Kungiyoyin Falastinawa sun bayyana farmakin birnin Kudus da aikin Jarumtaka
Published: 9th, September 2025 GMT
A cikin jawabai daban-daban da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sukayi sun yi marhabin da farmakin da wasu mahara suka kai a jiya Litinin a arewacin birnin Quds, inda suka bayyana hakan a matsayin martani ga kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa take yi kan al’ummar Falastinu, musamman a zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Irna, ya nakalto daga shafin tashar talabijin ta Al-Masirah cewa, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai jinjinawa da aikin wanda ta danganta da jarumtaka.
Muna mika gaisuwar bajinta ga farmakin da mayakan gwagwarmayar Falastinawa biyu suka kai a matsugunan yahudawan sahyoniya ta Ramot da ke arewacin birnin Quds da suka mamaye.
Ta kara da cewa wannan farmakin wani martani ne ga laifuffukan ‘yan mamaya da kuma yakin kisan kare dangi da suke yi kan al’ummarmu. »
Hamas ta jaddada cewa wannan mataki na kunshe da sako karara: ga “Shirye-shiryen mamaye Gaza, da kuma masallacin Al-Aqsa.
A nata bangaren, kunmgiyar Jihad Islama ta Falasdinawa ta bayyana wannan aiki a matsayin abin ban mamaki, tana mai imani da cewa yana wakiltar: Martani ga ci gaban manufofin gwamnatin sahyoniyawan masu aikata laifuka, da tsokanar da take ci gaba da yi, da yunkurin da take yi.
A jiya Litinin ce wasu mayakan Falasdinawa biyu suka bude wuta a cikin wata motar safa da ke dauke da mazauna Isra’ila a mahadar matsugunan Ramot da ke arewacin birnin Kudus (Quds), inda suka hallaka 6 daga cikin da raunawa wasu fiye da 10 a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta Isra’ila.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar dokokin Faransa ta yanke kauna ga firaministan kasar Francois Bayrou September 9, 2025 An bude taron sauyin yanayi na Afrika karo na biyu September 9, 2025 Iran : Araghchi da Grossi zasu gana a wannan makon September 9, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Masar Sun Tattauna Ta Wayar Tarko Kan Shirin Nukliyar Kasar September 8, 2025 Iran Ta Ce Akwai Sauyi Ta Yadda Zata Ci gaba Hulda Da Hukumar IAEA September 8, 2025 Xi Jinpng: BRICS Zata Ci Gaba Da Ayyukanta Duk Da Matsalolin Da Ke A Gabanta September 8, 2025 Kamfanin Kasar China Ta Sami Nasarar Samun Aikin Gina Titi Tsakanin Chadi Da Kamaru September 8, 2025 Gwamnati Najeriya Ta Kaddamar Da Sabbin Darussan Karatu September 8, 2025 DSS Ta BuKaci shafin X Ya Sauke Shafin Sowore Ko Ta Fuskanci Hukunci September 8, 2025 Tawagar Kasar Iran Ta Samu Gagarumar Nasara A Wasan Wushu Na Shekara 2025 September 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).
Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya cewa babu wani shirin makamin nukiliya domin mun dade muna duba shi.
Wannan ya zo ne yayin da Iran ta yi gargadin cewa aiwatar da abin da ake kira “snapback” da sake sanya takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai uku za su soke yarjejeniyar da ta yi da IAEA kan sake fara hadin gwiwa da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a ranar 9 ga Satumba.
Wannan ya zo ne bayan da Majalisar Dokokin Iran ta amince da doka da ta bukaci gwamnati ta dakatar da duk wani hadin gwiwa da IAEA bayan harin Isra’ila da Amurka a watan Yuni.
A bisa dokar Majalisar Dokoki, ba za a ba wa masu sa ido na IAEA izinin shiga Iran ba sai an tabbatar da tsaron cibiyoyin nukiliya na kasar da na ayyukan nukiliya na zaman lafiya, wanda hakan zai kasance ƙarƙashin amincewar Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa ta Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci