal WBO ta tabbatar da cewa Usyk “ya zaɓi ya ajiye kambun ne saboda wasu dalilai da suka gamsar da hukumar.” A halin yanzu, Usyk na ci gaba da riƙe kambuna uku: WBA, WBC da IBF,...
Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.
Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao. Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta. An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani...
Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba. Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba. Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa Kwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Aminiya a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.706, ta wani mutum ce da suke zaman haya a daya daga cikin dakunan gidansa. Ma’auratan sun shaida...
Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu a wasan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta doke Najeriya. Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari A yau Laraba ne Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) za ta sanar da sunayen gwarazan ‘yan wasan nahiyar na shekarar 2025, a yayin babban bikin da za a gudanar a Morocco. Za...
Matsayar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta dauka kan tattaunawa da Amurka Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da Amurka. Ya yi nuni da cewa: Babu wata hujja mai ma’ana ta tattaunawa da wani bangare da ke neman ta tsara sharuddansa kan Iran, yana mai cewa wasikar Shugaba Pezeshkian ga Yariman Saudiyya ta kasance ta biyu kawai kuma ba ta da alaƙa da ziyarar da ya kai Amurka. Da yake amsa tambaya a ranar Laraba game da ikirarin Shugaban Amurka na ranar da ta gabata game da tattaunawa da Iran, Baqa’i ya ce, “A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da...
Wani masani harkar tsaro da dabarun yaki ya ce: Babu wata kasa a yankin da ke da makamai masu linzami irin na Yemen, sai kasar Iran kawai Kwararren mai kula da harkokin tsaro da dabarun yaƙi Laftanar Janar Abdul Karim Khalaf ya bayyana takamaiman makamin “Mayun” na Yemen, wanda aka sanya wa sunan ɗaya daga cikin tsibiran Yemen mafi mahimmanci a tsakiyar mashigar Bab al-Mandab. Sanarwar tasa ta zo ne bayan nasarar gwajin fili da aka yi wanda ya girgiza sojojin ƙasashen waje a Tekun Red. Khalaf ya bayyana cewa makamin shine makamin farko mai cin dogon zango na Yemen, wanda ke da ikon yaƙi daga sama zuwa teku, daga teku zuwa teku, tare da cin nisan kilomita 1,000. Yana...
Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya {IAEA} ya bayyana cewa: Suna tuntubar Tehran kuma masu binciken hukumar sun koma kasar ta Iran Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya tabbatar da komawar masu binciken Hukumarsa ta IAEA zuwa Iran da kuma ci gaba da duba wasu wurare da ba su lalace ba. Ya lura cewa yana ci gaba da tuntuɓar mahukuntan Iran kuma ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa don ci gaba da duba cikakkun bayanai, musamman a wuraren da aka kai hare-haren soji a kwanan nan. A cikin rahotonsa ga kwamitin Gwamnonin a taronsu na yau da kullun, Grossi ya bayyana cewa masu binciken Hukumar IAEA sun koma Iran kuma...
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400 Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan laifukan sun shafi rayukan fararen hula kai tsaye, da nufin tsoratar da su da kuma fadada barna, ta haka ne ke kara ta’azzara yanayin jin kai da kuma barazana ga makomar kwanciyar hankali. Al-Thawabta ya kara da cewa, a cikin sanarwar da ya bayar ga Al Jazeera Net, cewa: Yanayin jin kai a Gaza yana kara muni tare da rugujewar tsarin lafiya da kuma rufe...
An yanke wa abokan aikin ɗan tsohon shugaban kasar Gabon hukuncin ɗauri a gidan kurkuku Kotun Hukunta Laifuka ta Musamman da ke Gabon ta yanke hukuncin ɗauri a gidan kurkuku daga watanni 26 zuwa shekaru 15 ga tawagar abokan Nouruddine Bongo, ɗan tsohon shugaban ƙasa Ali Bongo, a shari’ar da aka fi sani da “Tawagar Matasa”, wacce ke da alaƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma satar dukiyar gwamnati. Bayan dogayen zaman shari’o’i da aka kammala a safiyar ranar 18 ga Nuwamba, 2025, kotun ta yanke wa Iyan Ghislain Ngolo, tsohon darektan ofishin Nouruddine Bongo, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari, tare da dakatar da shekaru biyar, bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da satar dukiyar jama’a, cin...
An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane. Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su...
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU). Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron G20 karo na 20 da kuma Taron AU-EU karo na bakwai. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba. “Shugaban ƙasa ya umarci sojoji da ’yan sanda da su aike ƙarin jami’ai zuwa waɗannan yankuna domin a tabbatar...
Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
Shugabar kasar maziko Claudia shinbaum ta fadi a cewa kasarta ta yi watsi da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen wajen da kuma kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na kai harin soji kan iyakar kasar. A farkon makon nan ne trump yace yana so ya umarci sojoji su kaddamar da wani samame a kasar meziko domin yakar masu fataucin miyagun kwayoyi, yace wata dama ce gareshi ya aiwatar da wannan aiki don haka zai yi duk abin da ya dace wajen ganin an kawo karshen masu fataucin miyagun kwayoyi a yankin. Da aka tambayeshi ko zai nemi izinin kasar Maziko, sai yace ya riga yayi Magana da jami’an gwamnatin meziko sai dai basu gamsu da kokarinsa ba, amma...
Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza domin tabbatar da zaman lafiya, ta yi gargadin kada ayi amfani da shi wajen take hakkokin alummar falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kai A wani bayani daya fitar tun a ranar talata ma’aikatar harkokin wajen iran ta ce kudurin da aka amince da shi ya manta da ainihin rawar da majalisar dinkin duniya za ta taka da kuma kudurinta na baya da ya shafi yankin falasdinu. Kuduri mai lamba 2803 an amince da shi ne a ranar litinin da ta gabata inda ya bukaci kafa dakarun...
Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa cikin makarantar, sai suka shigo cikin gidansu. Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas HOTUNA: Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Matar ta ce ba ta san cewa mutane ne a bakin ƙofar ba sai da suka shigo cikin ɗakinsu. “Da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba a ranar Litinin muna kwance ni da mijina sai muka ji ana ƙoƙarin karya ƙofar dakinm. Na...
pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman lafiya. Bayanin karshe na taron da mamabobin kungiyar suka fitar ya yi tir da adawa da kasashen yamma ke nunawa kasar iran da ya shafi takunkumin karya tattalin arziki da ya sabama dokokin kasa da kasa , shuwagabannin sun yi gargadin cewa daukar irin wannan matakai zai cutar da majalisar dinkin duniya wajen cimma kudurin ci gaban alumma. Kasashen Amurka da sauran kawayenta sun maka...
Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya. Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu, ya gabatar a zaman majalisar . A yayin gabatar da kudirin, Amadu ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da “yaki ci yaki cinyewa” a Jihar Zamfara da ma fadin kasar, za a iya cewa, “gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba don kare rayuka da kadarorin ‘yan Nijeriya don ba su damar...
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai. Harin an kai shi ne kan sansanin yan gudun hijira mafi girma dake kasar Labanon yanzu dai dubban gidaje ne suka shiga cikin fargaba saboda da hare haren da isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa, Gwamnatin kasar labanon na fuskantar mummunar suka na rashin daukar matakan da suka dace da haka yasa isra’ila ke yawan kai hare-hare a kudancin kasar, yayain da jami’an gwamnatin ke cewa yanzu haka suna shirin mika wani korafi ga...
Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Shaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar. Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka...
Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar. DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo. Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
A Iraki an sanar da sakamakon karshe na zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Talata data gabata. Sakamakon ya nuna cewa Jam’iyar Firaminista Mai Barin Gado Mohamed Shia al-Soudani ce ta sami rinjaye mai yawa a majalisar da kujeru 46, inda za ta rike kusan rabin kujerun, idan aka kwatanta da kasa da kashi 40% a baya. Majalisar za ta gudanar da zamanta na farko a watan Janairun 2026. Sabuwar majalisar dokokin za ta kuma zabi sabon shugabanta daga bangaren ‘yan Sunni sai kuma shugaban Jamhuriya, wanda dole ne ya kasance daga bangaren Kurdawa. Shi kuwa shugaban gwamnati wato firaminista dama dole ne ya fito daga bangaren ‘yan shi’a kamar tsarin mulkin kasar ta tanada a Iraki....
A wani lokaci yau Laraba ne aka shirya shugaban majalisar dokokin Togo zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Moscow. Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu, wadanda suka dade suna da kyakkyawar dangantaka, za ta mayar da hankali kan zaman lafiya da tsaron yankin, da kuma batutuwa daban-daban, tun daga da makamashi zuwa ciniki da noma. Wannan zata zama ganawarsu ta farko ta keke da keke tun shekarar 2019. Wannan ziyarar aiki, bisa gayyatar Vladimir Putin, wani bangare ne na “shawarwarin da Rasha ke ci gaba da gudanarwa a cikin ‘yan watannin nan da abokan huldarta na kasa da kasa,” a cewar wata sanarwa da aka fitar a Lomé. Kamfanin dillancin labarai na Rasha TASS ya ambato Togo a cikin kasashen...
Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA). Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin. Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne. https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da...
Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse. Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi. A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke...
Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin
Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan dake nan Iran. Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran. A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka...
Ma’aikatar harkokin cikin gida a jamhuriyar Nijar ta sanar da dakatar da ayyukan kungiyoyi da dama masu gudanar da ayyukan agaji na cikin gida da kuma na kasa da kasa, saboda rashin fitar da bayanai akan yadda harkokin kudi. Bayanin ma’aikatar harkokin cikin gidan bai tantance adadin kungiyoyin da aka dakatar da su ba, sai dai wasu majiyoyi sun ce sun kai daruruwa. A karshen makon da ya shude ne dai aka fitar da sanarwar ta kafofin watsa labaru da su ka hada Radiyo da ake Magana da gwamnonin jahohi akan matakin. Bugu da kari bayanin ya ce; kungiyoyin da aka buga sunayensu a cikin jaridu ne kadai aka bai wa izinin ci gaba da gudanar da ayyyukansu, da adadinsu...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint Jubail ya fuskanci hare-hare ta hanar amfani da jirgin sama maras matuki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Tashar talabijin din ‘almanar’ ta Lebanon ta ambaci cewa, wani jirgin “sra’ila” maras matuki ta jefa bom a kan wata motar haka rami da hakan ya yi sanadiyyar konewarta, wanda shi ma sabon keta yarjejeniya ne. Mahukunta a yankin na “Bint-Jubail” sun fitar da bayanin...
Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil. Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan abinda yake faruwa na sauyin yanayi da shi ne jigon taron. Wata mace da ta fito daga Munduruku daga jahar Par, ta fadawa manema labaru cewa: “Mun zo nan wurin ne tun kwanaki da yawa, kuma muna son a ji muryoyinmu ne. Muna son zama ne domin yin taattaunawa aka abinda ya shafi sauyin yanayi.” Al’ummun karkara, wadanda sauyin yanayi yake shafa kai tsaye, suna...
A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata. Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4. Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba. Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su...