Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 79 A Yankin Zirin Gaza
Published: 4th, September 2025 GMT
Falasdinawa 79 ne suka yi shahidai sakamakon tashin gobara da farmakin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai zirin Gaza a jiya Laraba
Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar a cikin dare cewa: An kashe Falasdinawa 79 sakamakon tashin gobara da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ciki har da mutane 16 da ke jiran agaji.
Majiyar ta bayyana cewa, an mayar da shahidai 25 zuwa Asibitin Al-Shifa, 6 zuwa asibitin Sheikh Radwan, 7 zuwa Asibitin Al-Ahli Arab Baptist, 5 zuwa Asibitin Rehabilitation Hamad, 1 Asibitin Al-Awda, 12 zuwa Asibitin Shahidai Al-Aqsa, 23 kuma zuwa Asibitin Nasser.
Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza, inda suka kai farmaki a gabashin Hasumiyar Hamad dake arewacin Khan Yunus, inda suka yi ruwan bama-bamai a tantunan ‘yan gudun hijira da suka rasa matsugunansu da ke kusa da hasumiyar Italiya da ke unguwar Al-Nasr a birnin Gaza, tare da jefa bama-bamai a kan gidan iyalan Habib da ke unguwar Al-Sabra da ke birnin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Iran ba ta fargabar tattaunawa kuma ba ta tsoron kare kanta idan aka kallafa mata yaki September 4, 2025 Najeriya ta ba da izinin binciken danyen mai a karkashin teku ga kamfanin TotalEnergies September 4, 2025 Yemen ta sanar da kai hare-hare biyu kan ‘Isra’ila’ September 4, 2025 Afirka ta Kudu ta aika da wakilai 30 zuwa IATF 2025 September 4, 2025 Ministan Najeriya ya bukaci Afirka da ta tsara makomar AI September 4, 2025 Bikin baje kolin Ciniki tsakanin kasashen Afirka (IATF) 2025 AFRICA24 September 4, 2025 Gharibabadi: Iran Ta Nuna Diflomasiyya A Taron Kungiyar Shanghai September 3, 2025 Baqaei: Babu Aminci Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA September 3, 2025 IRGC: Takunkumin Turai A Kan Iran Daukar Fansa Kan Juriyar Al’ummar Kasar September 3, 2025 Qalibaf: Ya Kamata Gwamnatocin Kasashen Musulmi Su Fito Su Yi Allah Wadai Da Ayyukan Isra’ila A Gaza September 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zuwa Asibitin
এছাড়াও পড়ুন:
Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza
Rahoton da wani jami’in majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya jumaa ya nuna cewa sojojin isra’ila sun kama wani ma’aikacin UNICEF mai suna Raed Afif mai shekaru 45 da haihuwa a kerem shalom alokacin da yake gudanar da ayyukansa.
Yazu wa yanzu isra’ila bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama shi ba kuma take ci gaba da tsare shi.
Kwana daya kafin tayi kamun isra’ila ta bukaci kungiyar ta Unicef da ta kwashe dukkan kayayyakin agajinta daga yankin , kawai sai ta rufe dukkan kofofin shiga da magunguna zuwa asibitocin dake arewacin yankin Gaza. Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi gargadin cewa wannan matakin an dauke shi ne domin yanke duk wasu ayyukan jinkai da ake yi da kuma korar dukkan kungiyoyin agaji da hakan zai kara sanyawa yanayi ya kara tazzar a yankin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci Daga Yanzu November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci