HausaTv:
2025-09-18@00:44:33 GMT

“Kasashen Larabawa ma basu tsira ba daga hare-haren Isra’ila” (Naim Qassem)

Published: 11th, September 2025 GMT

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa idan kasashen Larabawa ba su goyi bayan ‘yan gwagwarmaya ba, to su ma za su fuskantar hare-haren Isra’ila”

A jawabinsa babban sakataren kungiyar ta Lebanon ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila da Amurka suna aikata munanan laifuka a zirin Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da ke mamaye, yayin da al’ummar Falastinu suka yi tsayin daka duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta.

Bugu da kari, Sheikh Naim Qassem ya yaba da sadaukarwar Iran da al’ummarta da kuma al’ummar kasar Yemen, kan yadda suka tsaya tare da al’ummar Falastinu.

A cewarsa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan Falastinu da al’ummarta da kuma tsayin daka domin ‘yantar da su daga mamayar, yana mai cewa wannan shi ne daya daga cikin manyan ginshikan hadin kan Musulunci.

A jawabin da babban sakataren kungiyar Hizbullah ya gabatar a wannan Laraba, a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW), ya tunatar da cewa, Imam Khumaini, wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yanke shawarar ayyana makon hadin kan Musulunci ne domin kusnato da al’ummar musulmi ‘yan uwan juna kusa da kusa ta hanyar hadin kai da fahimtar juna.

Dangane da harin da Isra’ila ta kai kan Qatar, Naim Qassem ya ce watarana Isra’ila za ta iya kai hari kan Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa,Saboda yadda kasashen Larabawa da ke yankin suka kasa daukar matakin soji kan gwamnatin Isra’ila, kamar yadda ‘yan gwagwarmaya ke yi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Faransa : Mutane 250,000 suka shiga zangar zangar ‘’a Toshe komai’’ inji CGT September 11, 2025 MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike September 11, 2025 Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci September 11, 2025 Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba” September 10, 2025 Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar September 10, 2025 Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da al ummar

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.

 

Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.

 

“Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen wannan ta’addancin.”

 

Dan Majalisar ya ce ya gabatar da bukata ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa domin tallafawa wadanda lamarin ya shafa kuma zai ci- gaba da bibiya domin ganin tallafin ya samu cikin lokaci.

 

Ya ce yana kokarin ganin rundunar sojoji ta kara tura wadatattun jami’ai tare da tallafa masu domin yakar ‘yan ta’addan da wanzar da zaman lafiya a yankunan.

 

Tallafin kayan abinci na gaggawa da dan majalisar ya bayar sun hada da buhuhuwan masara, gero, garin kwaki da kuma kuli- kuli.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •   Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar
  • Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila